Sashe 36
Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bata jima ba ta dawo da wasu jibga-jibgan kuloli, na alfarma, ajewa tayi, ta buɗe ta zuba masa a wani ƙayataccen Filet, ta kalle sa ta ce "kuma sai ka cinye dika," "ke mai kika maida ni ne???" dariya tayi, batare da tace komai ba, saida ya ɗan kwashi ƴan mintina yana latsa waya, sannan ya fara cin abincin, Aaminat kuwa sai murna take tana mai ƙara godewa Allah, aranta ta ce "duniya juyi-juyi yau gani ga yayana agida na," ta ƙarasa zancen zucin tana murmushi, ƙaɗan yaci ya ce ya ƙoshi dama don karta ga ya ƙi ci ne, tana ya ƙara ci yana ya ƙoshi, ya miƙe ya ce "ni kinga tafiya ta sai wata rana," yanzu tafiya zakayi??" "A'a kwanciya zanyi," ya ƙarasa maganar yana dariya, ita ma dariyar tayi, ya nufi kofa, bin bayan sa tayi domin yi masa rakiya, sallama sukayi, ya hau mashin ɗinsa ya ɗaware,
Abba kam tunda ya isa kasuwa, ya kasa komai sai tunanin Aaminat, kozata iya yafe masa, ko bazata yafe ba, wannan tunanin ne yake tayi masa juyi a ƙwa-ƙwalwa, in ya zauna sai ya tashi, sai zarya yake, Hamza ma tunda Abba ya bashi labarin komai, jikinsa yayi sanyi salam har dare yayi Abba ya koma gida, jikinsa amace, tunda ya koma yake zazzagawa Mama ruwan faɗa, banda kuka babu abinda take, Umma ce ta samu nasarar, bashi haƙuri kuma ya haƙura,
washe gari ma koda Abba ya tashi bai nunawa Mama bambanci ba sai nasihohi da ya haÉ—a su ita da Umma yayi musu,
Bayan wata É—aya.
Fati ce zaune, ta zabga tagumi sai hawaye take, kallo ɗaya zakayi mata kasan tana cikin mawuyacin hali, ta rame ta ƙanjame, tayi wani ragwaf-ragwaf kamar tsohuwa, saitayi yun ƙurin tashi saita kasa, tun safe take zaune awajen har shabiyu na rana tayi, amma ta kasa koda motsawa, in tayi kamar zata tashi sai jiri ya ɗebeta ta koma tayi jagab, tana cikin wannan halin Ahmad ya shigo, hannunsa riƙe da waya ya manna ta akunnan sa yana waya cike da jin daɗi, wucewa yazoyi ta gefen Fati, tayi saurin cafke ƙafarsa, ya harbatsar da ita gefe, cikin rawar murya ta ce "Allah ya isa tsakani na da kai macuci kawai, ka yaudareni kaci amana ta," cikin zafin rai ya dubeta ya ce "kekika yaudari kanki, duniya ta rufe miki ido kika kasa gane asalin waye ni," cikin kuka da taurin kai ta ce "mugu Azzalumi Allah saiya saka min, yau kwana biyu baka bani ci ba baka bani sha ba ga duka na rana daban na dare da ban," ta ƙarasa maganar tana wani galabai-taccen kuka, shi kuwa ko ajikin sa, yayi gaba, cike da tsiwa da rashin kunya Fati ta ce "Allah ya isa mugu kawai ɗan is...." marin da ya kifa mata ne ya hana ta ƙarasa maganar, ya ƙara sharara mata wani azababban marin mai rikitar wa, saida taga taurari sun gifta, shiɗewa tayi ta kasa kukan, cikin ɓacin rai ya ce "niki ka zagi, an faɗa miki ni ɗan asara ne da zaki zagi iyaye na, na ƙyaleki, to ki sani ni iyayena basu ce jeka ka gani ba,.." ya numfasa yaci gaba da cewa "ƴar iska ta wuce ke, wato kin samu duniya kin banzatar da iyayen ki, to kisani nine ajalin ki muddin baki daina ɗagamin harshe ba," cikin mawuyacin hali da azaba, Fati ta fara magana muryar ta dakyar take fitowa ta ce "Ahmad kayimin duk abinda ka gadama, Allah ne ya jarabce ni, bazan taɓa ganin laifinka ba, sakaiyar Aaminat ce da waɗan da na cuta na yaudare su, duniya kenan, kaico na da na kasance, mai son zuciya, duniya ta ruɗeni, na afka inda ajali na yake," ta ƙarasa maganar tana gursheƙen kuka, Ahmad jikin sa yayi sanyi, ya nufi inda Fati take, yana ƙoƙarin kamata ta ce "A'a Ahmad bancan-canti ka taimake ni ba, kaɗan na gani daga cikin abinda na aikata, amma don Allah idan Allah yayi na koma gareshi ka nema min yafiyar ƴar uwa ta Aaminat da iyayena, kane mamin yafiya a wajen mahaifiya ta da na juyawa baya," zuwa yanzu Ahmad tausayin Fati ya gama mamaye zuciyar sa, ya matsa kusa da ita ya ce "kiyi haƙuri da abinda nayi miki duk da nasan ba a son raina nake azabtar da ke ba" murya na rawa ta ce "baka da laifin komai, hakan jarabta ce daga uban giji, kuma ta silar hakan nayi na damar abinda na aikata abaya,!" Ahmad yayi murmushi, ya ce "Fati kin gane gaskiyar abinda kika ai kata ba dai-da bane!!!??" ta gyaɗa kai, alamar eh, "to ni da kaina zan taya ki roƙar ƴar uwarki ta yafe miki, kuma zata yafe miki," share hawaye tayi ta dubbeshi, ta ce "banajin Anty Aaminat zata iya yafe min, domin kuwa abun da na aikata mata ya munana, kuma ko ba komai yanzu nasan Aaminat ta wuce inda nake zato" "hakane amma ina mai kyauta-ta zaton zata yafe miki in sha Allah, gigiza kai Fati tayi tana ƙara tuno irin cin zarafin da tayi wa Aaminat abaya, Ahmad ya ce "kitashi kiyi wanka" ƙoƙarin tashi ta farayi, Ahmad ya taimaka mata ta tashi, ya raka ta banɗaki, tayi wanka, kafin ta fito ya haɗa mata shayi, tana fitowa tasha shayin sosai dan kuwa muguwar yunwa takeji, Ahmad ya kalle ta ya ce "Fati kinsan me" ta ce "A'a" ya ce "maganar gaskiya ni ba mai kuɗi bane hassali ma iyaye na a ƙauye suke, ni nataso ne a makarantar allo, daga bisani na samu aikin shara da bawa fulawoyi ruwa a gidan su Abubakar mijin yayar ki, daga baya suka maidani Direban su hakan yasa na iya mota, kuma nake hawa mota kala-kala, kikayi zaton ni mai kuɗi ne, a ranar da muka haɗu dake ma aike na akayi," ya numfasa, kana ya ɗora da cewa "gidan nan ma da muke zaune mallakin Yarima ne, banawa bane bamu da gadon sa, lokacin da na faɗa masa zanyi Aure ne ya bani wannan gidan na zauna na wani lokaci," tuni hawaye sun wanke fuskar Fati, tabbas duniya makaranta ce, ta gama ruwan idon da yaudare yaudare ƙarshe ga inda Allah ya jefota,
share hawayen tayi ta ce "naji kuma na yarda zan zauna da kai, amma don Allah tunda kasan inda Aaminat take kayi min Jagora, na nemi yafiyar ta," ajiyar zuciya ya sauke, kana ya ce "karki damu yanzu zamuje kuma zata yafe miki,"
Fati ta miƙe tana cewa "muje yanzu" shima tashi yayi ya mara mata baya,
Aaminat tana zaune ta harɗe ƙafa, ƴar aikin ta tashigo, ta ce "ranki ya daɗe kinyi baƙi," "baƙi kuma" Aaminat ta maimaita cikin sigar tambaya, Na'ima ta ce "eh ranki ya daɗe, kuma naga kuna shigen kama da ita," Aaminat a ranta ta ce "ko suwaye su Umaima da Siyama dai jiya sunzo to ko Iman, ce"
afili kuwa ta ce "ki saukesu a Falon baƙi kice ina zuwa" cike da girmamawa ta ce "to" ta nufi inda su Fati suke, Aaminat kuwa ɗaki ta nufa ta sako ƙaton hijab sannan tayi Falon Baƙi,
da sallama ta shiga ɗakin, rassss gaban ta ya faɗi, lokacin da idon ta ya sauka akan Fati, ja baya tayi tana watsawa Fati wani irin kallo, "mai ya kawo ki inda nake ko kinzo ki ƙarayi min wani ƙazafin, kina so kice na ai kata wani abun ne?!!!" ta ƙarasa maganar cikin hargowa da ɗaga murya, Fati kuwa wani kuka ta saki, mai cike da nadama da danasani, ta ce "don Alla.....!!!" Aaminat
ce ta katse ta da cewa "mai kike so kice dani mai zaki ce ki tattara yanaki-yanaki ki barmin gida, azzaluma, kawai, butulu!!!" cikin kuka Fati ta ce "nazo ne nanemi yafiyar ki koda bazaki yafe min ba, ina roƙonki da kiyi min gafara ki yafe min duk abinda nayi miki don Allah, kitaimaka min"
ta ƙarasa maganar tana durƙushewa agaban Aaminat, tuni jikin Aaminat yayi sanyi, ta shiga share hawayen ta, Fati kuwa kuka take tana ƙara nemar gafarar Aaminat, cikin kuka Aaminat ta ce "Fati na yafe miki kinji ke ƴar uwata ce, ki daina kuka," ta ƙarasa maganar tana rugume Fati, kuka suka shigayi, babu mai rarrashin ɗan uwan sa, Ahmad ma matsar hawaye yake, Aaminat ta share hawaye ta fara rarrashin Fati har saida tayi shiru, sannan ta ƙara nemar yafiyar Aaminat, Aaminat ta ce "na yafe miki, na daɗe ina jiran wannan ranar tazo, ranar da zamu haɗe kanmu," Fati tayi murmushi mai tafe da hawayen farin ciki, sai a lokacin Aaminat ta lura da Ahmad, suka gaisa, sallama yayi musu da niyar da yamma zai dawo ya ɗauki Fati,
Fati taji daÉ—i sosai, duk wunin ranar, da yamma Ahmad ya dawo ya É—auketa suka koma gida,
Haka rayuwa taci gaba da tafiya ko wane ɓangare farin ciki ya wanzu,
Akwana a tashi rayuwa tana ƙara shuɗewa sanyi zafi damuna rani bazara
waiza tana ƙara juyawa,