← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 54

Sashe 20

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ce. "Haba, mene na godiya, ai na faɗa miki tamkar ƴar'uwata ta jini haka na ɗauke ki, don haka babu godiya a tsakaninmu, abin da nake so da ke kawai duk wani abu da ya shige miki duhu ki faɗa mini zan ba ki shawara in sha Allah." Na ce. "Na gode, zan kira ki anjima na faɗa miki duk yadda muka yi da shi." Ta ce. "Allah ya kai mu, ina ƙara jaddada miki dai kar ki raga masa fa, ki buɗe masa wuta ya fito miki da kayanki." Na ce. "In sha Allahu." Tare da kashe wayar na yi cilli da ita cikin ƙunar zuci kamar ita ce Anas ɗin. Wani irin tafarfasa da turirin bala'i ne kawai yake kai kawo a cikinta. Maganganun Maman Nasmah sun yi zaman kafaffen rodi a cikin zuciyata, na yi amanna da yarda da su ɗari bisa ɗari, don a yanzu ko tantama ba na yi Abban Sultan ne ya sace mini kayana. Rasa inda zan saka kaina na ji daɗi na yi, na dinga safa da marwa daga tsakar gida zuwa ɗaki kamar zautacciya, filin zuciyata cike da tanadin tulin buhunhunan tijara da rashin mutuncin da zan zazzage a kan Anas. Ina bakin ƙofar soro na haɗa kaina da bango na ji an buɗe ƙofar gidan an shigo, kamar wadda ta ga abin tsoro haka na ɗago kaina da sauri na bi shi da mugun kallo, ban amsa sallamar da ya yi ba na fara magana cikin ɗaga murya. "Ina kayana? Kar ka ce mini komai kawai ka fito mun da kayana." Sororo ya yi yana kallo na cikin rashin fahimta, fuskarsa ɗauke da maɗaukakin mamaki ya ce. "Rashin kayan ne ya zautar da ke haka kike sunbatu marasa kan gado?" A fusace na ce. "Idan akwai abin da ya fi mahaukaciya ka kira ni da shi ma Anas bai dame ni ba, abin da na sani kawai wallahi sai ka dawo mun da abuna, ka je duk inda ka kai ma ko ka siyar da ka sata ka karɓo k...." "Sata kuma? Ni kike alaƙantawa da sata yau? Me zan yi miki da kayanki? Me za su ƙare ni da shi?" Ya yi maganar yana nuna kansa cikin ɓacin rai. Ɗage kafaɗa na yi na ce. "Oho maka, ka na tsammanin ba zan gane kai ba ne ka sata? Daga ni sai kai a gidan idan ba kai ba wa zai ɗauka?" Girgiza kai ya yi cikin takaici ya ce. "Wallahi Hafsah inda kika ajiye kayanki ma ban sani ba bare na ɗauka, rantsuwa ba ɗabi'ata ba ce kin sani, amma na rantse miki da zatin Allah ba ni na ɗaukar miki kayanki ba, ki dai tuna ko kin cilla su wani gurin kin manta, ban da haka wa zai ɗaukar miki? Wa ma ya shigo gidan?" "Kai mana!" Na faɗa ina zabga masa harara. Numfashi ya sauke ya ce. "Da farko na ɗauka da wasa kike da kika nuna kike zargi, amma yanzu ban ga alamar hakan a tattare da ke ba, ban taɓa tunanin akwai ranar da za ta zo a rayuwarmu ki alaƙanta ni da sata ba, kin fi kowa sani na da abin da zan aikata da wanda ba zan yi ba, ban san me na yi miki ba Hafsah kika zaɓi ki ta ɓata mini rai, kar ki kai ni bango na yanke hukuncin da duk ba zai mana daɗi ba." Baki na taɓe na ce. "An yi walƙiya na ga duk wasu mugayen halinka da a da son ka ya rufe mini ido ba na gani, don haka ko me za ka yi ka daɗe ba ka yi ba, ƙarƙari ka ce za ka sake ni ko? To idan ba ka sani ba ma ka sani shi na fi buƙata a yanzu, don in na rabu da kai wanda ya fi ka komai da komai zan aura." Taune leɓensa ya yi yana hucin ɓacin rai ya ce. "Huɗubar da suke yi miki kenan?" Na ce. "Oho maka, ni dai yanzu ba dogon surutu na nema ba, kawai ka fito mini da kayana, don ba ka siya mini ba, ba ka isa ka ɗauke wanda aka ba ni ba wallahi." Ya ce. "Sai ki yi ta yi, Allah ne shaidata kuma shi zai bayyana gaskiya." Cikin zaƙalƙala na riƙe ƙugu na ce. "Aikin banza, gayyar tsiya kawai da rashin zuciyata, ban da mugun hali babu abin da mutum ya iya, ko da yake an ce gado ba karambani ba ai, tunda ba ka tashi ka ga ana yi a gidanku ba ai kai ma ba ka yi a gidanka ba." Cak ya tsaya daga ƙoƙarin shiga ɗakin da yake, ya juyo ya zuba mini idanunsa da suka yi jajir ɗin bacin rai, muryarsa na rawa ya ce. "Hafsah! Me kike nufi?" Ba tare da tsoro ko dogon nazarin sakamakon da maganata za ta janyo ba na ce. "Abin da yake akwai shi nake nufi, wanda ya kasa riƙe ɗansa ya turo shi almajiranci ta yaya zai iya kula da matarsa har ya yi mata duk abin da take so? Ka ga kenan ba a ƙasa ka ɗauka ba." Jikinsa har tsuma yake saboda tsananin fushi da ɓacin rai, don da farko na ɗauka duka ne zai yi idan ya ƙaraso inda nake, amma sai na ga ya kama hannayena ya damƙe a cikin nasa, muryarsa kamar mai shirin fashewa da kuka ya ce. "Cin mutuncin har da iyayena da suke ƙasa Hafsah? Kar ki fara don Allah! Kar ki fara abin da zuciyata ba za ta ɗauka ba wato sako iyayena a cikin sabgar mu, don ba zan jure ba, zuciyata za ta iya tunzura ni na aikata abin da ban yi niyya ba, kar ki bari mu yi asarar juna saboda wasu can da ba ki san su ba, ba ki san da alkhairi suke nufin ki ko da sharri ba. Please na roƙe ki ko dan su Sultan, ina son ki, ban shirya rabuwa da ke. Kuma kar ki manta yanzu igiyar aurenmu saura biyu, furucin da na yi a baya na idan kika fita a bakin aurenki ya riga ya tabbata saboda kin fitan, na shiga tashin hankali a sanadin hakan, amma ke na ga ko a jikinki, to don girman Allah kar ki bari saura biyun ma su tsinke mana." Dogon tsaki na ja tare da fizge hannuna, ko kaɗan ban ji tausayinsa ko kuma na ji kalamansa sun ratsa ni ba, sai ma wani irin haushin shi da ya ƙara rufe ni, musamman da na tuno gobe ne taronmu, kuma shi nake zargi da sace abubuwan da za su saka na zama tauraruwa a taron, da kuma baƙincikin ƙin siyo mini wayar da ya yi, alhalin matan group ɗinmu komai suke so mazajensu suna yi musu cikin gaggawa. Ga uwa uba huɗubar Maman Nasmah, da ta dinga jaddada mini na tabbatar na matuƙar ɓata masa rai, ya ji babu daɗi shi ma kamar yadda na ji. Cikin son ƙara ƙona masa rai na ce. "Ai da ma wanzami ba ya son jarfa, to tunda ba ka so in dinga taɓa maka Iyaye, ka sake ni na je na auri wanda zai so ni, ya gatanta ni, ya yi mini duk abin da nake so a duniya, mai kuɗi ba faƙiri irinka ba." Bai ce komai ba ya juya kamar zai tashi sama alamun ba ya son ci gaba da jin maganganun da nake yi. Jikinsa sai kyarmar tsantsar ɓacin rai yake. Da sauri na bi bayansa na riƙo rigarsa, cikin fitsara na ce. "Na gaji! Na gaji da wannan takaicin naka! Ka sawwaƙe mini idan ka cika ɗan halak a cikin Binta da Musa!" Ban san lokacin da ya juyo ba sai ji kawai na yi ya ɗauke ni da wani wawan mari da ya saka ni kifawa. Da sauri na dafe kuncina tare da ɗaga kaina na kalle shi ina hawaye. Sai na ga shi ma nasa idanun da suka kaɗa suka yi jajir cike suke da ƙwalla, muryarsa a dashe saboda tsananin tashin hankali da ɓacin rai ya ce. "Ki je na sake ki Hafsah!".......✍️
Chapter 20 · 0% Book details