Sashe 27
Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har sha biyu na dare ta wuce ban yi bacci ba, ina zaune a tsakiyar makeken gadon da nake na tasa kayana a gaba ina aikin kallon su, sai jujjuya dalleliyar wayar nake a hannuna ina sakin murmushi. "Allah ka cika mini burina, ka nuna mini ranar da ni ma zan yi kyauta ga wani ninkin ba ninkin ɗin wannan." Na yi maganar ina bin bedroom ɗin da ya kusa rabin gidana gabaɗaya a girma da kallo. Gado, wardrobe, mudubi duk suna gefe ko rabin ɗakin ba su ci ba. Ƙuntataccen ɗakina na tuna, wanda space ɗinsa da ya rage bai fi ya ci ƙaramar tabarma biyu ba. Tsaki na ja na tattara kayan ba don na gaji da ganin su ba na kwanta. Sai na ji kuma na kasa baccin, duk da juyin da nake yi a gadon ina bararrajewa son raina. Tashi na yi na rage hasken ko shi ya hana baccin ɗauka ta. Amma still ya ƙi zuwa, tunanin Anas da su Sultan na ji ya cika zuciyata, wata irin kewar su da ban taɓa zaton yin ta ba ta ziyarce ni. Duk yadda na so na yakice su amma abu ya ci tura. Taune leɓena na yi ina ayyana da dare bai yi sosai ba sai na koma gidana a yau, don na gane ba zan taɓa iya rayuwa babu mijina da ƴaƴana ba, ko kuɗin da nake so da shi nake son mu yi ba wai mu rabu ma, amma shi ya ƙi gane hakan bare ya ba ni haɗin kai. Da ƙyar na samu bacci ya ɗauke ni lokacin da dare ya kusa rabawa. Washegari bayan na yi sallar asuba na koma bacci, sai bayan 10 na tashi muka fara shirin tafiya taronmu. Mai kwalliya ta musamman ce ta zo ta yi mana har gida ni da Maman Nasmah. Zuwa bayan azhar mun gama shiryawa cikin ankonmu. Na daɗe ina kallon kaina a mudubi saboda ba ƙaramin kyau na yi ba ni kaina na sani. Maman Nasmah ta dinga yi mini hoto a wayarta, don tawa har yanzu ba a kunna ta ba, ni ban iya using iphone ba ita kuma ta ce sai mun nutsu za ta saita mini komai. A wata luntsumemiyar mota mai numfashi muka tafi gidan Aunty Billy, muna baya driver yana gaba shi kaɗai. Sosai harabar gidan da aka yi wa decoration ya yi kyau, mun tarar da sama da mutum 20 a gidan sun zo. Da gudu wasu suka taho suka rungume Maman Nasmah, ta nuna musu ni, suka ce ko da ba ta faɗa ba sun san ni ce, saboda sun san duk inda suka gan ta za su gan ni a gurin, tunda kowa ya san ita ce babbar ƙawata a group ɗin. Zagewa na yi aka shiga hada-hada da ni, ina jin kaina kamar kowa tunda na saka gold da sauran kayan kwalliya masu tsada. Sama da mutane 60 ne suka halarci taron, kuma duk ƴan group ɗin namu ne, kowacce kuma ta saka anko, ta yi ɗinki mai tsada da sarƙar gold ɗin da aka ce. Sosai muka yi kyau kamar yadda muke fata. An ci an sha, an yi rawa an cashe an tattauna, abin gwanin ban burgewa. Hakan sai ya ƙara mini son group ɗin sosai, na ji ko me za a yi ba zan fita daga cikinsa ba. Mun sha hotuna da video kamar ba gobe. Sai da aka kusa tashi Maman Nasmah ta saka mini sim ɗina a cikin sabuwar wayar, ta nuna mini yadda zan yi kira da wasu ƴan abubuwan, sauran kuma ta ce sai mun koma gida za ta nuna mini. Kaf matan da suka zo taron babu wadda ta kai ni duhu, saboda kowacce sai na gan ta fara ƙal, waɗanda ba fararen sosai ba kuma duk sun fi ni haske, duk da gyaran jikin da aka mun, alaƙanta hakan na yi da don su matan masu kuɗi ne ni kuma matar talaka ce. Messages na gani da numbern Naja, na farko ta ce tana ta kira na a kashe, na biyu kuma ta ce ina ina? Ta zo gidan ba na nan, alamun tun jiya ta yi su kenan. Sai yau da ta ƙara cewa ta je da safe ba na nan, sai na ƙarshe kuma wanda da alama ba ta daɗe da yin shi ba, ta ce duk inda nake na koma gidana don Anas ya mayar da ni tun jiya, idan ba haka ba za ta je ta faɗa wa Kawu duk abin da yake faruwa. A tsorace na bar filin rawar da muke na ja Maman Nasmah gefe na ce. "Ni fa tafiya gida zan yi yanzu, na ga Magriba ta kusa." Kallon sama da ƙasa ta yi mini ta ce. "Saboda me? Ya kira ni ne? Ba gidana za ki koma ba da ma?" Girgiza kaina na yi cikin fargaba na ce. "Bai kira ni ba, amma ƙawata ta yi mini text ta ce ya mayar da ni." Tsaki ta ja ta ce. "Ita ƙawar taki ya aka yi ta sani?" In brief na ba ta labarin tattaunawar da muka yi da Naja. Tafa hannuwa ta yi ta ce. "Shi ne kike wannan rawar jikin komawar? Bai kira ki da kansa ba tun jiya amma daga an yi miki text an ce ya mayar da ke duk kika gigice haka? Hafsah wai wacce iriya ce ke ne? Akan namiji? Namjin ma talaka." Kamar zan yi kuka na ce. "Ba haka ba ne, ina tsoron ƙawar tawa ta faɗa wa Babana ne." Taɓe baki ta yi ta ce. "To bari ki ji, ita ƙawar taki ita ce babbar munafuka kuma maƙiyiyarki, saboda ba ta son ki da arziƙi, da tana son ki da arziƙi ba za ta ce ki rabu da mu ba, bayan kin faɗa mata yadda muke da irin kyautar da na yi miki, amma saboda tana baƙincikin ki yi mu'almala da masu kuɗin da ita ba ta yi shi ya sa ta ba ki wannan gurguwar shawarar, za ta ce kar ki fara gayu ki bar ta a baya." Girgiza kai na yi na ce. "Naja ƙawata ce ta haƙiƙa tun muna yara, tana so na da son ci gabana sosai, ba za ta taɓa yi mini abu don hassada ba gaskiya, kawai dai tana faɗa mini tata fahimtar ne." A sheƙe kamar kashi ta saki baki tana kallo na, kafin ta jijjiga kai ta ce. "Taɓɗijan! Amma gaskiya ba ki san halin da duniya take ciki ba, to ki je ki tambaya ki ce kaf yanzu a rayuwa wa ya fi rashin amana da nuna hassada, za a faɗa miki a ce aminiya ce. Tun yaushe aka daina ƙawancen tsakani da Allah, kowa zuciya da tsatsa burinsa ya ga ya fi ɗan'uwansa ci gaba. Idan kuma kina tantama akan maganata ki je ki ce mata ta auri miji talaka kamar naki, za ki ji abin da za ta ce, wanda zai nuna ba ta so, amma ke tana danƙwarar da ke akan ki zauna." Jinjina kai na yi, zan yi magana Aunty Billy da ta ƙaraso inda nake ta riga ni da faɗin. "Ku ce aminai kuna nan kuna zantawa?" Murmushi muka yi duk da nawa na yaƙe ne. Ta ce. "Ku zo mu je ku gaisa da Ogana, ya dawo yanzun nan, ya gaisa da kowa ban da ku." Maman Nasmah ta ce. "Shi ya sa na ga bakinki ya ƙi rufuwa, ashe rabin ran kika gani." Ta ce. "Bari ke dai, har ya ƙara mini da kuɗin liƙi." Faɗaɗa fara'a Maman Nasmah ta yi ta ce. "Ai na sani da ma, ni da na san dawar garin, duk dawowa da ma kin ce da kyauta yake yi miki sallama, kamar nawa mai gidan, shi ma yana dawowa zai ce ungo." Dariya suka kwashe da ita tare da tafawa suka yi gaba. Na bi su abaya kamar saniyar ware, a raina ina faɗin. 'Wato su mazajen nasu da kuɗi suke tarɓar su kullum? Gaskiya matan masu kuɗi suna shanawa da yawa, ga ƙaton gida, ga abinci lafiyayye, ga sutura mai tsada, ga hawa mota da sauran abubuwan more rayuwa." Wani part ɗin muka shiga daban ba inda ta kai mu da za mu yi Sallah ba, ba ƙaramin dauriya na yi ba gurin ɓoye ƙauyancina, saboda haɗuwa da tsaruwar shi. Na kasa gane tsakanin gidan Maman Nasmah da na Aunty Billy wanne ya fi kyau da girma, saboda kowanne ya kai duk inda ake son gida ya kai a tsaruwa. Cikin fara'a kamar ya san mu muka gaisa da mijin nata, ta ƙasan ido na ƙare masa kallo. Irin alhazawan nan ne da kuɗi da hutu suka zauna a jikinsu, ga shi ɗan dumurmuri ya sha babbar riga cikin kaya na alfarma. Irin dai mijin da mace ba za ta ji kunyar nuna shi ba ko a ina ne. Anas ne ya faɗo mini a rai, na ja tsaki ƙasa-ƙasa, tare da addu'ar kar Allah ya kawo ranar da wata a group ɗinmu za ta ƙara ganin shi a matsayin mijina bayan Maman Nasmah. Don abin kunya ne a gare ni. Bayan mun fito Maman Nasmah ta ce mini. "Wai tafiyar za ki yi da gaske na ga kina abu kamar a ce ƙyet! Ki gudu?" Ɗaga mata kai na yi ban ce komai ba. Aunty Billy ta ce. "Saboda me? Ki bari a tashi mana, ba wani ɗadewa za a kuma yi ba fa, ana yin Magriba DJ zai tafi." Kafin na yi magana Maman Nasmah ta yi karaf ta ce. "Mijinta ne ya kira ta yaron ta babu lafiya, shi ya sa." Ajiyar zuciya na sauke ina ƙara jin son ta a raina, saboda duk yadda za ta yi kar asirina ya tonu sai ta yi. Aunty Billy ta ce. "Ayya, Allah ya ba shi lafiya, bari na zo to ina zuwa." Bayan ta bar gurin Maman Nasmah ta ce. "Ki yi tafiyar ki kar ki yi wa kowa sallama tunda kin nace, saboda su Maman Suhail tun jiya suke ce mini ina ne gidanki za su je, yanzu idan suka ji za ki tafi bin ki za su yi. Gobe idan Allah ya kai mu da safe sai ki zo gidana, zan saka wani