← Book details Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 38

Sashe 24

Aaminat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*HALY-JASHERU venture's*
*munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.*
*prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA*
Ya na cikin tafiya ya ji wayarsa ta fara tsuwwa, ya duba ga mamakinsa sai ya ga lambar Aaminat, da sauri ya ɗaga tare da ƙoƙarin tsayar da motar a gefen titi.
Sallama ta yi ya amsa cikin sauri sannan ya ci gaba da tambayar lafiyarta.
Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Na kiraka ne don na baka haƙuri akan duk abin da na yi maka, ina fatan za ka manta da komai."
daga jin muryarta za ka san ta na cikin sanyin jiki gami da tsoro tsoro.
Abdulkareem ya saki murmushin farin ciki gami da cewa "Kullum cikin manta abin da ki ka yi min na rashin daÉ—i nake, kuma kullum farin cikin da ki ka sa ni nake tunawa na tin kafin ma na furta miki kalmar so, ina fatan nima kin yafe min akan turo miki wani da na yi, bayan haka kuma ina so ki faÉ—a da bakinki cewar yanzu kin yarda ni masoyinki ne ko da kuwa ke bakya sona."
Murmushi ne ya suɓuce mata ba tare da ta shirya ba, "Eh na amince kai masoyina ne, kuma ni ba ka yi min laifin komai ba."
Kusan tare su ka sauke zazzafar ajiyar Zuciya, Abdul ya lumshe ido ya na godewa Allah.
Jin ta ce "Sai anjima" ya sa shi sauri cewa "Tsaya mana, daga kira kuma sai ki ce sai anjima? nifa na fita ne amma sai na ji kamar in dawo, ko kina wani aikin ne?" zaro ido ta yi ta ce "Ahh gaskiya kar ka dawo."
Ya yi murmushi gami da cewa "Me yasa?" Æ´an kame-kame ta fara yi masa don haka ya ce "Ba komai zuwa dare dai za ka ganni in Allah ya yarda, ki tanadar min kyakkyawan murmushin nan naki ma kawai ya ishe ni."
Ba ta iya cewa komai ba sabi da wata ƴar kunya da ta rufeta, don kuwa ta na sane da cewa shi ɗin Ƙaninta ne, a ganinta abin kunya ne ta saki jiki ta yi soyayya da shi.
Shi kuwa hakan bai dameshi ba.

Tuna baya

Lokacin da Abdulkareem ya yi rashin lafiya su Abdulmajeed su ka kai shi Asibiti da daddare.

sai da su ka yi waya da DR Yarima ya sanar musu ya na asibitin Ameenu Abdullah sannan su ka nufi can don dama shi ne Family Dr É—insu.

Bayan ya gama bincikar lafiyarsa ya ce su bi shi Office É—insa.
Hakan su ka yi nan yake musu bayanin damuwa ce ta sako Abdulkareem É—in gaba, jin hakan ya tsuma musu zuciyarsu don ba su ga wani abin damuwa a Duniyar Abdulkareem ba.
Dr Yarima ya miƙe gami da cewa "Kai ƙaramin mai gida zo mu je in gana da kai."

Abdulkareem ya tashi ya na ƙasa-ƙasa da ido don ya lura fa kallon tuhumar da suke jefa masa.
Bayan sun fita sarari inda ba mutane Yarima ya tsaya ya na kallon Abdul sannan ya ce "Kai ya ne?" Abdul ya bashi hannu suka tafa ya na cewa "Likita Bokan Turai, ba ka so a Mutu ba ka so a Zauna Lafiya." Yarima ya yi dariya ya na cewa "Ai ku ne ku ka ɗaure mana abin, kai wai meye a ciki ne? faɗa min gaskiya me ya sa ka jawowa kanka ƙunci?? soyayya ka fara yi ko?"
Abdul ya ce "Malam ina ruwanka ba na son sa ido it's my life."
Yarima ya dara kafin ya ce "Ba ruwana amma da ruwan Alhaji Mai kasuwa, zan iya gaya masa gaskiya har ma na ƙara da duk abin da na ga dama."
Abdulkareem ya shafi ƙeyarsa gami da cewa "Ka matsa da yawa; kuma hakane wallahi soyayya na faɗa, amma ba wannan ce matsalar ba Yarinyar ta ƙi yarda da ni ne, ni kuma ina baƙin cikin ganinta cikin damuwa ina so na kawar da wannan tsarin a rayuwarta amma ita duk ta ƙi yarda, yanzu haka ba ta da lafiya amma ta ƙi yarda da temako na, amma yanzu komai ya zo da sauƙi kai ne za ka temake ni."
Yarima ya zaro ido ba tare da ya bi ta kan sauran zancen ba ya ce "Ta ya? kai da masoyiyarka kuma ni meye nawa a ciki?"
Abdul ya ce "Ta na da gardama fiye da kima don haka nake so ka je mata a sigar likita daga nan sai ka fara jan hankalinta, har ku fara soyayya, amma fa ka bi a hankali idan ka kuskure min sai an ji ni da kai har Kotun Ƙoli."
Yarima da mamaki ya cika shi ya ce "Kai, gaskya yaro yaro ne, ni ba zan iya wannan kasassaɓar ba, ka dai nemo wata mafitar." Abdulkareem ya ce "Ba ni da wata mafita sai kai, ka fahimta mana, ni fa wallahi bala'in tausayinta nake ji, ba wai na damu akan dole ta so ni bane, kawai ina sonta ne don na sanya ta farin ciki na gaji da ganinta cikin damuwa da wani mugun hali na rayuwa, daga tausayinta ma na ji gaba ɗaya ita nake son Aura, don Allah ka yi min alfarmar nan Dr in ba da haka ba za ta iya rasa ranta a banza domin ta fi ni faɗawa rashin lafiya."

Yarima ya yi shiru ya na nazari har na wani lokaci kafin ya ja numfashi, ba tare da hakan ya kwanta masa a rai ba ya amince don kawai Abdul ɗin ya nemi temakonsa ba zai iya ƙin yi masa ba.

Abdul ya yi matuƙar farin ciki da amincewar Yariman, su ka rabu da haka da cewar za su ƙarasa plan ɗin ta waya.
Hakan su ka yi Abdul ya zauna ya tsara Siyama da Yarima kuma su ka aiwatar kamar gaske.

Ci gaban labari

kamar yadda ya ce za ta ganshi da daddare bai yi ƙasa a guiwa ba ya je, ta sha surutu sai dai ta kasa sakin jiki da shi.
Abdul kuwa samun kanta ya sa ya manta da rigimar cikin gidansu, har sai da ya ko ya ga suna yi masa gani-gani sannan ya tuna akwai ƙura.

Tin daga wannan lokaci Abdulkareem da Aaminat su ka haɗe, ya na gwada mata soyayya iya iyawarsa, a nata ɓangaren kuwa tunanin halin da Yarima yake ciki take yi, haka kawai ta ji duk ta damu da shi, gashi ta na tsoron kiransa ya gayawa Abdul ta kira shi hakan ya jawo mata matsala don haka ta haƙura ta ci gaba da tunaninsa ba dare ba rana.

a ɓangaren Yarima kuwa tin daga ranar da ya rabu da Aaminat duk ya rasa nutsuwarsa, ba dare ba rana ba aiki ba rashin a kowace daƙiƙa ita yake tunani, a gefe guda kuwa yayarsa Raheena da Ammee sun saka shi gaba da tsangwama, ga sharri iri-iri da Raheena ta ke binsa da shi don kuwa har cikin ranta ta tsane shi.

©️INDO tare da AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)

Littafin Haɗaka ne💪🏾

Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA ONLINE WRITER'S

Tare da

Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S

Shafi 20

"salamu alaikum"
Abi yayi sallama ganin yarima be amsa ba yasa ya ƙarasa inda yake, dafa kafarɗar shi yayi, da sauri Yarima ya ɗago tare da zazzaro ido, Abi ya murmusa gami da cewa "Abubakar lafiya ina sallama amma hankalinka baya jikin ka!!!!???" "Abi babu komai" "A'a da wani abu faɗamin" rausayar da kai yayi ya ce "Abi dama... dama.. wata matsala ce" "matsala kuma" ya faɗa cikin sigar tambaya, kafin ya ce "faɗamin" ajiyar zuciya Yarima yayi gami da cewa "Abi maganar gaskiya wata yarinya ce Abdulkareem mai kasuwa yake sonta kuma Bazawara ce bata sonshi, shine ya turani wajen ta a matsayin ina sonta rana ɗaya mahaifinta ya ce nafito nan da wata ɗaya ze Aurar da ita ni kuma na laburtawa asalin masoyin ta yanzu ban san yadda suke ba"

tunda Yarima ya fara magana Abi yake binshi da kallon mamaki, gyaran murya Abi yayi kana ya ce "Abubakar maiyasa kuka aikata haka????.. ƙuruciya da shirme ya rinjayeku kunje kun ai kata ba dai-dai ba" Abi ya ƙarasa maganar cikin damuwa, Abubakar ya numfasa kafin ya ce Abi yanzu a bin damuwar shine ina son Aaminat nima" rassss rassss gaban Abi ya buga ya dubi Yarima ya ce "dama baka da tunani ka rasa hankalinka ne kasan kuwa me kake shirin aikata wa ????!!!!! cin amana fa karka manta shima fa ɗana ne nida mahaifin shi tamkar wa da ƙani muke fa!!!!"
ƙasa yayi da kai yana goge ƴar ƙwallar da ta gangaro kumatun sa Abi ya ce "kayi haƙuri ɗana, karka bari zuciyar ka tayi maka ɗanyan aiki kaji kaida Abdul ɗaya ne a waje na ba zan iya dannewa Abdul haƙƙin shi ba banda haka da na yi wani abu a kai" murmushin ƙarfin hali Yarima yayi ya ce "Abi ni dama bazan iya cin a mana ba ko makamancin haka ba, kuma zanyi ƙoƙari har naga Abdul ya mallaki Aaminat" murmusawa Abi yayi yace tare da cewa "ka kawar da tunanin komai kaji Allah yayi muku Albarka baki ɗaya" "Amin" yarima yace, suka kamo wata hirar suka ɗora,
Chapter 24 · 0% Book details