Sashe 9
Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gwauron numfashi na ja na sauke lokacin da nake ƙara saurarar voice ɗin a karo na uku.
"Maman Sultan ki ba ni address ɗin gidanki zan kawo miki atamfar taki da kaina." Shi ne abin da kunnuwana suke jiye mini Maman Nasmah ta faɗa. Girgiza kai na yi na ce. "Taɓ! Karen hauka ne ya cize ni da zan bari ki zo wannan akurkin gidan nawa da ko mai aikinki na san gidansu ya fi shi kyau nesa ba kusa ba." Tunanin ƙaryar da zan sharara mata kawai na fara yi. Ban kai ga yi mata reply ba na ga ta ce ko kuma na turo Driverna ko mai delivery ya karɓar mini. Ajiyar zuciya na sauke cikin jin daɗi, duk da hakan ma akwai yiyuwar asirina ya iya tonuwa, tunda ban da Driver bare wani mai delivery.
Reply na yi mata da duk yadda ta yi daidai ne. Ta ce tom shikenan na turo address ɗin nawa kawai ta ba wa drivernta ya kawo mini. Citson yatsa na yi na fara tunanin ƙaryar da zan shirga mata.
'Ki ba ta address É—in gidan Shamsiyya kawai, sai ta tura drivern nata can a matsayin nan ne gidanki.' Wani sashe na zuciyata ya ba ni wannan shawarar. Murmushi na yi tare da haÉ—e yatsuna biyu na É—ana na ce. "Yes!" Saboda Gidan Shamsiyya babba ne sosai shi ma, duk da a yanda nake hasashen gidajen Æ´an group É—inmu ba zai kai su ba, amma babu laifi, ya fi dai wannan akurkin namu.
Jikina na mazari saboda kar Maman Nasmah ta ga na daɗe ban yi mata reply ba na yi searching numbern Shamsiyya na tambaye ta tana gida gobe? Idan tana nan zan zo. Na yi sa'a tana online, kuma ina yi mata message ta ba ni amsa da. "Ayya ba na nan, mun yi tafiya Dubai da baban su Zuhura." Tagumi na yi cikin rashin jin daɗi na yi musu fatan dawowa lafiya, a raina na ce. 'Ku kuka yi auren jin daɗi Shamsiyya, mazajenku kullum cikin ɗaukar ku, ku tafi yawon shaƙatawa ƙasashen waje suke, mu kuwa namu ƙauye ma idan za a je a ga dangi sai an yi wata ana shirye-shirye da tara ɗan kuɗin mota. Saboda rashin zuciya, kowa yana fita ya nemi kuɗaɗe masu yawa amma ban da irin mazajenmu, da ba sa burin yin tarin arziƙin da za su zama hamshaƙai, sai dai ɗan wanda za a ci abinci a kwanta a makwanci duk munin shi da rashin kyan shi.' Tsaki na ja na koma chat ɗin Maman Nasmah na ce mata ba na nan mun yi tafiya Abuja sai jibi za mu dawo, amma zan ba ta address ɗin gidansu mai aikina ta aika akai a atamfar can, idan ɗan aiken ya je ya tura yaro ya ce ga shi a ba wa Salamatu. Na tura mata da address ɗin gidana a matsayin nan ne gidansu mai aikina. Ta ce tom shikenan babu damuwa. Kamar an sauke mini wani dutse mai nauyi da ya danne mini ƙirjina haka na ji, ganin na samun mafita, don haka kawai ba za ta zo ta ga gidana ta raina ni ba, in sha Allah sai mun koma tsamfatsetsen gida irin nasu kafin wata a group ɗin ta ƙara buƙatar zuwa gidana, saboda ba wannan ne karon farko da aka buƙata ba tunda na ce ni ma ƴar Kano ce.
Mun ci gaba da chatting da Maman Nasmah, ta ce na tura mata numbern mai aikin tawa, kar drivern nata ya kasa gane kwatancen, idan ya kakare sai ya kira ta. Ƙaryar ba ta da waya na yi mata. Emogin mamaki ta tura mini tare da faɗin. "Haba Hajiya Hafsah, kamar ke a ce mai aikinki ba ta da waya? Gaskiya ki siya mata." Murmushin yaƙe na yi kamar tana gabana ta ce. "Na siya mata fa ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba tana siyarwa, kin san halin mutane marasa ƙarfi, da sun ji rashi ko mene nasu ɗauka suke su siyar." Ta ce. "Haka ne, amma dai ki ƙara siya mata ko don irin haka." Na ce. "in sha Allah, kawai da ma na bari ta ɗan jigatu ne saboda kar ta kuma siyarwa."
Daga nan muka shiga hirar taron da za mu yi, ta tutturo mini agogo, ɗanƙareriyar sarƙa da ɗan'kunne na gold, haɗaɗɗen takalmi da rantsatstsiyar jakar da ta siya duka sababbi saboda taron ta ce ni ma na siya irinsu, mu yi komai iri ɗaya ranar. Jiya mijinta ya ba ta kuɗin ita ma duk ta siya. Tsam na yi a zaune ina rarraba ido, don na san ko gidan da muke zaune zan siyar kuɗinsa ba zai sai mini wannan kayan ba. Jikina a saɓule na ce mata zan siya in sha Allah, ba ta jira na tambaye ta ba ta turo mini price ɗin kowane. Kusan rikitowa na yi daga kan kujerar da nake kai saboda yawan kuɗin da na lissafa. Millions kusan biyar, a iya kayan sakawar rana ɗaya kawai. "Wanda ya ba da wannan kuɗin wanne irin kuɗi ne da shi, shi kuwa? Me yake yi yake samun kuɗi da Anas ba zai iya yi ba?" Na tambayi kaina a ruɗe. Zuciyata ce ta ba ni amsa da 'Rashin zuciya ne ya hana shi mana.' Dungurar da wayata na yi ina jin kamar na haushi bango tsabar takaicin irin mijin da na aura talaka. Da na san haka masu kuɗi suke hutawa da unguwar masu kuɗi nai ta zuwa da ina budurwa, da wani mai kuɗin ne zai gan ni ya aure, ni ma na yi rayuwar hutu da jin daɗi da kwanciyar hankali, na saka abin da nake so na ci wanda nake so a duk lokacin da na so. Dukan kaina na yi ina jin kamar na fashe da kuka. Miƙewa na yi ina tunanin abin da zan yi kafin ranar taron na samu kuɗin siyen abubuwa irin na Maman Nasmah ko da ba duka ba. A haka na koma ɗaki na dinga zarya, a ƙarshe na samu mafita biyu kafin na kwanta. Ta farko zan takura wa Anas akan ina buƙatar kuɗaɗe, ya je ya nemo mini a duk inda suke, ai su ma mazajen su Maman Nasman mutane ne kamar shi, kuma nema suke yi ba da kuɗin aka halicce su ba, don haka shi ma dole ya samo ya ba ni. Ta biyu kuma idan ya ƙi zan ce Shamsiyya ta ara mini duk abin da zan saka ranar, sai na cewa Maman Nasmah kawai gani na yi Abban Sultan ya siyo mini su. Da wannan tunanin na samu na iya bacci, duk da na raba dare kafin ya ɗauke ni.
Washegari na tashi cikin farinciki da ɗokin kawo mini atamfar da za a yi, hakan ya sa na yi ayyukana na gida cikin walwala tare da Anas. Bayan su Sultan sun wuce tahfiz saboda weekend ne Abbansu ya yi wanka ya shirya cikin kayan da yake zuwa aikin fenti da su, sana'arsa da ma fentin ne, ranar da babu aiki kuma zaman shago yake yi wa ubangidansu. Yana ƙoƙarin fita ganin kiran da ake ta yi masa a waya na dube shi na ce. "Wai wa yake kiran ka ne?" Yana duba ƴar wayar tasa ya ce. "Su Halliru ne mana, kin san su idan za mu je aiki idan ban fito ba sun ta kira na kenan, dole su sai dai mu fita tare." Ba yabo ba fallasa na ce. "Tom shikenan sai ka dawo." Ya ce. "Za mu iya kaiwa bayan Magriba, saboda gidan da za mu yi aiki babba ne sosai, kuma duk da haka ba za mu gama a yau ba." Gyara zama na yi na ce. "Ku yi ta zuwa tafka-tafkan gidaje aiki, ba ya burge ku ne ku ji da ma ku ne kuke rayuwa a cikinsa?" Murmushi ya yi ya ce. "Ai babu wanda daula ba ta burgewa a duniyar nan, sai dai idan Ubangiji bai ba ka ba sai ka yi haƙuri ka gode masa, tare da fatan ya ba ka a lahira." Taɓe baki na yi yadda ba zai gane ba na ce. "Amma duk da haka ai za ku yi ta kallon gidan ku ce da ma ku ne a ciki ko?" Ya ce. "A'a, a saboda me? Kowa inda Ubangiji ya ajiye shi nan ya so ya gan shi fa, don wani inda kake shi kuma nan yake fatan da ma shi ne a gurin, ai mu sai dai kawai mu ce Alhamdullillah, tunda Ubangiji ya bar mu da lafiyarmu da za mu nemi kuɗinmu na halal ai ya ga yi mana komai." Kamar na rufe shi da duka tsabar takaici da baƙinciki, wato shi ko damun shi manyan gidajen ba sa yi bare ya yi burin gina su watarana, shi komai da an yi magana ya ce kaza-kaza shi sarkin tawakkali, to ai Allan da kansa ya ce tashi in taimake ka. Ban ƙara magana ba har ya fita, yana ta cewa yau babu rakiya ne na yi masa banza.
Ƙarfe goma da mintuna na ɗora girki saboda kar su Safwan su dawo 12 ban gama abinci ba. Bayan na gama na gyara kitchen ɗin ina shirin yin wanka na ji ana knocking, ganin sha biyu da mintuna na san su Sultan ne suka dawo, da sauri na nufi ƙofar na buɗe ina faɗin. "Wannan bugun ƙof...."
Maƙalewa maganar ta yi a inda ban sani ba saboda ganin wadda ko a mafarki na gan ta sai na gane ta, duk da ba mu taɓa haɗuwa a zahiri ba. Wani irin abu na ji yana yawo a cikin jinina dunƙule-dunƙule saboda tsanani mamaki, ruɗewa gami da razani. Lokaci ɗaya na ji kaina ya fara juyawa saboda matsananciyar ɗimautar da na shiga.
"Maman Nasmah!" Na furta a fili tare da dafe Æ™irjina, idanuwa gabaÉ—aya sun yo waje kamar za su faÉ—o Æ™asa, tsabar firgici.........âœï¸
*Zeey Kumurya*
[3/8, 1:37 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
7.