← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 54

Sashe 33

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau ta kama Laraba, wanda ya yi daidai da watanni uku da fara takun saƙar mu da Anas. Ina zaune a ɗaki da hantsi ina chatting tare da kallon su Sultan da suke ball a tsakar gida, da yake ana cikin hutu ne babu school. Ƙara kishingiɗewa na yi cikin jin daɗin hirar da muke yi a group ɗinmu. Don yanzu ban da matsalar data, Maman Nasmah tana saka mini ishashshiya tare da kati, chaji ma ban da matsalar shi saboda ta aiko mini da sabuwar power bank. Wani video Aunty Billy ta turo, da sauri na yi loading na buɗe, don yanzu duk wani motsinta akan idona yake. Wani haɗaɗɗen gida ne da ya gaji da tsaruwa gurin gini da kayan alatun da suka ƙara ƙawata shi. Gidan mai hawa uku ne, bedrooms da parlourn cikinsa kuwa kasa ƙirga su na yi, kuma kowanne da kaya a cikinsa. Na maimaita kalla ya yi sau biyar sannan na haƙura ba don na gaji da kalla ba. Abin da na ga ta rubuta ne ya saka ni tashi zaune a zabure ba tare da na shirya ba. Sake watching video ɗin na yi cikin zazzaro ido kamar zan saka su a cikin wayar. Ina nuna gidan da ɗan'yatsana na ce. "Kan uba! Da gaske ko da wasa?" Ban kai ga samun amsa ba kiran Maman Nasmah ya shigo, cikin rawar jiki na ɗaga. Ba tare da mun gaisa ba ta ce. "Kin ga abin da Aunty Billy ta turo?" Da rawar murya na ce. "Gidan da ta turo ta ce za su koma a Abuja ita da mijinta?" Ta ce. "Eh, kin ga abin da nake faɗa miki ko? Kina nan zaune sai ta gama tatike shi, wannan uban gidan ko ni mijina ba shi da kamar shi, ki yi ki yi ki bar gidan talakan nan amma abu ya gagara, na tabbata da tuni yanzu ke za ki shiga gidan, don yana ta damu na akan maganarki, ko ɗazu da safe ma ya kira ni, kuma ya ce da an yi auren naku Abujan zai kai ki." Wani yawu na haɗiye mai ɗaci cikin takaici na ce. "To ya zan yi? Anas ya ƙi saki na, na yi masa tijarar, na yi bala'in amma ya ƙi, ba fa na yin komai a gidan shi yake yi, sai ya kai shabiyun dare bai yi bacci ba yana ta kujiba-kujiba da aikin gida." Maman Nasmah ta ce. "Taɓ! Amma wannan mijin naki wanne Iri ne shi? Kamar ba zuciya a ƙirjinsa?" Na ce. "Bala'in haƙuri ne da shi, kuma idan bai ga damar yin abu ba babu wanda ya isa ya saka shi, kuma yana so na sosai, da ma na san da wahala ya iya rabuwa da ni." A zafafe ta ce. "Ba wani so, da yana son ki ai da ya yi miki duk abin da kike so, kawai dai ya san idan kuka rabu ba zai samu wadda zai dinga cuta ya dunkume a gida kamar ki ba ne, shi ya sa. Ni dai abin da na kira na faɗa miki ki yi sauri ki dage ku rabu a cikin satin nan, ki san duk yadda za ki yi ku rabu a wuce gurin. Saboda na gaji da yi wa Alhaji Kyauta ƙarya, kullum ta yau daban ta gobe daban, don ya ce mini shi aure yake da buƙata cikin gaggawa, idan abin nan ba zai yiyu ba ya haƙura kawai ya nemi wata." Da sauri na ce. "A'a, ba ni iya yau zuwa gobe kacal, na san me zan yi." Ta ce. "Ya fi miki dai." Bayan mun gama wayar na ci gaba da kallon gidan ina hasaso kaina a ciki, da tuni ni ce zan wataya a cikinsa amma Anas ya yi mini buƙulu, ƙwafa na yi ina ayyana abin da zan yi masa yau idan ya dawo, wanda na san duk nacin shi dole ya rabu da ni. Ina nan zaune na ji an buga gida, Sultan ya je ya buɗe suka dawo tare da mai bugun, Naja ce, kuma da alama daga gurin aiki take, don sanye take cikin fararen kaya na nurses. Ba yabo ba fallasa na amsa mata sallamar da ta yi. Bayan ta shigo ta yi wa kanta mazauni ta ce. "Hajiya Hafsah, ana ta sana'ar ne? Don na ga yanzu U are always online, ko garin ma ba kya ji." Fari na yi da ido tare da faɗin. "Na kusa zama Hajiyar dai in sha Allah." Ta ce. "To Ubangiji ya tabbatar ya nuna mana lokacin, da fatan kin gama fushin da kike yi da ni?" Yamutsa fuska na yi na ce. "Fushi kuma? Akan me?" Ta ce. "Eh mana, tun daga ranar da na zo ɗin nan shikenan ba kira, ba magana a chat bare ki zo gida kuma." Taɓe fuska na yi na ce. "Au babu komai to, Allah ne kawai bai nufa ba." Ba ta ba ni amsa ba sai wayar hannuna da na ɗaga ta ƙura wa ido, kamar wadda ta ga abin tsoro haka ta nuna wayar ta ce. "Hafsah! A ina kika samu wannan Iphone 14 ɗin?" Jujjuya wayar na yi na ce. "Tsohon zance, tun yaushe na yi ta, wata ƙawata ce da take auren hamshaƙin mai kuɗi ce ta siya mini, ta ce idan mijinta ya dawo ma za ta saka ya siya mini 15." Kamar Naja za ta yi kuka ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Hafsah kina da hankali kuwa? Da kika karɓi wannan wayar mai tsada kin tabbatar saboda Allah ba da wata manufar ta baki ba? Kin ma ce wanda ta ba ki da farko an sace, ganin kayan kika yi ko kuma wasu ta ƙara siya miki?" A gadarance na ce. "Wasu ta sake siya." Shiru ta yi na wasu sakanni sannan ta ce. "Anya ba da wata manufar ta yi miki wannan kyautar ba? Hafsah ki dinga tunani da ƙwaƙwalwarki fa, kar son duniya da ruɗun shaiɗan su kai ki su baro." Tsaki na ja na ce. "Babu wata manufa sai ta alkhairi, kuɗi ne kawai da su, wannan ai ba wani abu ba ne a gurinsu." Ban jira cewar ta ba na buɗe wayata na koma kusa da ita na fara nunnuna mata abubuwan da suke turowa a group ɗin, tare da ba ta labarin gidajen waɗanda na je na gano. Tana kallon gidan da Aunty Billy ta turo ta ce. "Don Allah na tambaye ki mana?" Na ce. "Ina jin ki?" "Wa ya saka ki a group ɗin nan? Yaya aka yi kika tsinci kanki a cikinsa?" Murmushi na yi na ce. "Ke ma ya burge ki ko? Ai group ɗin nan yana da shiga rai, duk wanda ya zauna a cikinsa ba ya iya fita, ga shi mutanen ciki duk ƴan gayu ne masu haɗin ka..." A ƙufule ta katse ni da faɗin. "Ni ba wannan na tambaye ki ba, yadda aka yi kika kasance a group ɗin nake son ji." Tashi na yi na koma inda nake da farko sannan na ce. "Wata ƙawata ce da muka yi islamiyya tare, ta turo link ɗin a group ɗinmu na ƴan'ajinmu, a nan na gani na shiga." Naja ta ce. "To ita ƙawar taki har yanzu tana cikin group ɗin?" Na ce. "A'a, kamar a ranar da na shiga ma ta fita, da muka haɗu kwanaki ta ce mini wayarta ce ta lalace, duk wanda muka shiga tare ma sun fice, sun ce ba za su iya da uban suturun da ake yi a group ɗin ba." "Sai ke da rabon wahala yake jan ki shi ya sa kika zauna ko?" Ta faɗa cikin faɗa da ɗaga murya. A fusace na ce. "Ke Naja! Haifa ta kika yi ne da za ki dinga yi mini magana cikin faɗa da tsawa? Na gaji da abubuwan da kike mini, ki ƙyale ni, babu ruwanki da rayuwata, ki fita daga sabgata, ki tsaya iya matsayinki." Jinjina kai ta yi ta ce. "Na ji, amma ko da wannan ne karo na ƙarshe da zan faɗa miki gaskiya sai na faɗa miki." "To ba na so." Na faɗa cikin ƙaraji. Miƙewa ta yi tare da cillo mini wayata, a sanyaye ta ce. "Idan har kina cikin group ɗin nan ba za ki taɓa ganin duk wata gwanintar da Anas zai yi miki ba, saboda abubuwan da suke turowa na mahaukatan kudi, wanda duk da ban sani ba, rabi da ƙwata duk ƙarya ne. Amma irinki masu ƙaramar ƙwaƙwalwa ba za su gane hakan ba. Ko za ki ƙi ji, ko za ki ƙi amfani da shawarata ba zan fasa faɗa miki gaskiya ba. Anas namiji ne ɗaya tamkar da dubu, idan kika yi gangancin rabuwa da shi za ki yi danasani mara amfani, a lokacin da time ya ƙure miki." Tsaki na ja na ce. "To ko Anas ɗin za ki aura ne Naja? Tunda na ga kullum cikin yabon shi kike." Murmushi ta yi mai ciwo ta ce. "Tabbas da zan samu miji mai nagarta kamar Anas babu abin da zai hana ni auren shi, ko da kuwa ni zan dinga cikon kuɗin cefane, in dai ba shi da hali ne ba mugunta ba ce. Amma Anas babu aure a tsakanina da shi har abada, saboda kin riga da kin yi mana katangar ƙarfe da hakan. Ki saka a ranki har abada ni Naja ko da kin mutu ba zan taɓa auren mijinki ba. Gaskiya ce kawai nake faɗa miki." Taɓe baki na yi na ce. "Ba wani nan, kawai don dai talaka ne shi ya sa ba za ki aure shi ba, amma da mai kuɗi ne sanda za ki auren shi ma wa ya sani?" Cikin takaici ta ce. "Ke ce kuɗi yake gabanki, abin da ba ki sani ba ma ni zuwa na yi na faɗa miki an kawo kuɗina tun last month, an saka biki nan da 3 months." A sheƙe na ce. "Allah ya sanya alkhairi." Ta ce. "Amin na gode, duk da a wulaƙance kika amsa, saboda ina ɗora ki a turbar gaskiya, ki je ki ci gaba, ai ta ɗora ki a kan keken ɓera, KANKI ZA KI YI WA ba wani ba, don ba zan fasa maimaita miki ba ki da wani
Chapter 33 · 0% Book details