← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 38

Sashe 34

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Atsaye suke cirko-cirko, kowa yana tunane tunane, Nana Hauwa ce ta dubi Abdussalam gami da cewa "anya kuwa Abdul zai dawo garemu, kusan wata ɗaya kenan baya garemu kuma duk ta silar ku ne" ta ƙarasa maganar tana sharar hawaye, Abdussalam ya jata jikinsa cikin sigar kwantar mata da hankali ya ce "sorry Nana ki daina kuka, in sha Allah komai zai dai-daita, kuma muna ta addu'a Allah ya juyo da hankalin sa gida" Nana Farida ce ta tashi daga kusa da Dadda ta ce "kalli fa Ummi bata da lafiya, ya zama dole in muna son rayuwar mahaifiyar mu mu nemo ya Abdul," Abdurrahim ya girgiza kai kana ya ce "ta hanya ɗaya zamu sami Abdul"
Abdulmajid ya ce "wace hanya ce???" "ta hanyar roƙon Kadija ta faɗa mana inda yake domin kuwa ina da tabbacin ta san inda yake" da sauri Dad ya tashi zaram yana zaro ido ya ce "haka ne Maza ku kira ta " "to" Abdullah ya faɗa yana nemo number Kadija, kira ya danna mata bugu huɗu ta ɗauka da sallama, hankali tashe ya ce "don Allah kadija ki taimaka ki faɗa mana inda Abdul yake karki ce baki san inda yake ba, hakan na iya silar rasa mahaifiyar mu," ya ƙarasa maganar kamar zai yi kuka, Kadija kamm tayi suman zaune ta kasa koda magana ne, jin ya ƙara cewa "Kadija Abdul shine rayuwar mu baki ɗaya dan Allah" yasa tayi fifgigit, cikin muryar kuka ta ce "Abdul yana india, dole ce tasa na faɗi inda yake," "Kadija kidawo gida Abdul ma zai dawo" hawaye ta share tana tuna lokacin da su Dadda suka murzawa idon su toka suka hana Abdul Abinda yake so, "Kadija yanzu in sha Allah zamu shirya tafiya, kuma hada ke gobe zamu je inda Abdul yake mu dawo dashi gida", wata nannauyar Ajiyar zuciya ta sauke gami da ce wa "ganin nan zuwa yanzu" sallama sukayi, Abdulmajid cikin jindaɗi ya ce "Alhamdulillah mun kusa dawo da Autanmu," kowa na ɗakin farin ciki ya hauyi ciki kuwa har da Dadda Ummi ma murmushi take tana miƙa saƙon godiya ga sarki Allah buwayi gagara misali,

Washe gari da sassafe Jirgin su Dadda Abdussalam Abdulmajid Nana Kadija, ya tashi izuwa ƙasar india,

Umma na zaune a ɗaki ta kammala karatun Alƙur'ni mai girma ta na yin addu'a, wayar ta ta fara ruri, ta mayar da Alƙur'anin mazaunin sa, sannan ta juyo inda wayar take kafin ta ƙaraso wayar ta katse, ɗaukar wayar tayi sannan ta zaune a gefen godo, kira ne ya ƙara shigowa wayar, ta ɗauka da sallama, "Assalamu'alaikum Ummana ta kai na," "Aminwa'alaikisalam," ta faɗa tana murmushi, cikin farin ciki da jin daɗi, Aaminat ta ce "Umma ya kuke ina kewar ku wallahi, dan Allah kice ya kawoni" "A'a Aaminatu kefa ba yarinya bace, ki zauna agidan ki kinji ko?" turɓune fuska tayi, kamar tana ganin Umma ta fara magana cikin shagwaɓa, "ni Umma na zan gani yaufa kwana huɗu rabo na da Umma na" "to kinga kwana huɗu ai bakyazo gida ba kuna zaune lafiya," "nifa Umma ji nake tamkar nayi shekaru ban ganku ba" Umma ta murmusa, Aaminat ta ƙara cewa "ina su Walid da Umaima suzo dan Allah" "A'a bazasu zo ba, kedai ki nutsu ki zauna agidan mijin ki banda yawon banza"
"kai Umma kin sanni fa ko a nan bana zuwa ko ina sai gidan su Siyama, anan kuma wa na sani, gidan da ko yara babu, ni duk na gaji, jinake kamar akan ƙaya neke, wata tsawa Umma ta darka mata ta ce "ba ki da hankali gidan mijin naki kike kira kan ƙaya? to karki sake na ƙara jin wannan maganar a bakin ki" tsitt Aaminat tayi baki na rawa ta ce "Umma dan Allah kiyi haƙuri bazan ƙara ba, kinji Ummu na" tsaki Umma taja, sannan ta ce "sai anjima" tana gama faɗin haka ta katse wayar, Aaminat kuwa ajiyar zuciya ta sauke.

Koda su Dadda suka isa masaukin Abdul, basu sha wahalar shawo kansa ba, kwanansu É—aya suka juyo gida.

Zaune suke Falon kowa sai farin ciki yake kamar ba gobe, Ummi kam tunda taga ɗan Autan ta sai ta nemi cuta ta rasa sai rashin ƙwarin jiki, Abdussalam kuwa sam ya kasa sakewa da Abdul dan kuwa bai manta lokacin da yake marin Abdul ba da maganganu mara sa daɗi, Dadda ya dubi Abdul ya ce "babban mutum" Abdulkareem ya ɗago da runannun idanun sa ya zubawa Dadda su, Dad yayi gyaran murya gami da cewa "Abdulkareem kayi haƙuri mun sani bamu kyauta maka ba, amma mu muna gyara goben ka ne, inaso ka sani ita rayuwa ba komai ne muke nema mu samu ba, wani abun muna neman sa ido rufe, amma sai Allah ya hana mu kuma duk dan ya jarraba mu ne, wani abun kuma zakuga bamu nema ba Allah ya bamu,"...... zuwa yanzu Abdul yayi ƙasa da kansa sai sharar hawaye yake, Dadda ya ce "komai na rayuwa haƙuri ake dashi, saika ga mai haƙuri ya cimma duk wata nasara, da yasa gama kuma Aure nufi ne na Allah idan Allah yayi matarka ce to babu makawa sai ta zama matar ka, idan kuma Allah baiyi ita ce matar ka ba to ko anzauna za'a ɗaura Auren sai Allah yayi yadda yaso, sai Auren ya warware,,

Abdul ina so ka zama cikakken musulmi mai yarda da ƙaddara aduk yanda tazo maka, ka daure ka cinye wannan jarrabawar" ɗakin yayi shiru sai shash-sheƙar kukan wasu daga ciki kakeji, tashi Abdul yayi ya durƙusa a gaban Dadda ya fara magana cikin da kakkiyar muryar sa mai daɗin sairaro, ya ce "haƙiƙa ka cancanti zama uba domin kuwa kaine cikakken da ya amsa sunan sa uba, ka jajirce akan iyalin ka ka tsaya tsayin daka don ganin anbi maganar ka, domin kuwa samun uba kamarka da kamar wuya, Dadda kaiɗin uba ne wanda bakowa ne yake da kamar ka ba," ya ƙarasa maganar yana faɗawa jikin Dadda, bayansa Dadda ya shiga bubbugawa, cikin nutsuwa, har saida Abdul ya samu nutsuwa sannan Dadda ya miƙe ckin farin ciki da jin daɗi, ya ce "Babban mutum kazo ka tayani fira," "to" Abdul ya ce ya tashi yabi Dadda sashin sa,

Bayan sati biyu komai ya dai-daita a gidan su Abdul sun manta da komai sai farin ciki Abdul ma Alhamdulillah bashi da aiki sai karatun Alƙur'ani mai girma gami da Azkhar.

INDO & AUTA
[8/9, 2:01 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)

Littafin Haɗaka ne💪🏾

Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

Tare da

Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION

Shafi 29

Ɓangaren Mama kuwa waɗanda ta ciwa bashi sun hanata sakat arana mutum biyar sa zo karɓar bashin da taci musu, yau ma kamar kullum tana zaune, a tsakar gida, Hajja Lantana tayi sallama, gaban Mama ne yayi wata muguwar faɗuwa, kasa amsa sallamar tayi, Umma ta amsa, Hajja Lantana ta kalli Mama kallo mai cike da razanarwa, ta ce "to koriyar munafuka Allah ya kamaki, yau ɗinnan zaki biyani kuɗi na, dan wallahi indai kika ga na bar gidan nan to da kuɗi na in kuwa ba haka ba, zanzo da mota na kwashe kayan ɗakin ki,!!!!!" tuni Mama ta fara zufa, jiki na rawa ta ce "dan Allah kiyi haƙuri idan na samu da kaina zanzo na kawo miki!!" wata shaiɗaniyar dariya Lantana ta saki lokaci ɗaya kuma ta murtuke fuska kamar ba ita tayi dariyar ba, hakan ya ƙara rikita Mama ta fara sharar gumin wahala, Umma kam tana so tayi magana amma ta kasa sai ido, Lantana ta daki bango, cikin hargowa, ta ce "zaki biyani kuɗina ko saina sa an kamaki, dan kuwa wallahi akan kuɗi babu abin da bazan iya ba,!!!" ta ƙarasa maganar tana tafe-tafe cikin muryar kuka Mama ta ce "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un na shiga uku, duniya ta ruɗeni,"...!!! "bakiyi salati ba sai kinganki a office ɗin ƴan sanda" sakin baki Mama tayi tana kallon Mara da tashigo, Mara ta kalli Mama sama da ƙasa sannan ta ce "yaro man kaza, rashin sanin wace ce Mara shiya kaiki cimin bashi ki ƙi biya, bana yafiya kuma bana ɗaga ƙafa, yanzu haka tafe nake da ƴansanda, zakije ofishin ƴan sanda ki biyani kuɗi na,, Lantana ta kwashe da dariya gami da cewa "tirƙashi ana wata ga wata, nima dani za'a ofishin nan a ƙwatar min ƙaƙƙi na!!" hannu Mama ta ɗora aka ta fashe da wani gigitaccen kuka ta na cewa "Allah na tuba ka yafemin Alhakin Aaminat ma kadai ba zai barni na sha ruwa ba, na zalumci baiwar Allah nayi mata sharri iri-iri, ni yau tawa ƙaddarar ta zo, nayi kuskuren cewa babu ni babu ƙaddara, gashu ƴar tawa ma ta gujeni kamar ba ni na haifeta ba don ta samu duniya, waiyo Allah na yau zasu tozartani!!!" haka Mama ra fara suntiri a tsakar gidan tana rusa kuka, Umma ma sharar haweye take domin kuwa idan kaga halin da Mama ta shiga sai ka tausaya mata,, cikin rashin imani Mara ta cukumi Mama da ƙarfin tsiya ta jata ƙiiiiii!!!!, Mama kam kuka take tana sambatu, har suka fita waje, mutane taf a layin kowa ya zubawa su Mama Ido, Walid yana zaune a cikin su Abdul, baisan lokacin da wani kuka mai ƙarfi ya kufce masa ba, haƙuri suka shiga bashi, Abdulkareem kuwa kauda kai gefe yayi,

Haka sunaji suna gani aka tafi da Mama, Umma kam ta rasa yadda zatayi sai faman sintiri take.
Chapter 34 · 0% Book details