← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 54

Sashe 26

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sai da Naja ta koma gida ta huta sannan ta kira Anas, duk da halin tashin hankalin da yake ciki da zazzaɓin da ya rufe shi lokaci ɗaya amma da sauri ya ɗaga yana fatan Allah ya sa zancen Hafsah za ta yi masa, saboda duk da abin da ta yi masa ko kaɗan son ta bai ragu a cikin zuciyarsa ba. Bayan Naja ta yi sallama ya amsa ta ce. "Abban Sultan idan babu damuwa ina son don Allah mu yi wata magana ne da kai, idan kana free yanzu, in kuma kana abu idan ka gama sai ka kira ni." Ya ce. "A'a babu abin da nake yi, ina sauraren ki." Ta ce. "To Masha Allah, ɗazu na zo gidanka na riski wani mummunan al'amari da bai mun daɗi ba ko kaɗan wallahi, ya kuma saka ni a cikin tashin hankali mara misaltuwa, kana nan ma na zo, amma saboda yanayin da kake ciki na san da ƙyar idan ka gan ni. Hafsah ta faɗa mini komai da yake faruwa, na yi mata faɗa sosai tare da ba ta shawarwari, kuma na ga alamar ta ɗauka daga yanayin yadda jikinta ya yi sanyi. Shi ya sa na kira na roƙi alfarmarka, akan don Allah ka yi haƙuri ba don halinta ba, ka mayar da ita ɗakinta, saboda tana gidan ma a can na baro ta, na hana ta tafiya." Numfashi ya sauke ya ce. "Anya kuwa Hafsah za ta risina? Don abubuwanta sun daina ba ni mamaki yanzu sai dai tsoro. Don da farko ma na yi tunanin ba ta cikin hayyacinta ne, sai daga baya na gane tsantsar iskanci ne da burin shirme da ruɗin shaiɗan." Naja ta ce. "In sha Allahu ba za ta sake ba, ka yi haƙuri, ta faɗa mini komai babu abin da ta ɓoye mun, amma ni na yi mata uzuri, saboda rashin mai ba ta shawara da ƙarancin wayewa sun taka muhimmiyar rawa a wajen habbaƙa al'amarin nan, amma komai ya zo ƙarshe in sha Allahu, zan kawo Mama da kaina har gidan ta ƙara yi mata faɗa, ba na son Kawu ya ji zancen nan, don kansa duk son da yake yi mata sai ya kusa balla ta." Ya ce. "Tom shikenan Naja, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, amma da na so na bar ta, ta je gida ta huta, idan ta gaji da zaman gidan ne." Naja ta ce. "A'a fa, da yardar mai duka komai ya zo ƙarshe, kuma kai ma da ka sani ka ƙwace wayar tata ka karya sim ɗin da ka fuskanci inda matsalar take. Da may be abun bai yi tsamari haka ba."  Ya ce. "To ai ba ta bari mun yi magana ma ta fahimta ba bare na gane inda matsalar take, sai dai kawai ɗan abun da na fahimta daga maganganunta na baya da gugar zanan da ta dinga mun, da zuwan wata ƙawarta gidan." Cikin takaici Naja ta ce. "Allah ya kyauta ya ƙara ganar da ita, Da iliminta amma na rasa inda ta ajiye shi ta ɗauki kishiyarsa." Ya ce. "Ni ma mamakin da nake yi kenan, don ban taɓa zaton za ta iya ambaton sunan mahaifana ƙarara ta haɗa kuma da cin mutunci ba."
"Ka yi haƙuri, na san ta yi hauka da wauta, kuma ta ɓata maka rai matuƙa, amma ka taimaka ka mayar da ita, ba na son na ga kun rabu wallahi, ba na son ta yi asarar miji irinka."
Runtse idonsa ya yi don har lokacin muryar Hafsah ba ta daina yi masa kuwwa a kunne ba, a sanyaye ya ce. "Shikenan na mayar da ita, Allah ya sa ta yi nadamar abubuwan da ta aikata har cikin zuciyarta." Ajiyar zuciya Naja ta sauke ta ce. "Amin ya rabb, na gode sosai da ka fahimci ni da kuma wannan alfarmar da ka mun, Ubangiji ya ƙara muku zaman lafiya da kwanciyar hankali, Allah ya kaɗe fitina a tsakaninku da sharrin shaiɗan, ya sa makamancin hakan ba za ta kuma faruwa ba." Ya ce. "Amin ya hayyu ya ƙayyum, ke ma Allah ya ba ki miji na gari." Murmushi ta yi ta yi masa sallama ta katse wayar. Shiru ya yi yana tunanin rayuwarsu ta da shi da Hafsah, ya so rabuwa da ita na har abada ko don ya nuna mata daraja da ƙimar da iyayensa suke da shi a wajensa, amma darajar su Sultan da kyautatawar da ta yi masa a da su saka sanya ya amince ya mayar da ita. Amma ba zai koma gidan ba a yau, su Sultan ma ba zai mayar da su ba, don da ma da ya ɗauko su ɗazu daga tahfiz gidan wani abokinsa ya kai su, ya ce musu Hafsan ta je unguwa ne. Ya san Naja za ta kira ta, ta faɗa mata duk yadda suka yi, zai gani idan za ta neme shi, inda da gaske ta yi nadamar abubuwan da ta yi masan.

Bayan Magriba na ce wa Maman Nasmah zan koma gida, don na san zuwa yanzu Naja sun yi magana da Anas kamar yadda ta alƙawarta, kuma na san ba zai ƙi mayar da ni ba, duk da ba ni da tabbas, don ban taɓa yi masa irin ko da makamancin irin wannan laifin ba na taɓa mahaifansa. Ga shi wayata ta ɗauke ta ƙi kunnuwa gabaɗaya, bare na kira ta ko ita ta kira ni. Hana ni tafiya Maman Nasmah ta yi, ta dinga yi mini faɗa kamar za ta ari baki, wai shi bai neme ni ba, bai mayar da ni ba amma zan komar da kaina saboda zubar da aji da rashin sanin ciwon kai, ta takura sai na kwana a gidanta, gobe inda an gama komai sai na tafi. Don dole ba don son raina ba na amince. A daren muka je saloon aka yi mana wankin kai da na ƙafa, aka kuma kawo mini kayana da sabuwar waya kamar yadda ta faɗa, har da kuɗin liƙi sabbin ƴan ɗari biyar-biyar. Farinciki, murna da ɗoki suka saka na manta da Anas da babinsa, na ci gaba da shirin taronmu da za mu cashe mu raƙashe a gobe.
Kallon Hafsah kawai Maman Nasmah take tana yi mata murmushin mugunta a zuciyarta, saboda ita kaɗai ta san me ta shirya mata a wannan kwanan da za ta yi a gidanta.......✍️

*Zeey Kumurya*✍️
[3/8, 1:40 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

*14.*
Chapter 26 · 0% Book details