Sashe 28
Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
a cikin my driver's ya kai ki É—aya daga cikin guest house É—inmu, ki zauna a can a matsayin nan ne gidanki, sai su zo nan su same ki, idan za ku tafi zan haÉ—a miki da wadataccen abincin da zai isa a ci da drinks. Zan ba su address É—in yanzu idan sun tambaye ni ina ne gidanki. Bana son su je ainihin gidanki su raina ki ne, shi ya sa na yi wannan dabarar." Ban san lokacin da na rungume ta ba tsabar farinciki na ce. "Ya Allah! Na rasa da bakin ma da zan gode miki wallahi, duk abin da za ki yi ki kankaro mini mutunci kin san shi." Tana murmushi bayan ta raba ni da jikinta ta ce. "Ƙauna ce ta kawo hakan, ke dai duk abin da na ce ki yi kawai ki bi, don ba zan taÉ“a cutar da ke ba." Cikin zumuÉ—i na ce. "Na tabbatar da hakan takwara, Allah ya bar mu tare." Ta ce. "Amin." Kayan ciye-ciye da abinci da lemuka Aunty Billy ta haÉ—o ta ba ni, na yi musu sallama na tafi cikin sauri, don na ga Naja ta fara doka mini kira. Allah ya taimake ni ina fita titi na samu mai napep, ya ce zai kai ni har gida a 2k. Ban tsaya ja'inja ba na shiga, saboda ina da ishashshen kuÉ—i a hannuna ragowar na liÆ™in da Maman Nasmah ta ba ni. Mun fara tafiya mai napep É—in ya ce. "Hajiya ga wata mota tana bin mu a baya, ko kin san su ne?" Girgiza kai na yi na ce. "A'a." Ya ce. "To dai wannan mu take bi, amma bari na shiga ta layuka don na tabbatar, idan mu yake bi zai shigo shi ma." Na ce. "To." Don ni hankalina gabaÉ—aya ya yi gida, burina kawai na gan ni a cikinsa, don ba na son maganar abin da yake faruwa ta je kunnen Kawu, na san na lahira sai ya fi ni jin daÉ—i a gurinsa. Da gudu motar da take bin bayanmu ta zo ta wuce mu ta tsaya a gabanmu. Cikin faÉ—uwar gaba na ce. "Innalillahi! Su waye wannan? Me suke nema a gurinmu?" "Sai Allah." Mai napep ya faÉ—a a tsorace bayan ya tsayar da babur É—in. Fita ya yi ya je suka yi magana, ina ta leÆ™en su a tsorace na ga ya dawo ya ce. "Hajiya ke suka biyo, da ma daga layin da kika fito na ga su ma sun fito." Dafe Æ™irji na yi a firgice na ce. "Na shiga uku! Me zan yi musu to?" Yana murmushi ya ce. "Ki je ki ji, amma na tabbatar ba cutar da ke za su yi ba." A tsorace na kalle shi na ce. "Ko dai bakinku É—aya da su?" Ya ce. "Wallahi ban ma taÉ“a ganin su ba sai yau, ki daure ki je, sun ce ba jimawa za ki yi ba." Girgiza kai na hau yi na ce. "Ka shigo ka ja mu kawai mu tafi, ni sauri nake babu inda zan je." "Ko mun juya sai sun kuma bin mu, ki je kawai ki ji me za su ce ki dawo, don Allah!" Ya yi maganar cikin roÆ™o. Ina kallon layin da babu kowa sai mu kaÉ—ai na ce. "Wai maza ne ma ko mata?" Ya ce. "Mata ne." Ajiyar zuciya na sauke na fita ina waige-waige a tsorace, sai a lokacin na lura da sababbin kuÉ—in da suke hannunsa, tabbacin cin hanci suka ba shi, shi ya sa ya dage sai na je. Kamar kar na Æ™arasa, saboda haka kawai na ji zuciyata tana bugawa. Tsayawa na yi cak a gaba da napep É—in amma ban Æ™arasa inda motar take ba. A hankali na ga an buÉ—e front seat an fito, damm! Ƙirjina ya buga da Æ™arfi bayan na yi tozali da mai fitowar........âœï¸