Sashe 35
Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*Zeey Kumurya*âœï¸
[3/8, 1:42 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
*18.*
https://chat.whatsapp.com/EDdhJ4RW54T88HqTwLQWI2
Cikin sauri ya miƙe tsaye zumbur, ledar da ta harɗe masa takalmi ta yi sanadiyar faɗuwar shi ya zare ya nufi bakin toilet yana hucin ɓacin rai ba tare da dube ni ba. Yaran sai sannu suke yi masa kamar za su yi kuka, ni kuma na ci gaba da dariya har da riƙe ciki. Fuskarsa ya wanke tare da cire rigar jikinsa da duk ta ɓaci ya bar singlet kawai. Ya shiga toilet zai cilla ta a cikin bucket ya ci karo da aika-aikar da na yi. Sultan da ya bi shi da wayarsa yana haska masa ya yi saurin toshe hancinsa tare da dawowa baya da sauri. Shi kuwa kakarin amai ya fara. Raina fes kamar takarda na koma ɗaki ina faɗin. "Kaɗan ma ka gani, ba dai ka nace ka ƙi rabuwa da ni ba? Yanzu ka fara ganin abubuwa." Ina jiyo su suka gyara tsakar gidan da toilet ɗin, ban ko matsa ba har suka gama facaka da ruwansu, ina kan sana'ar tawa wato chatting. A lokacin ya hura wuta ya ɗumama musu ruwan wanka suka yi dukansu. Bayan ya gama dube-duben shi ko zai ga na yi girki ya ga ban yi ba ya fice daga gidan. Sai kusan sha ɗaya ya dawo, har time ɗin yaran ba su yi bacci ba. Daga yadda na ji suna murna da ƙarar ledar da na ji na san wani abin cin ya siyo musu.
Bayan sun yi bacci ya shigo ya kwanta, ban ce masa komai ba na fita na shiga kitchen, don yunwa ta fara nuƙurƙusata. Jikina na rawa na buɗe ledar da na gani a kan kanta wanda ƙamshin abin da yake cikinta ya gama buɗaɗe ni na ga banɗashen gurasa ne suka ci suka rage. Zaman ɗabaro na yi a ƙasa na fara ci hannu baka hannu ƙwarya. Sai da na cinye tas na yi gyatsa sannan na tashi na sha ruwa. Ruwan zafin da na gani a flaks na juye na yi wanka. Ina sauke ajiyar zuciyar jin daɗin jikina na koma ɗaki, lokacin ƙarfe ɗaya saura. Ina cikin shiri aka kawo nepa, hakan ya sa na ƙura wa Anas ido da ya yi ɗaiɗai yana bacci hankalinsa kwance. Wani irin takaici da baƙinciki ne ya turniƙe ni, saboda na fuskanci duk abin da zan yi masa ba ya damun shi, sai dai ni kullum ya bar ni cikin damuwa da tunanin mafita. Ƙwafa na yi na miƙe na je na ɗebo ruwa a waje wanda ya yi sanyi kasancewar sanyi ya busa na dawo na hau gadon na yaye bargon da ya lulluɓa na sheƙa masa tun daga fuska har wajen cikinsa. A firgice ya tashi har yana tuntsirar da ni na kusa faɗawa ƙasa cikin kakkarwa. Ina sauke numfashi na ce. "Anas Musa Shu'aibu ka yi wa girman iyayenka ka sauwaƙe mini wannan ƙaddararren auren naka, na ce maka na gaji, ba na son ka, ba na son ci gaba da zama da kai. Ko ana dole ne? Ka yi zuciya mana, ko ba ka da ita ne?" Ya na jifa na da wani irin kallo ya ce. "Ba tsoron rabuwa nake yi da ke ba, ina duba Kawu da su Sultan ne kawai, don tun ina ɗaukar abin naki yarinta da shirme yanzu na gane zallar iskanci ne. Na yi miki zuru na zuba miki ido duk ba kya gani, a kanki har ƙara yawan tsaiwar dare na yi, kowacce Sallah da addu'ar Ubangiji ya shirya ki nake farawa, amma ban ga alamar lamarin naki na ƙare ba ne. Duk abin da za ki yi don ki ɓata mini rai ina sane, dannewa kawai nake yi ba na biye miki amma...." Dogon tsaki na ja na katse shi da faɗin. "Ni ba wani dogon jawabi na nemi ka yi mini ba, kawai saki nake buƙata daga gare ka, tunda kai ka kasa yi mini abin da nake so, ka kasa wadata ni, sai ka saka wanda zai iya yi yana can yana jira na ya ɗauka." Idanunsa jajir alamar ba ƙaramar tafasa zuciyarsa take yi ba ya ce. "In sha Allah a yau zan rabu da ke Hafsah ko ƴar gold ce ke. Na sake ki! Na sake ki!" Ba tare da na damu da dare ne ba na saki shewa tare da kwaso shoki daga zaunen da nake, duk da wani irin abu mai nauyi da ya ji ya tokare mini ƙirjina. Guɗa na rangaɗa na ce. "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Yau na rabu da auren jaraba da ƙaddara." Bai ce komai ba ya tashi ya fice fuuu kamar zai tashi sama. Na raka shi da mugun kallo. Korar duk wata damuwa da ke ƙoƙarin kawo mini ziyara na yi na tashi na fara haɗa kayana. Ji nake kamar na kira Maman Nasmah a daren nan na sanar mata wannan daddaɗan albishir ɗin. Ko kaɗan ban bari zafin sakin ya yi tasiri a zuciyata ba, Alhaji Kyauta da daular da zai mayar da ni kawai nake hangowa, don ko Kawu ba na ji don na gama tsara abin da zan faɗa masa.
Da layi kamar wanda ya bugu Anas ya ƙarasa ɗakin su Sufyan da jan ƙafa ya tura ƙofa a hankali saboda kar su farka ya shiga ya zube a kan dandaryar ledar tsakar ɗakin, yana sassauke numfarfashi da sauri da sauri. Ganin komai yake tamkar a mafarki, bai taɓa tunanin haka za ta faru a tsakaninsu da Hafsah ba. Ko da wasa bai taɓa kawo za su rabu ba idan ba sanadin mutuwa ba. Bai taɓa budurwa ba sai a kanta, daga itan kuma bai ƙara yi ba. Bai san ya zai fara shirin rayuwa da wata macen da ba ita ba. Ƴaƴansa ya kalla da suke kwance suna bacci, wani irin tausayinsu ne ya tsirga masa a cikin zuciya, don ya san zafi da ƙunar yin rayuwa ba tare da UWA ba. Babban tashin hankalinsa inda zai kai su a riƙe su ko kuma matar da zai samu ta riƙe su tsakani da Allah. Don ko sama da ƙasa za su haɗe ba zai taɓa ba wa Hafsah su ta tafi gidan wani da su a matsayin agololi ba. Duk yadda ya yi kar aurensu ya ƙare gabaɗaya ya yi amma sai da Hafsah ta ƙure shi, duk da ya riga ya saka wa ransa hakan rubutaccen abu ne da Ubangiji ya rubuta sai ya faru. Runtse idonsa ya yi yana tuno wayar da suka yi da Naja ɗazu, yadda ta dinga roƙon shi akan ya ƙwace wayar Hafsah ko na wucen gadi ne, sannan ya hana ta fita bare ta je shaiɗanun ƙawayen nata su ƙara ba ta wata, ko hakan zai sa ta hankalta ta dawo cikin hayyacinta. Ya gama tsara yadda zai yi a gobe wanda yake ganin shi ne mafitar da zai sauya komai ashe yana nasa ne Allah na nasa bai sani ba. Ba ƙaramin ɓaci ransa ya yi ba da dattin da Hafsah ta baza ta kacaccala gidan ɗazu, amma duk ya shanye saboda ba ya so ya ɓata plan ɗinsa. Dafe kansa ya yi cikin ƙololuwar tashin hankali yana maimaita "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" A fili. Don shi su Sultan kawai yake ji a faruwar wannan al'amarin. Baccin da bai ƙara komawa ba kenan ya ƙarashe sauran dare a zaune.
Duk yadda na so bacci ya ɗauke ni bayan na gama haɗa kayan amma ya ƙi zuwa, na dinga tsaki ni kaina cikin takaicin rashin baccin. Wayata na soka a chaji na dinga playing videon sabon gidan Aunty Billy nai ta kalla. Hakan ya sanyaya mini rai, na ji kamar na zuƙo watanni ukun da zan yi na idda, don ba ƙaramin ƙaguwa na yi na gan ni ina rayuwa a irin gidajen nan ba. Tun daga lokacin da Anas ya furta ya ƙarashe ragowar sakin da ya rage mana jikina yake ta rawar da ban san dalilinta ba har safiya. Ni dai na san ban bari sakin ya dame ni ba, amma na rasa me ya sa wani abu mai nauyi yay tsayuwar kafaffiyar bishiya a cikin zuciyata ba.
Har gari ya waye Anas bai dawo daga masallaci ba shi da su Sultan, murmushi na yi don na fahimci manufarsa ba zai dawo ba har sai ya tabbatar na bar gidan, saboda kar na ce zan tafi da su. Bai san ma ba zan ce hakan ba, don Kawu ba ƙarfi ne da shi ba yanzu ba zan je na ɗora masa wahala ba, sai na yi aurena zan karɓe su, a lokacin ne dole ya ba ni su ko ya ƙi ko ya so. Kafin takwas na tattara na bar masa akurkin gidansa. Duk da zuciyata na ta azalzalata na kira Maman Nasmah na faɗa mata, amma na ƙi saboda so nake sai na fara gamawa da Kawu tukunna.