← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 54

Sashe 22

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tamkar saukar aradu da ka haka na ji furucin nasa a tsakiyar kaina, wani irin abu mai zafi da zugi ya baƙunci zuciyata. Lokaci ɗaya na nemi zafin marin da ya mini na rasa, saboda wanda nake ji a cikin zuciyata sakamakon sakin da ya mun ya ninninka shi. Da ma haka sakin yake? Haka mata suke ji idan aka yi musu shi ko da su suka nema? Ji na yi duniyar tana juya mini, na daina fahimtar komai na wucen gadi. Sama-sama na ji muryar Naja ƙawata da ban san lokacin da ta shigo gidan ba tana rafka salati, tare da ƙarasowa ta kama ni a inda na ƙame kamar mutummutumi ta shigar da ni parlour ta zaunar a kan kujera. Ko da wasa ban taɓa tunanin ko me zan yi wa Anas zai iya saki na ba, na ɗauka ko da zan dinga yankar naman jikinsa ina gasawa saboda azabtarwa ba zai iya rabuwa da ni ba, saboda matsananciyar soyayyar da na san yana mini. Numfarfashi kawai nake yi. Naja da ke riƙe ni har lokacin tana sallallami ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Hafsah me ya faru? Me ya haɗa ku da Abban Sultan? Don Allah ki ce abin da suka ziyarci kunnena lokacin da na shigo gidan nan ƙarya ne, kunnen nawa ne bai ji mini daidai ba." Girgiza kaina na yi ina hawaye na ce. "Daidai ki ji Naja'atu, kuma ni na buƙaci hakan da kaina." Ja baya ta yi a ruɗe ta ce. "Subhanallahi! Me ya yi zafi har haka ke kuwa? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Da na san abin da zan tarar kenan da wallahi ba zan zo ba." Gimtse baki na yi tare da share hawayena na ƙwace daga riƙon da ta yi mini na dafe kaina tare da lumshe idona. A hankali a hankali na ji zafin sakin yana raguwa daga cikin raina, ina kallon Naja da ta ishe ni da tambayar sanin ba'asi na ce. "Me ya sa kika damu ne haka? Mene a ciki don na rabu da Anas?" Kallon mara hankali ta mun ta ce. "Ba don na gan ki fes kin ƙara fresh da kyau ba da sai na ce kina cikin mayen hauka ne, na zo na tarar da ku cikin tashin hankali ke da mijinki har ya sake ki sannan kuma ki ce me ya sa zan damu?" Murmushi na yi don a yanzu ba ta Anas da sakin ya yi mini nake ba, duk da ina jin ɗacin abun matuƙa a cikin raina, taron da za mu yi gobe da abin da zan saka shi ne kawai danuwata. "Me ya sa idan na kikkira ki ba kya ɗagawa? Idan na yi miki magana a Whatsapp ba kya dubawa bare ki mun reply?" Hararar ta na yi na ce. "Saboda kin gama kunce mini zani a kasuwa mana, na yi ƙarya da ke amma kika ce wa Anas ba ki san zancen ba." Gyara zama ta yi ta ce. "Shi ne dalilin da ya sa nake ta kiran naki ai, na ji dalilin da ya sa kika aikata hakan." Baki na taɓe na ce. "Ya riga ya wuce ai." Na ƙarashe maganar ina miƙewa don fara haɗa kayana na bar wa Anas akurkin gidansa. Naja da har lokacin na lura a cikin ruɗu take ta kamo hannuna kamar za ta yi kuka ta ce. "Hafsah kin bar ni a cikin duhu fa, don girman Allah ki faɗa mini abin da yake faruwa, na ga kin ware kamar ba wadda take cikin zullumi ba." Komawa na yi na zauna don na labarta mata duk abin da yake faruwa, saboda Naja ta wuce ƙawa ko aminiya a gurina, ta zamo ƴar'uwa da ba zan iya ɓoye mata komai nawa ba. Cikin takaici na ce. "Naja Anas ba so na yake yi ba kamar yadda yake pretending, na yi da na sanin auren shi." A zabure ta ce. "Kamar ya? Ban gane ba?" Tsaki na ja na ce. "Matan da mazajensu suke son su, suke yi musu duk abin da suke so a lokacin da suke so bayan wadata su da suka yi da komai na more rayuwa suna can daban, amma ni ko kusa ba na cikinsu, ba na cikin mata masu sa'a da ake kwatance da su, ake sha'awar su, ake burin samun mazaje irin nasu." Na ƙarashe maganar kamar zan fashe da kuka. Galala ta yi tana kallo na ba ta ce komai ba. Numfashi na sauke na ce. "Ba ki gane me nake nufi ba ko? Yanzu zan ganar da ke." Ban jira amsarta ba na kwashe labarin komai na faɗa mata. A matuƙar gigice na ga ta miƙewa kamar wadda na faɗawa ranar mutuwarta, tana nuna ni da hannu ta ce. "A'uzubillah! Hafsah da ma ba ki da hankali? Ashe mahaukaciya ce ke ban sani ba?" Haɗe rai na yi na ce. "Haukan uban me na yi?" A fusace ta ce. "Ban sani ba, wallahi ba don na kai zuciyata nesa ba da sai na kikkifa miki mari, kamar na rufe ki da duka haka nake ji, I'm speechless! Na rasa me zan ce miki, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Ta ƙarashe maganar tare da dafe kanta. Tsaki na ja ban ce komai ba. Komawa ta yi ta zauna tana bi na da wani irin kallo, idanunta cike da hawaye ta fara magana da faɗin. "Ko a mafarki aka ce mini za ki aikata wannan tafkeken haukan da jahilcin ba zan taɓa yarda ba, yaushe kika haukace Hafsah? Yaushe kika daina amfani da ƙwaƙwalwarki wajen yin al'amuranki? Ina iliminki na addininki yake? Kin watsar saboda son duniya da hangen dala ko?" Shiru na yi ban ce komai ba. Kamar za ta rufe ni da duka ta ce. "Kin ba ni matuƙar mamaki da kunya, akan wani banzan group kika bari salihin miji irin Anas ya yi miki har saki biyu? Saura igiya ɗaya fa a tsakaninku yanzu? Saboda wasu tsinannu Hafsah!" Ta ƙarashe maganar cikin ƙaraji. Kallon banza na yi mata na ce. "Saboda sun haska mini abin da ban sani ba na rayuwa shi ne suka zama tsinannu? Ki yi mini duk zagin da za ki mini amma ban da su, don ni sun gama yi mini komai a rayuwa." "Sun gama kam, tunda sun cuce ki sun kashe miki aure, su kuma suna can zaune lafiya ƙalau da mazajensu." Naja ta faɗa tana jifa na da wani mugun kallo. Cikin tsagalgala na ce. "Ai su mazajensu ba talakawa ba ne, kuma da ma irin gidajensu ai ba a fatan a fita." Ta ce. "Haka ne, duk da na ga alamar kin yi nisa amma ba zan ƙi faɗa miki gaskiya ba, da tunatar da ke abin da gidahumar ƙwaƙwalwarki ta mantar da ke ba. Hafsah tun kina ƴar ƙarama a zanin goyo mahaifinki ya rasu, mahaifiyarki kuma bayan kin ɗan girma ba ki fi shekara uku ba ita ma ta bi bayan shi, daga lokacin aka dawo da ke gurin Kawu ya riƙe ki. Kawu ya yi miki riƙo na tsakani da Allah tamkar ƴar da ya haifa a cikinsa, kuma ya nuna miki soyayya saboda bai taɓa haihuwa ba, sanadiyyar hakan Gwaggo matarsa ta tsane ki, ta gana miki azaba. Ba sai na tuna miki irin uƙubar da kika sha a gurinta ba, saboda kin fi kowa sani. Yanzu idan kika bar nan kika koma gida a matsayin bazawara ya kike tunanin zamanku zai kaya ke da Gwaggo? Kina budurwa ma ba ta so ki ba balle a yanzu? Ko kin mata da wannan? Kuma idan ba gidan ba, ba ki da gurin zuwa, tunda dangin mahaifiyarki suna can Lafiya, tsakaninki da su waya ce ko chat, ba ki taɓa zuwa ba, su ma ban da lokacin bikinki ba su taɓa zuwa kun haɗu ba, can kike tunanin za ki je ki yi zawarcin a haka? Ba su saba da ke ba, ba ki taɓa zuwar musu ba, kawai sai su gan ki rana tsaka ki ce musu aurenki ne ya mutu kika koma? Ki yi aiki da hankalinki ki yi tunanin abin da zai fishshe ki, takamaiman gurin da za ki je ki zauna ma ki ji daɗi ba ki da shi idan kin bar nan ɗin, amma a haka kika kashe aurenki?" Shiru na yi don maganganunta sun fara ratsa ni, amma duk da haka ba su saka na ji zan saduda ba. Ganin haka ta ci gaba da magana da faɗin. "Abu na biyu kuma, samun mijin da yake son ka tsakani da Allah ma kamar yadda Anas yake son ki a wannan zamanin wahala yake, ya so ki tun kina ƴar ficiciyarki, ba ki san kanki ba, bare ki yi kwalliya da za a ce ita ta ja hankalinsa gare ki, kuma a lokacin ko alamar zama budurwa ba ki fara ba, bare ya ce ya ga kyanki ko jikinki ya so ki don su, hasalima a cikin rayuwar wahala da ƙuncin rayuwa ya gan ki, ya fara da jin tausayinki daga nan ya rikiɗe ya koma soyayya. Babu gatanta kin da bai yi ba tun kina gida har zuwa aurenku daidai ƙarfin ikonsa. Soyayya, kulawa, darajawa, babu wanda bai nuna miki ba. Ya taya ki aikin gida, ya kai ki unguwa da kansa, ya ɗauke miki dukkan wata ɗawainiyarki, da kika haifi ƴaƴa bai canza miki ba kamar yadda wasu mazan suke yi, ya rungume ku ke da yaranki kuka ci gaba da rayuwa cikin farinciki da annushuwa. Anas bai taɓa ragar ki da komai ba, to me kike nema a gurin miji da ya fi wannan? Me kike da buƙata? Ke ba matsalar kishiya, ba ta uwar miji, ba ta ƙannensa ko yayye ba, miji ba ya dukanki, ba ya cin mutuncinki bare zagi. Amma saboda hauka ki dinga hangen na wasu can da ba ki san irin taskun rayuwar da suke ciki ba, wallahi Maman Sultan daɗi ne ya yi miki yawa, da kuma kin samu Anas ɗin mai haƙuri. Da ma an ce samu mai saka hauka." Baki na zunɓura na ce. "Hmm, duk waɗannan bayanan naki kin san dai na fi ki sanin da su ko?" Ta ce. "Eh, amma ba kya duba su ai." Na ce. "Eh, saboda ni yanzu ba su ne a
Chapter 22 · 0% Book details