← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 54

Sashe 34

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

gata a duniyar nan bayan Ubangijin da ya halicce ki sama da Anas ba." Cikin ƙosasa da surutunta na ce. "Shi gatan ne da shi? Yanda ba ni da kowa shi ma hakan yake." Tana gyara zaman jakarta a kafaɗarta ta ce. "Shi namiji ne, ba shi da matsalar neman matallafi a rayuwa kamar ke, zai iya yin rayuwarsa shi kaɗai ma a cikin gidansa, amma ke kuwa a matsayinki na mace dole sai kina ƙarƙashin wani!" Tsaki na kuma ja ban tanka mata ba. Ta ce. "Hmm, Hafsah kenan, yau ni kike wa haka akan wasu can haɗuwar jiya-jiya?" Na ce. "Na yi ɗin, hurumin da ba naki ba da kika shiga shi ya janyo miki." Ta ce. "Haka ne, kowa rai ya yi wa daɗi babu kamar mai shi, in sha Allah daga yau ba zan ƙara yi miki magana akan wannan rayuwar da kika ɗaukar wa kanki ba." Cikin kora da hali na ce. "Ya fi miki alkhairi, ki sakar mini mara ki bar ni na yi rayuwata yadda na ga dama." Sallama ta mun ta tafi bayan ta ƙara yi mini bitar maganganunta da kwata-kwata ba su da mazauni a gurina, don tamkar amahin shata haka na ɗauke su. Ban da ƙona mini rai ma babu abin da suke yi. Na fara yarda da maganar Maman Nasmah da ta ce hassada da baƙincikin mu'amalata da ƴan gayu take yi. Wunin yau cikin tufka da warwara na yi shi, don ko girkin rana ban yi ba, na jiƙa wa su Sufyan garin kwaki suka sha suka wuce islamiyya. Da suka dawo kuma na ba su ragowar abincin da suka ci da safe, na ce musu idan uban nasu ya dawo ya nemo musu abin da za su ci da daddare ko ya dafa musu. Ni kuma na ci biscuit ɗin da na siya da yawa na ajiye saboda da irin haka, na kora da ruwa. Daf da Magriba na ɗauko bola na wargatsa a tsakar gida da soro, na ɗebi ruwa na kwara a kai. Da kaina na fita ƙofar gida na ɗebo ƙasa na tila akai. Na yi hakan ne saboda Anas, don na san ba ƙaramin ɓaci ransa zai yi ba idan ya zo ya tarar da gidan a haka, saboda ba ya son ƙazanta ko kaɗan a rayuwarsa, ga shi da ƙyanƙyami, kuma kafin ya fita sai da ya share gidan tas. Toilet kuwa da Sufyan ya yi bayangida hana shi flushing na yi, na ƙara damalmala bakin masan na bar shi a haka, duk saboda ya gani ransa ya ɓaci. Da ƙyar Sultan ya iya yin alwala, sai kakkame jikinsa yake ya na ɓata fuska cikin ƙyanƙyami. Sufyan kuma ya na fitowa daga ɗaki ya kama bakinsa ya ce. "Mami wa ya yi mana wannan ƙazantar a gida?" Na ce. "Ban sani ba don ubanka." Jijjiga kai ya yi yana keɓe baki ya ce. "Taɓ, idan Abba ya dawo zai yi faɗa, ki yi sauri ki gyara kar ya zo ya gani." Ban kuma tanka masa har ya ƙaraci surutunsa ya yi shiru, Sultan kuwa da ya san ni na yi bai ce komai ba. Bayan ya idar da alwalar ya ɗauko tsintsiya zai fara shara na ƙwace na kora shi waje. Tare da suka dawo da Baban nasu, ina daga ɗakin su Sultan na ji yana cewa. "Mene wannan kuma a gidan kamar kwata ?" Daga nan ban san ya aka yi ba sai ji na yi ya faɗi tim a cikin cakwalin. Da sauri na fito na haske shi, ganin shi na yi kwance male-male, ƙoƙarin tashi ya yi cikin hanzari, ban san lokacin da wata irin dariya ta ƙwace mini ba, saboda tozalin da na yi da fuskarsa ta yi dagaje-dagaje da ruwa da ƙasa da bolar da na zubar.........✍️
Chapter 34 · 0% Book details