← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 54

Sashe 44

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Yau idan an kai azumi huɗu, da rana ina zaune a ɗakina ina karatun Alkur'ani da na manta rabon na yi, hawaye ne yana zuba a kan kuncina, wani irin abu mai ɗaci da maƙaƙi ne ya tsaya mini a ƙirji, ga kewar su Sultan da ta cika mini zuciya a kwanakin nan. Rufe kur'anin na yi na rushe da kuka. Wacce irin amarya ce ni mara daraja da har an yi sati guda amma ango bai zo ya gan ni ba? Na tambayi kaina cikin takaici. Abin da yake ƙara baƙanta mini rai kullum sai na tambayi gateman ya tabbatar mini da Mansur yana nan ƙalau cikin ƙoshin lafiya. Bayan na yi kukan mai isata na tashi na haye kan gado, saboda jin maganin baccin da na sha da asuba ya fara aiki, rashin bacci ya sa na ba da aka siyo mini da yawa, kullum idan aka sha ruwa sai na sha nake iya bacci, haka ma bayan sahur. Cikin baccin na ji ana lalubata, a firgice na farka jin ana ƙoƙarin haɗe mini ruwan ciki da katifar gadon, Allah ya ba ni sa'a na wancakalar da ko ma waye tare da tashi zaune ina ƙoƙarin kurma ihu. Wanda na yi tozali da shi ya sa na fasa, ƙura masa ido na yi cikin wata irin mummunar faɗuwar gaba. Muryata na rawa na ce. "Mansur!" Bai amsa ba sai ƙara kusanto ni da ya yi, daga shi sai gajeren wando. A ruɗe na ja baya na mannu da fuskar gado fahimtar abin da yake nufi. Jikina na rawa na ce. "Na shiga uku! Mansur azumi fa ake yi, ko ka manta ne?" Cakuma ta ya yi cikin wata ƙatuwar murya ya ce. "Ke kika san azumin." Tare da fara raba ni da kayan jikina. Duk yadda na so ƙwace kaina amma na kasa, don ƙarfi ya gwada gurin matse ni. Ba yadda ya bi da ni kamar dabba babu wasan komai ne abin damuwata ba, azumin da ke bakinmu da yadda yake ƙoƙarin amfani da ni ta baya shi ne babban tashin hankalina. Yana daf da cimma burinsa Allah ya ba ni sa'a na ƙara hankaɗe shi a karo na biyu cikin zafin nama. Kamar an yi cilli da ni na yi tsalle na bar kan gadon na koma gefe, jikina na kyarma cikin razani na ce. "Mene haka? Me kake shirin aikatawa? Laifi biyu? Ga azumi ga kuma ta gurin da ubangiji ya haramta." Na ƙarashe maganar cikin kuka. Tsaki ya ja ya ce. "Duk ke kika san wannan, ni kawai abin da na sani buƙatata ta biya." Ido na ƙura masa cikin kokawa da numfashina cikin dokawar zuci, tabbas wannan shi ne wanda Maman Nasmah ta tura mini pictures ɗinsa, shi ne ya zo gidanmu zance har sau biyu, shi ne kuma aka ɗaura mana aure da shi, ya zo ranar ɗaurin aure aka yi mana hotuna. Amma ba wannan muryar tasa ce muke waya da ita ba, waccan mai daɗin sauraro da magana cikin taushi ce, wannan kuma ƙatotuwa ce mai hawa kai a maimakon ta kwantar da zuciya. To me hakan yake nufi? Muryar ce ta canza ko kuma me? Na tambayi kaina cikin tsananin ruɗewar rashin sanin wanne iri miji na aura da yake ƙoƙarin aikata manyan laifuka ga Allah da ni matarsa ta sunna a cikin wannan wata mai girma da tarin falala? Wanda kowa burin shi ya nemi rabauta da samun dacewa a gurin mahaliccinsa.........✍️

*Zeey Kumurya*✍️
[3/8, 1:44 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

*BRIGH PENS*
(FREE BATCH)

*23.*
Chapter 44 · 0% Book details