← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 54

Sashe 30

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ina shiga cikin gida ana ɗauke NEPA, wani irin ƙunci da takaici ne suka cika ni, na tuno tunda na je gidan Maman Nasmah ko motsi wutarsu ba ta yi ba, haka ma gidan Aunty Billy. Tsaki na yi na zaro sabuwar wayata na kunna fitila na haska gidan. Kayan hannuna na fara kaiwa kitchen sannan na shiga toilet na yi alwala na yi Sallah. Bayan na idar na zauna bitar abubuwan more rayuwar da na gano, babban abin da ya fi burge ni yadda idan mutum zai shiga unguwar su Maman Nasmah sai an tsayar da shi a bakin gate ɗin ginin da ya zagaye unguwar, an tambaye shi gidan wanda zai je ya kira shi sun yi magana da security ɗin. Sabga cikin mutunci da arziƙi dai. A cikin gidanta kuwa babu wani abu mara kyau da ƙayatarwa, toilet kaɗai ya isa ɗauke wa mutum dukkanin damuwarsa saboda tsananin kyansa, ga fanfon ruwan sanyi daban na ruwan zafi daban. Gabaɗaya yanzu da na gan ni a gidana sai na ji duk na ƙuntata, kamar ba na samun wadataccen nunfashi ma tsabar ƙanƙantar gidan.
Sai wajen goma ya shigo gidan shi da su Sultan, bai kula ni ba, ni ma ko kallon shi ban yi ba. Na É—auki abincin da na taho da shi muka ci tare da Æ´aÆ´ana, muna ci suna labarin gidan da suka je, bayan na gama shan uwar tambayar ina na je na tafi na bar su.
Ni kaɗai na kwanta a ɗakina don Anas ko parlour'n bai shigo ba, na gane nufin shi, so yake na je na ba shi haƙuri, ni kuma abin da bai isa ba kenan a yanzu, don ba zan iya fama da talauci da faɗin rai ba.
Kusan raba dare muka yi muna hira da Maman Nasmah, ta ba ni labarin abubuwan da aka tattauna bayan na taho, ni kuma na faɗa mata yadda muka kasance da Abban Sultan. Ta ce ko za mu shekara a haka kar na sake na ba shi haƙuri, don ita mijinta tunda suke ba ta taɓa ba shi haƙuri don ta yi masa laifi ba, ko ita ce mara gaskiya shi yake bin ta yana lallaɓa ta. Ina ta son na ba ta labarin biyo nin da mijin Aunty Billy ya yi amma har ta sauka daga online ban faɗa mata ba. Yau ma sai na ji na kasa bacci, saboda yadda gadona tun na aure yake ta ƙarar tsufa, ga katifar duk ta lotse, ta wani gurin har layi-layin katakon karagar gadon ana jiyowa. Luntsumemen gadon da na kwana a kai jiya kawai nake tunowa, na san da shi ne da tuni bacci ya ɗauke ni yadda na kwaso gajiyar nan. Tashi zaune na yi ina firfita saboda zafin da ya addabe ni da sauron da yake ta mun kuwwa a kunne duk da na ɗaura net. Na san in dai ba nepa aka kawo ba, ba zan taɓa iya bacci a cikin wannan izayar ba. Jiya na kasa bacci saboda kewar ƴaƴana da mijina duk da ina cikin ɗakin da babu wani abu na wahala zai hana ka bacci, yau kuma ga ni a tare da iyalin nawa, amma azabar sauro da zafi sun hana ni bacci. Kenan da a irin gidansu Maman Nasmah nake tare da ƴaƴana da mijina babu abin da zai dame ni bare ya hana ni bacci? Jinjina kaina na yi ina ayyanawa a raina ko ta halin ƙaƙa sai mun bar gidan nan mun koma wani ƙato wanda ya haɗa komai na rayuwa nan kusa, don na gane kamar yadda ba zan iya rayuwa ba su Sultan ba haka ba zan iya ci gaba da zama a cikin talauci da ƙuncin rayuwa ba. Tilas ko ni ko Anas mu nemo kuɗi ko a ina ne mu yalwata rayuwarmu.
'To amma ni a ina zan samo?' Zuciyata ta yi mini wannan tambayar.
Mijin Aunty Billy da one million ɗin da ya ce zai ba ni don kawai na saka kati ne ya faɗo mini a rai, tamkar shi ne amsar tambayar da zuciyata ta yi mini........✍️

*Zeey Kumurya*
[3/8, 1:41 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

*BRIGH PENS*
(FREE BATCH)

*16.*
Chapter 30 · 0% Book details