Sashe 12
Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Ina durƙushe na kifa kaina a jikin gado ina runtumar kuka kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwar uwarta na ji ya shigo, ƙara volume na yi ba tare da ɗago ba balle ya saka ran zan saurare shi. Ina jin shi yana zauna a gefen gado kusa da kaina. Matsawa na yi tare da ƙoƙarin tashi na bar ɗakin na ji ya ruƙo ni, ƙoƙarin ƙwacewa na yi amma ya nuna mini shi namiji ne, ya riƙe ni gam ya mayar da ni na zauna a fusace. Cikin taushin murya ya ce. "Ki yi shiru don Allah Hafsah mu yi magana, mene ne haka? Wannan kukan na mene?" Tsaki na ja na ce. "Don Allah, don darajar iyayenka ka ƙyale ni Anas, ba na son magana a yanzu." Ya ce. "Na ji zan ƙyale ki, amma don Allah ki bar wannan kukan da kike yi mara amfani, ko dan su Sultan da suke jin ki." Na ce. "To." Kawai, tare da share hawayena, duk da na san dole wasu sai sun zuɓo. Ni kaɗai na san halin baƙinciki da takaicin da nake ciki, kamar nai ta zunduma ihu haka nake ji. Babban tashin hankalina ban san me zai biyo baya ba a gurin Maman Nasmah da yadda ta zo ta gan ni, ina tsoron ta faɗa wa wasu ƴan group ɗinmu.
Wunin yau gabaɗaya haka na yi shi sukuku, zuciyata a cunkushe da jin haushin Anas. Tun bayan da na dawo daga rakiyar Maman Nasmah na kashe wayata, har dare ban kunnata ba, duk da yadda zuciyata take ta azalzalata na kunna na ji me Maman Nasmah za ta ce mini, na ji matsayin da ta ajiye ni, na Salamatu mai aiki ko kuma Hafsah Maman Sultan. Tsabar abin duniya ya bi ya dame ni ko ruwa ban kai bakina ba. Hakan ya sa nake ji na wani iri kamar mai cuta, ƙirjina har zafi yake mini.
Maman Nasmah kuwa bayan ta koma gidanta ta ci gaba da saƙawa da warwarar hanyar da za ta bi ta mallaki Anas, a ƙarshe ta yanke wasu shawarwari, abu na farko da za ta fara yi shi ne ta raba shi da Hafsah, na biyu kuma za ta saka a yi mata binkice akan shi, sai ta fara da bin iyayensa da ƴan'uwansa ta yi musu alkhairi, bayan ta tabbatar ta karɓu a gurinsu sai ta bayyana masa manufarta, yadda ko da ya ƙi amincewa wani nasa zai yi masa dole ya amince, fatanta kawai ya kasance mahaifansa suna raye, don idan da su komai sai ya fi tafiyar mata daidai. Tun yamma take kiran wayar Hafsah a kashe, don ta fara aiwatar da aikinta a kanta, domin da zafi-zafi ake dukan ƙarfe, ba za ta tsaya kuma garin kallon ruwa kwaɗo ya yi mata ƙafa ba.
Ina kwance a kan dardumar da na yi sallar Magriba Anas ya dawo. Ban ko kalle shi ba, har ya yi wanka ya je masallaci sallar isha'i ya dawo. Da kansa ya zuba abinci ya ci, na dinga kallon shi ina jin kamar na je na samu fuskarsa nai ta mari, ya na cin taliya da manja da yaji amma kamar mai cin wani haɗaɗɗen abincin da ya ji nama, sai wani lumshe ido yake yana zurƙuma lauma. Ban san lokacin da na ja wani dogon tsaki ba. Bayan ya gama ya dube ni ya ce. "Wace ce ta zo ɗazu?" Kamar na share shi, amma yadda na ji ya yi magana babu alamun wasa ya sa a ƙufule na ce. "Sai yanzu za ka tambaya? Me ya sa tunda ka gan ta ba ka tambaye ta, ta ba ka amsa da kanta ba?"
"Saboda ke nake da hurumin tambaya, ke kika kawo ta gidana."
Tashi zaune na yi cikin tsiwa na ce. "Ina gidan yake? Har kake wani ƙafafa kana cewa gidanka?" Na ƙarashe maganar ina keɓe baki. Girgiza kai ya yi ya ce. "Ki ba ni amsa kawai, kar ki tunzura ni, na yi miki abin da ba ki taɓa zato ba."
'Ka yi mana' Na faɗa a cikin raina, amma a fili sai na ce. "Ƙawata ce." Ya ce. "Ya yi, amma ya aka yi ban san ta ba tunda muke da ke?" Na ce. "Allah ne bai yi ba." Daga haka na tashi na shige ɗaki.
Anas ya bi ta da kallo, har yanzu tantama yake akan anya Hafsah ita kaɗai ce kuwa? Saboda tun sanin da ya yi mata bai san ta da irin waɗannan halayen ba, ya san dai tana da fushi idan aka yi mata abu, amma bayan wannan bai san wani hali nata mara kyau ba. Kuma shi abin da yake ƙara ɗaure masa kai rashin sanin dalilin da ya sa take masa hakan, a iya sanin shi bai san ya yi mata wani laifin ba, bare ya ce ko shi ne dalili. A ɗazu bayan ya koma gurin aiki yay ta tunane-tunane, shi mutum ne da ba ya son zargi ko ƙala wa mutum abin da ba shi da tabbas a kan shi. Hakan ya sa ya ƙi alaƙanta abubuwan Hafsah da matar da ya gani ɗazu, duk da wani sashe na zuciyarsa yana ta faɗa masa wataƙila ya na da nasaba da hakan, ya dinga tambayar kansa wacce mata ce ita da har Hafsah take kunyar ta gan shi a matsayin mijinta. Numfashi ya sauke cikin rashin sanin abun yi, makamancin haka bai taɓa faruwa a tsakaninsu da Hafsah ba tunda suka yi aure, shi ya sa abin ya dame shi matuƙa, ya rasa tudun da zai dafa wanda zai taimaka masa ya gano hasken da zai fitar da shi daga duhun da yake ciki. Yana son matarsa so mai tsanani, ba ya son abin da zai shiga tsakaninsu ko yaya yake. A parlour'n ya goce ya kwanta, don so yake ya ga iya gudun ruwan Hafsah.