Sashe 14
Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Washegari
Da misalin Ƙarfe 10:00am ta na zaune ta buga tagumi bayan ta gama haɗiyar Maganinta, takaicin shan maganin duk ya isheta don kuwa ba ƙaunarsa ta ke yi ba. Siyama ce ta yi sallama fakatan-fakatan ta shigo ta tsaya ta riƙe ƙugu kafn ta ce "Aaminat! fita idona in rufe, na aiko Walid ya ce ki fito mu tafi Asibitin sabi da gardama kin ce ba za ki je ba ko?" Cikin matuƙar takaicin rawar kan Siyaman ta ce "Allah i yaye miki Siyama, ni dai ba na samu sauƙi ba? to ban ga me sa ni na fita ba yanzu, ni ba na son temakonsa; ba wani gwajin da za a yi min." Siyama ta gyara ɗaurin ɗankwalinta ta tunkuɗo shi gaba ta fara tattafa hannaye gami da cewa "To wallahi ko Mutuwa za ki yi sai dai ki mutu bayan mun je Asibitin!" ta na kaiwa ƙarshen maganar ta maida hannun kan ƙugunta ta riƙe gami da cellaro ƙafa ɗaya gaba, Aaminat ta tsaya kallonta ta na tunanin ta yadda akai ta zama Ƴar Buyagi haka. Cikin sigar rarrashi Aaminat ta ce "Siyama ki fahimce ni don Allah, ba ki san komai ba a halayen Maza shi yasa ki ke dagewa akan sai na bi shi, temakon nan zai iya zamewa wani sabon babin Baƙin ciki na rayuwata, ki yi haƙuri ki bar ni zan lallaɓa Ya Umar ya kai ni Asibitin duk wani abin da za a yi sai a yi min." Siyama ta sassauta murya sannan ta ce "Nima ki fahimce ni Aaminat, tare da ni fa za mu je, kin ga in ma tsoron zargi ke ke yi kin fita tinda da ni, idan kuma ki na tsoron Dr Yarima ne ina me shawartarki da ki dinga kyautatawa mutum zato, jiya ki ka fara haɗuwa da shi kar ki yi masa zaton da shi ba haka yake ba, ki nemi Kariyar Allah in kin yi haka ba abin da zai faru in sha Allahu.
Aaminat ta yi shiru ta na nazarin kalaman Siyama, ta daɗe ta na tunani kafin ta tashi ta ce "Ɗakko min Hijab ɗina Dogo, a shirye nake tinda ba kwalliya zan yi ba ni." Siyama ta ce "Ki ma yi kwalliyar mana, Mutum ba lafiya ba sai Ƙilinbo iri-iri kamar rainon Jinnu." Aaminat ta yi mata banza don kuwa ta lura akan Guiwa Ƙawar ta-ta take.
Su na fita Ƙofar gida su ka yi Tozali da Fallatsetsiyar Mota Fara kar da ita, Siyama ta ce "Alhamdulillahi, dama ina tsoron tafiyar Ƙasan nan, Allah ya kawo shi." a ɗan Fusace Aaminat ta ce "Wai way....." kasa ƙarasa maganar ta yi sabi da IDO HUƊU da su ka yi ita da shi, ya zuba mata Brown Eyes ɗinsa masu zaiba-zaiba, suƙut ta haɗiye Yawu tare da sauran Kalamanta. Ya haɗe Cikin Riga Baƙa me ɗan Gajeren Hannu da Wando Blue (Bulu), ya wani Coge a jikin Mota ya na ɗaiɗaita idanu akanta.
Ganin ta tokare ta kasa tafiya ya sa Siyama ta ja hannunta kiiii ta na cewa "Yanzu in biye miki za mu yi sai Wankin Hula ya kaimu Dare." Sai da ta tura ta cikin Motar sannan hankalinta ya kwanta, ta kalli Dr Yarima da yake dariya Ƴar ciki-ciki cikin yanayinta na shiririta ta ce "Yallaɓai Ina kwananka? ga ta nan na fito da ita da ƙyar, Allah ya sauwaƙe min da tuni Na yanka Kazar Wahala na Fige na cinye." sai da ya tuntsire da dariya sabi da jin kalaman nata, ta taɓe baki ta yi masa kallon ba ka dameni ba sannan ta shige Motar, Dr Yarima ya Zagaye ya shiga Mazaunin Direba ya fara Tuƙi cikin nutsuwa.
Aminu Kano Teaching Hospital Su ka nufa, su na zuwa ba ɓata lokaci ya yi abin da zai yi su ka fito daga Aminu Kano zuwa AA Hospital. Cikakken sunan Asibitin shine, AMEENU ABDULLAH HOSPITAL
a nan ma gwaje-gwaje aka yi mata sannan ya tarkato su ya dawo da su gida. sallama su ka yi bayan ya jaddada musu gobe zai dawo tare da Bayanan Gwajin nata, Aaminat dai sai gyaɗa kai da girgizawa ba Baki, Siyama kuwa ita da shi babu gwani a fagen Magana idan ya faɗi Ɗaya za ta shirya masa goma shi kuma zai ƙara mata da wata ɗayar Zazzafa, ta ari bakin Aaminat wajen yi masa godiya sosai da nuna farin ciki akan Temakon da ya yi musu.
Sai da su ka shiga cikin gida Aaminat ta kasa Aradun Mita, motsi kaÉ—an sai ta yi maganar surutunsu, da Siyama ta gaji sai ta bar mata gidan.
Washegari
Gwajar ɗin wayarta ce ta ta fara ƙara, ta janyota Zuciyarta cike da takaicin kiran ko ma waye, sai da ta katse wani kiran ya ƙara shigowa sannan wayar ta taɓu da ƙyar don kuwa ta fara cin sensor, ta yi sallama a ɗaya ɓangaren Dr Yarima ya amsa, Sai da ta kusa yarda wayar sabi da ɗan firgitar da ta yi na wucin gadi, ya yi mata bazata ba ta taɓa tunanin za ta ji shi ba, don kuwa da hannunta ba ta bashi lambarta ba, kai tsaye ta ɗorawa Siyama laifin. "Aaminat ki na tare da ni??" ya jefo mata tambayar cikin lallausar murya, gyaɗa kai ta yi a sanyaye ta ce "Eh." ya ce "Na zo fa, za ki fito ne ko na haɗu da Siyama kawai?" cikin sauri ta ce "Ya ma fi sauƙi, ka haɗu da ita yanzu aiki na ke yi." ya yi murmushi me sauti ba tare da ya ƙara magana ba ya katse wayar, Siyama da ta hakimce a kujerar ɗan zaman banza ya kalla kafin ya ce "Yau ba zan samu ganinta ba, don haka mu yi magana." ta maida hankalinta kansa sannan ta ce "To Dr ina jinka." "Da na yi tunanin fa Hawan jini ne ke shirin tasarwa Ƙawarki, bayan bincike kuma na gane Ƙarancinsa ne ya fi damunta sabi da yawan ciwoce-cowoce da take, amma inda matsalar ta ke, ta fiye sa kai a damuwa hakan kuma ka iya janyo mata Taɓuwar Zuciya anan gaba; ya na da kyau ki kula da ita yadda ya kamata ki dinga sa ta shan magani sannan ki dinga ƙoƙarin hana ta zaman tunane tunane da damuwa; za ki iya ganina kwatsam na zo ganinta a koda yaushe don haka ki zauna cikin shiri domin ke ce abar dafawata. Siyama ta zuba tagumi ta na kallonsa, sai da ya gama dogon bayanin sannan ta rausayar da kai ta ce "Allah Sarki Aaminat, dama na yi tunanin haka shi ya sa na damu akan mu je Asibiti, mun gode da temakawarka Yallaɓai, ai ka yi mana mutunci idan ka dawo ganinta in sha Allah za ka ganta." ya saki lallausan murmushi gami da cewa "Na gode." buɗe murfin Motar ya yi ya fita, itama Siyama ta fita, a gidan baya ya ɗakko Ledar Magunguna ya miƙo mata ta karɓa gami da ƙara masa wata Godiyar.
Sai da ya tafi sannan ta shiga gida ta kaiwa Aaminat Magungunan tare da kora mata jawabi, jikin Aaminat ya yi sanyi Salam da ta ji abin da ke damunta, Siyama ta ce "Ya ƙara da wasu dokin ma fa, kuma ya zama dole ki kula ni zan dinga ku la da ke ma, ga shi ko Abinci ba ƙaunar ci ki ke ba." Cikin rauninnZuciya ta ce "Siyama Abinci ne sai ka ce ba na gidan Mahaifina ba, da gori da gore-gore ake ba ni shi kullum ko da ni na girka." Siyama ta rausayar da kai gami da cewa "Allah i kawo ƙarshen abin."
Bayan wani lokaci Aaminat jiki ya yi ƙwari ta samu lafiyarta, Siyama ba ta yi mata da wasa wajen ɗura mata Abinci da magani da sauran abin da ya kamata kuma takan zauna ta dinga bata labarai ko kuma ta karanta mata Littafan da ta ke karantawa.
hakan kuwa ya matuƙar samawa Aaminat nutsuwa duk hayaniyar kanta ta yi sauƙi, ƙarin farin cikin nata kuwa, Abdulkareem da ba ya shiga shirginta tin lokacin da ta fara rashin lafiya za ta iya cewa Ba ta yi IDO HUƊU da shi ba (Sunan Wani littafi nawa IDO HUƊU me ban tsoro) hakan ya sa ta farin ciki sosai ta saki jikinta.
Fitowarta kenan daga gidan su Siyama kamar daga sama ta ji ya kira sunanta, Gabanta ya yanke ya faɗi, a ranta ta ce Shi kenan baƙar ƙaddarar tawa ta dawo.
"Aaminat na samu wasu baƙaƙen labarai da ba su yi min daɗi ba."
Â©ï¸ INDO tare da AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin HaÉ—aka ne💪ðŸ¾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S
Shafi 12
Bismillahirrahmanirrahim