← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 54

Sashe 25

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*Zeey Kumurya*✍️
[3/8, 1:40 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

*13.*

Ban gama yanke shawara ba shi ma kiran ya katse, ko 1 second ba a yi ba wani ya ƙara shigowa. Ɗagawa na yi cikin son jin dalilin wannan uban kiran da take zabga mini. Cikin faɗa kamar wata uwata ta ce. "Ina kika ajiye wayar ne nake ta kiran ki ba ki ɗauka ba?" Ba yabo ba fallasa na ce. "Ina parlour ne, wayar kuma tana ɗaki." Ta ce. "Okay, ya kuka yi da shi? Ya dawo miki da kayan naki?" Numfashi na sauke na ce. "A'a, ya ce ba shi ya ɗauka ba, na haƙura kawai na bar wa Allah." Cikin zuzuta ta ce. "Kin ce gobe ya ƙara ɗauka kenan? Shikenan kin buɗe masa ƙofar jidar miki abubuwa, ina nan na kasa sukuni saboda tunanin halin baƙincikin da kike ciki ashe ke har kin ware? Tsabar yadda na damu da abun ko abinci ban iya ci ba tunda kika faɗa mini." A sanyaye na ce. "To ya zan yi? Na yi bala'in na yi masifar, ƙarshe har saki na ya yi fa."
"Saki kuma?" Na ji ta faÉ—a a yanayin da na kasa tantance na murna ne ko kuma na ruÉ—u ne, saboda yadda ta yi kamar za ta fasa mini dodon kunne.
Na ce. "Eh, kin ga ya zama biyu kenan, da na farkon nan da ya ce idan na fita a bakin aure na, na ɗauka baraza ce kawai ya yi, ashe da gaske yake." Cikin karsashi ta ce. "To shi ne me? Ai akan gaskiyarki kike, kuma duk abin da ya faru shi ne ya janyo da ya ƙi kula da ke ya yi miki dukkan abin da kike so, ƙarshe ya ƙara miki da sata." Shiru na yi ban ce komai ba, don na rasa abin faɗi. Cikin sassauta murya ta ce. "Amma ki kwantar da hankalinki, ki zo gidana yanzu, ga ɗinkinki nan an kawo ki zo ki karɓa, duk abubuwan da aka sace kuma zan ƙara ba ki sabbi, har wayar ma duk zan siya miki sabuwa dal, idan da wadda kike so sai ki faɗa a kawo ta, idan kuma ba ki da choice zan ce a kawo miki irin ta hannuna." Cikin farinciki na ce. "Da gaske za ki ƙara ba ni kayan, har da sarƙar gold ɗin?" Ta ce. "Mene a ciki? Yanzu ina yi wa Hubby waya zai saka a kawo komai, wannan ba komai ba ne ai a gurinsa, kuma ko me na ce masa ina so babu ɓata lokaci yake mun, so kar ki wani damu. Ina son ki fito fes kamar kowa ke ma a gobe." Dogon numfashi na ja na sauke na ce. "Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ya ƙara buɗi, ya bar ƙauna tsakaninki da mijinki." Ba ta amsa ba ta ce. "Ki yi maza ki zo, yanzu zan tura miki address ɗin."
A gaggauce na shirya cikin doguwar rigar atamfa cikin zumuɗi. Jikina har tsuko yake saboda farinciki. Na yi niyyar bin shawarar Naja, amma sake ba ni kayan da Maman Nasmah ta ce za ta yi ya sa na manta da wata Naja'atu da batunta ma gabaɗaya. Ban damu da rashin dawowar su Sultan ba har biyu saura na fice daga gidan. Na samu mai napep muka tsadance ya kai ni har ƙofar gidan Maman Nasmah.
Tun daga farkon unguwar tasu na tabbatar wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, saboda maka-makan gidajen da na fara tozali da su, sakin baki na yi ina ba wa na mujiyata abinci. Gabaɗaya sai na ƙara raina kaina. Muna tafe ina waya da ita tana faɗa mini inda zan na cewa mai napep ɗin ya bi. A bakin wani ƙatoton gida muka tsaya. Da sauri na zuro kaina kamar zan faɗo ina ƙare masa kallo, ban san lokacin da bakina ya furta. "Aljannar duniya." Ba. Sai da drivern ya mini magana sannan na dawo cikin hayyacina na fita na sallame shi. Ban san ya zan iya fasalta girma da ƙawatuwar gidan Maman Nasmah ba tun daga waje ma. Don ko tantama ba na yi idan na ɗaga kaina na ce zan hango ƙarshen tsayinsa sai ɗankwalin kaina ya faɗi. Ina nan tsaye da baki a buɗe aka buɗe ƙaramar ƙofar makeken gate ɗin gida, wani matashi ne ya ƙaraso inda nake ya ce. "Ke ce baƙuwar Hajiya?" Ɗaga masa kai na yi don ruɗewar da na yi ta hana ni magana. Ya yi gaba na bi bayan shi ina tuntuɓe saboda kalle-kalle. Mun yi tafiyar mintuna biyar kafin mu kai inda part ɗinta yake. Ya danna wani abu da ban san mene ne ba, babu jimawa aka buɗe ƙofar da ita ma ɗaukar ido take ya ce na shiga. Zan cire takalmi yarinyar da ta buɗe ƙofar ta ce na shigo da shi. Duk yadda na so sakaya ƙauyancina amma sai da ya bayyana kansa, saboda tsintar kaina da na yi a wani tsamfatsetsen parlour, wanda ya wadatu da fitilu masu wasu wani irin ƙyalƙyali da haske. Ajiyar zuciya na sauke na lumshe idona tare da ƙara baza hancina, don sake shaƙar sassanyan ƙamshin da yake tashi a parlourn a wadace. A iya tunanina ban taɓa tsammanin za a samu kamar wannan falon a Nigeria ba sai dai a ƙasar waje. Sai da muka wuce faluka uku, a na huɗu wanda yake upstairs muka tarar da Maman Nasmah. Fuskarta ɗauke da fara'a sosai ta taso ta rungume ni tare da yi mini sannu da zuwa. Na amsa cikin yaƙe, don ko mai aikinta da ta yi mini jagora ta fi ni kyan gani, don daga gani suturar jikinta ma ta fi tawa tsada. Ta zaunar da ni bayan ta baya wa yarinyar umarnin ta kawo mini drinks. Tana ta jana da hira amma na kasa sakin jikina, satar kallon parlour'n kawai nake ina faɗin. "ALLAHUMMA ARZUƘUNI" A cikin raina. Ita kanta sai na ga ta ƙara yi mini kyau fiye da ganin farko da yi mata, yadda ta hakimce a kan kujera cikin shiga ta alfarma tana latsa waya a gayance ba ƙaramin burge ni ya yi ba. Hakan ya ƙara girmamar burina na son rayuwar kuɗi da hutu. Ta wata ƙofa da ke cikin parlour'n ta shigar da ni inda dinning yake shi kaɗai da zan ci abinci, haɗuwar gurin da tsaruwar shi da kyawun dinning ba za su faɗu ba, food flaks ɗin da aka zuba abincin ma kaɗai abin kallo ne. A taƙaice dai duk yadda nake tunanin girma da ƙawatuwar gidan Maman Nasmah ya wuce nan, don tamkar rainon daji haka na koma saboda ƙauyanci. Bayan na yi Sallah ina zaune a bedroom ɗin da ta kai ni ta shigo ta ce. "Kamar kina  cikin damuwa ko?" Na ce mata. "A'a babu komai." Baki ta taɓe ta ce. "Ai ko kin ɓoye fuskarki ta fallasa ki, kuma na san ba zai wuce akan wancan mijin naki ba ne, da zuwa yanzu ya kamata a ce kin gane ba son ki yake ba, tunda har akan abu ƙanƙani ya iya sakin ki." Girgiza kai na yi na ce. "Wallahi ba shi ba ne, don yanzu da shi da babu duk ɗaya ne a gurina." Murmushi ta yi ta ce. "Ko ke fa, anjima za a kawo kayan naki, yanzu mai lalle ta zo tana parlour, mu je ta yi mana ko iya baƙi ne, tunda time ya ƙure ba damar yin ja." Na ce. "Tom shikenan."
Ana yi mini lallen Maman Nasmah tana ƙara kushe Anas da aibata shi, da nuna mini ko ya dawo ya ce na koma kar na yarda, ni dai na yi shiru ban ce komai ba, don har yanzu zafin sakin bai bar sukar zuciyata ba.
A ɓangaren Maman Nasmah kuwa wani irin farinciki da annashuwa take ji, duk da a plan ɗinta saki uku take so Anas ya yi wa Hafsah kafin ta shiga cikin rayuwarsa, ta yadda babu aure a tsakaninsu kenan bare ya ce zai mayar da ita. Tana lura da yadda ta ɗimauce da ganin gidanta, ta dinga murmushi a ranta tana faɗin. 'Kina burin kasancewa a cikin irin wannan daular, ni kuma ina burin kasancewa da mijinki da kike ganin shi a banza, wanda duk wannan daular da nake ciki ta kasa gamsar da ni da sanya ni a cikin farinciki, saboda rashin samun abokin rayuwa kamar shi.'
Chapter 25 · 0% Book details