Sashe 32
Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
A ɓangaren Maman Nasmah kuwa tsalle ta doka cikin farincikin murnar samun wani chance ɗin a sauƙaƙe na raba Hafsah da Anas. Za ta yi amfani da hakan tai ta ƙara cusa mata son rayuwar gidan kuɗi har ta yi nasarar raba sun. A cikin mazan da take hulɗa da su za ta haɗa ta da guda ɗaya su dinga waya da chatting a matsayin shi ne mijin Aunty Billy. Don ba ƙaramin daɗi ta ji ba da Hafsah ta ce mata ba ta karɓi card ɗinsa ba, bare ta kira shi ya ci gaba da yi mata maganar banza asirinta ya tonu na ƙaryar da ta zabga mata. Ita kanta ba ƙaramin kaɗuwa ta yi da ta ji mijin Aunty Billy ya bi Hafsan, kuma tsabar ƙwanƙwararre ne shi ya bayyana mata manufarsa ba tare da tsoron komai ba. Murmushi ta yi a fili ta ce. "Ashe ba namu mazajen ne kaɗai bunsuraye ba." Za ta ci gaba da nuna wa Hafsah son ta take yi tsakani da Allah da kuma burin taimakon ta, yadda duk abin da ta ce mata ta aikata za ta yi ba tare da jinkiri ba.
Wuni na yi ina abu ɗaya wato tunanin mafita, a ƙarshe na yanke shawarar amincewa da abin da Maman Nasmah ta faɗa, na rabuwa da Anas na fita na auri mai kuɗi irin mijin da nake fata da burin samu. Idona ya rufe gabaɗaya, ƙaton gida da rawuwar jin daɗi kawai nake hangowa, na manta da ƙalubalen da za su biyo bayan faruwar hakan. Da kaina na kira ta na sanar mata na amince, ta nuna mini ta ji daɗi sosai, don mutumin mai suna Alhaji Kyauta ya ƙara kiran ta a kaina, ta ce masa wasa take yi masa ba ni da aure za ta haɗa mu. Na nuna mata ba zan iya mu'almala da shi da aure na ba, ta san abin da za ta faɗa masa kafin na rabu da Anas sai mu fara magana a lokacin. Ta ce tom shikenan babu damuwa, amma na yi komai cikin sauri kar a ja lokaci, na ce mata in sha Allah.
Tun daga ranar na fara sauke wa Abban Sultan tsibiri-tsibirin kwandon rashin mutunci da tijara, wulaÆ™ancin yau daban na gobe daban. Duk abin da na san ba ya so shi nake yi, wanda yake so kuma na daina yi. Ci gaba da maganganun abubuwan kuÉ—i da turo su a group É—inmu shi yake Æ™ara tunzura ni, don na sha alwashin ba zan bari wani taron da za mu kuma yi ya zo ina cikin wannan akurkin gidan ba. Saboda an tsayar da cewar duk bayan wata shida za mu dinga yin taron, amma ba za a sake yi a gida ba sai dai a kama guri..........âœï¸
*Zeey Kumuryaâœï¸*
[3/8, 1:41 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGH PENS*
(FREE BATCH)
*17.*