Sashe 42
Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Kwana uku a tsakani Mansur ya turo magabatansa suka kawo kuɗin aure da sadaki, Kawu da wani abokinsa da maƙotanmu guda biyu ne suka karɓa, duk da Kawu bai so haka ba, don shi tambaya kawai suka ce masa za a yi ban da kawo kuɗi, ya yi niyyar ƙin karɓa amma ragowar suka ce a karɓa kawai, yarinya ta samu miji ba a toshe ta ba. An sanya biki sati biyu kacal, wanda ya kama saura kwana uku azumi a lokacin. Duk wanda Kawu yake da tabbaci a kansa ya saka ya yi masa bincike akan Alhaji Mansur, kuma Alhamdulillah ta ko'ina sakamako mai kyau ake kawo masa. Hakan ya sa hankalinsa ya kwanta ya bi abin da addu'a kawai.
Sosai nake shirin bikina, duk da ban da ɗan tayi sai Maman Nasmah da Inna Habi. Don Naja tun ban fi kwana biyu da dawowa gida ba na yi blocked ɗinta a ko'ina da na san za ta same ni, don wani irin haushin ta nake ji. Na kuma ƙudurce a raina ba zan nema ta ba har sai na yi aure, na kira na sanar mata ta zo ta ga irin mijin da na aura da gidan da nake. Ƴan group ɗinmu babu wanda ya san aure na ya mutu bare ya san zan sake wani auren, da ma haka muka tsara ni da Maman Nasmah, ba za su taɓa sani ba, shi ya sa babu wanda na gayyata, haka ma ƙawayena da ƴan unguwar da na zauna, duk ban faɗa musu ba. Kuɗi sosai Idonnera yake tuttula mini na hidimar biki, amma ko sau ɗaya ban taɓa bari Kawu ya sani ba. Na je an yi mini gyaran jiki, na haɗa wa kaina lefe a gidan Inna, na sissiya abincin da za a dafa ranar bikin. Kayan ɗaki da na kitchen da ma ko tsinke ba zan tafi da shi ba, ya riga da ya siya komai. Amma Kawu bai san da batun ba, don wata gonarsa ya ɗaga ya siyar ya ba wa Inna Habi kuɗin ya ce a yi mini komai da su. Ta nuna masa kuma an siya suna nan a gidanta, har jeren ƙarya ta ce masa an tafi ana i jibi ɗaurin auren. Tun daga zuwan da Mansur ya yi na farkon nan sau ɗaya ya ƙara dawowa, saboda ayyuka da abubuwa da suka sha masa kai. Ina ta hidima amma zuciyata cike take da kewar ƴaƴana, na so zuwa har ƙauyen su Anas na kwaso abuna, amma sanin Kawu ba zai yarda ba ya sa na bari sai na tare bayan na gama cin amarci na je na ɗauko su ko ta halin ƙaƙa. Ranar Juma'a ɗaurin auren ya kama, ranar Alhamis na je aka yarfa mini kitso tare da rangaɗa mini ƙunshi. Bayan an gama na tura masa da hotunansu, sai ya ce ba su fita ba sosai, Camerar da na yi amfani da ita ba ta da kyau, bari ya turo a kawo mini waya, da ma yana ta son ya sauya mini kuma ya sha'afa. A daren ya aiko wani yaronsa ya kawo mini sabbin wayoyi, keypad da iphone. Ita kanta keypad ɗin ban taɓa ganin irinta ba, mai kyau ce sosai kuma daga gani babu tambaya da kuɗi mai yawa aka siye ta. Ban yi amfani da su ba na ce sai Allah ya kai mu gobe bayan na tare a gidana.
Washegari ta kasance rana mafi girma da tarihi a rayuwata, rana mai ɗumbin farinciki da murnar cikar burina. Duk da ban yi gayya ba amma gidan cike yake da mutane, don ita Gwaggo ta yi, ƴan'uwanta da na Kawu da maƙota. Dangin mahaifiyata kuwa babu wanda ya zo, sun ce abun ya zo a ƙurarren lokaci, sai aike suka yi mini tare da alƙawarin daga baya za su zo su ga gidan nawa.
Ƙarfe biyu na rana aka ɗaura aurena da Alhaji Mansur Ibrahim Idonnera, a babban masallacin juma'ar unguwarmu. Bakina ya ƙi rufuwa saboda farinciki, na je aka yi mini makeup mai kyau, na shirya cikin wani tsadadden lace milk color. Maman Nasmah ta zo amma ba ta jima ba ta tafi, saboda za ta je gidansu Ango, don su a event ma suke yinin ba a gida ba. Mansur ya so na je, amma na ce masa a'a don na san Kawu ba zai taɓa bari ba. Yadda nake cikin nishaɗi da walwala haka ma ango yake, bini-bini ya kira ni ya ce ya rasa ina zai saka kansa saboda farinciki, kamar ya zauce haka nake ji. Murmushi kawai nake yi masa. Saboda yadda ya nuna ya ƙagu a kai ni ya sa ana yin sallar la'asar aka tafi kai ni, bayan Kawu ya yi mini doguwar nasiha mai ratsa jiki. Mota ɗaya kacal ya kawo kamar yadda na ce masa, saboda har yanzu Kawu bai san mai kuɗi ba ne sosai, sadaki da kuɗin aure duk kuɗi kaɗan na ce masa ya bayar.
Daga Inna Habi sai wata Æ™anwarta da wata maÆ™ociyarmu aka tafi kai ni, unguwar da nisa daga tamu, hakan ya sa sai daf da Magriba muka Æ™arasa. Tun daga farkon unguwar muka fara cin karo da tafka-tafkan gidajen, wanda tsabar tsaruwar su kamar za su yi magana. Ta cikin mayafi nake Æ™are wa ko'ina kallo. Layinka unguwar kowane shafe yake da titi luwai-luwai, a bakinsa kuma an saka gate. Future house É—in da nake fata dai nan aka kai ni. Ban san ta yanda zan iya fasalta girma, kyau, da haÉ—uwar gidan da aka kai ni ba, don duk tunanin mai tunani ya wuce nan. A wani Æ™aton É—aki na alfarma da ke hawa na uku a gidan aka ajiye ni, su Inna suna yin sallar Magriba suka yi mini sallama suka tafi suka bar ni daga ni sai halina.........âœï¸
*Zeey Kumurya âœï¸*
[3/8, 1:43 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGH PENS*
FREE BATCH
*22.*