← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 54

Sashe 36

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A soro na tarar da shi kamar yadda na yi zato, saboda tunda ya fara ciwon ƙafa nan ne ya koma mazauninsa a kodayaushe saboda masu zuwa dubiya, sai dare ya yi yake lallaɓawa ya koma cikin gida. Kaina a ƙasa na yi sallama bayan na mayar da fuskata kalar tausayi. Ya amsa cikin fara'a, sai dai gani na janye da ƙaton akwati kuma babu yara ya sa fara'ar tasa ɗaukewa cak tare da fara bi na da kallo mai alamar tambaya.
Bayan na tsugunna na gaishe shi ya amsa tare da faɗin. "Lafiya kuwa Hansatu?" Kukan ƙarya na fashe da shi ban ce komai ba. A ruɗe ya ce. "Ba kuka za ki yi ba, bayani za ki mun? Me ya faru na gan ki da wannan ƙatuwar jaka haka? Ina yaran da Anas ɗin?" Cikin sheshsheƙa na ce. "Kawu Anas ya sake ni har saki uku."
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Sa..sa...saki uku fa kika ce?" Ya faɗa kamar zai miƙe, da alama ya manta da lalurar da yake tattare da ita.
Ƙara sakin gunjin kuka na yi na ce. "Eh." Salati kawai ya shiga rafkawa cikin tashin hankali, kamar zai yi kuka ya ce. "Hansatu garin yaya haka ta faru? Me kika yi da kika tunzura yaron kirki mai haƙuri ya yi miki wannan arangizon sakin? Jiya-jiya nake cewa Lami kwana biyu shiru ba ki zo ba ke da yara, da ina da ƙafa da na je na yi bikon ku, ko wani laifin muka yi muku, tunda shi yana zuwa, ko wancan satin ma ya zo da kayan dubiyarsa rigijib, kuma bai ce mini wata matsala tana faruwa a tsakaninku ba, bare na ce ko ita ce sila." Cikin makirci na ce. "Babu abin da na yi masa, kawai wata bazawara ce ta shiga rayuwarsa ta asirce shi ta tarwatsa mana farincikinmu, kusan shekara kenan wulaƙancin yau daban na gobe daban Abban Sultan yake mun, ya hana ni abinci ya dake ni ya zage ni ya kore ni, amma duk na daure na shanye. Sau biyu yana saki na amma na ƙi tafiya bare na faɗa wa wani, sai jiya cikin dare ya cikashe mini na ukun tare da yi mini korar kare, sai a wani kango na samu na raɓa kafin gari ya waye. Wai aurensu ya kusa da bazawarar na fice na ba shi guri zai saka ta, kuma ya ƙwace ƴaƴan ya hana ni tahowa da su." Na ƙarashe maganar ina ƙara fashewa da kuka.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Hasbunallah! Subhanallahi! Wanne irin al'amari ne wannan mara daɗin ji? Lallai bawa ba ya taɓa ƙaucewa ƙaddarar shi, Ubangiji ya sa haka shi ya fi alkhairi. Amma duk da haka zan kira Malam Anas ɗin na ji ta bakinsa." Ya yi maganar cikin matsanancin tashin hankali.
Gwaggo da ke leɓe tana sauraren mu tun zuwana ta faɗo soron tare da yin farat ta ce. "Kar ka soma kiran shi, ai aikin gama ya riga da ya gama tunda ya yi saki har uku, ka ƙyale shi ya je can ya ƙarata. Na ji duk abubuwan da kuka tattauna ai." Cikin jin daɗin maganar tata duk da na san farinciki take da sakin na ce. "Ni ma haka na gani, saboda ko ka kira shi ba za ta sauya zani ba, kuma yaran ma na san ƙauye ya tafi ya kai su, ba bayarwa zai yi ba." A sanyaye Kawu ya ce. "Shikenan, Ubangiji ya fi mu sanin abin da yake nufi da faruwar wannan al'amarin, Allah ya sa haka shi ya fi alkhairi. Amma ban da kin ce ba ya cikin hayyacinsa da ba zan taɓa yarda yaron kirki kamar Anas ne ya aikata haka ba." Gwaggo ta ce. "To ya za a yi, tunda mai duka ya yi ƙarshen auren kenan, sai dai kawai mu yi addu'ar Allah ya kawo mata wani na gari." Gyaɗa kai Kawu ya yi bai ce komai ba, tabbacin abun ba ƙaramin girgiza zuciyarsa ya yi ba. Da hannu ya mun alamar na tashi na shiga ciki, bayan ya tambaye ni Abban Sultan ya ba ni shaida na ce a'a.
Ina lura da Gwaggo kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha don farinciki, don tun can baƙinciki take da yadda muke zaune lafiya da Anas. Murmushi na yi bayan na shiga ɗakina tun na da kafin na yi aure na ce. "Ki yi ta murnarki, ta kusa koma miki baƙinciki, don wanda zan aura ya fi Anas komai da komai."
Sai da na gyara ɗakin don ba zai zaunu ba, saboda karikicen da yake cikinsa. Na haɗe wa Gwaggo shirginta a gefe na ɗauki tabarma a ɗakin Kawu na shimfiɗa, sannan na kira Maman Nasmah cikin ɗoki. Ringing biyu ta ɗaga.......✍️

*Zeey Kumurya ✍️
[3/8, 1:42 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

*BRIGH PENS*
(FREE BATCH)

*19.*

Cikin zumuɗi na ce. "Ta faru ta ƙare!" Cikin rashin fahimta ta ce. "Ban gane ba, ko ya sake kin?" Ina dariya na ce. "Tun cikin daren jiya ma, yanzu haka ina gidanmu." Wata shewa na ji ta saka mai haɗe da ihun murna tare da faɗin. "Don Allah da gaske kike?" Na ce. "Wallahi Allah." Cikin dariya ta ce. "Alhamdulillah! Ni na tabbata na fi ki farinciki da faruwar al'amarin nan, yanzu za ki huta ki wataya ke ma kamar mu." Na ce. "Allah ya nufa ya yarda ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda." Ta ce. "Danmadaƙyar kenan, sakin ukun ne dai ko?" Da sauri na ce. "Ko gargada babu." Dariya ta kuma sheƙewa da ita sannan ta ce. "To Ma sha Allah, yanzu nan da three months kina gama idda zan haɗa ki da Alhaji Kyauta, ku fara shan soyayya." Cikin farinciki na ce. "In sha Allahu." Daga haka muka yi sallama ina murmushi, a muryar Maman Nasmah kaɗai na gane ba ƙaramin farinciki take ba, kamar ma ta fi ni. Hakan ya ƙara mini son ta da yarda da ita a cikin raina, domin mai son ka ne kaɗai zai damu da damuwar ka tamkar tasa, idan abin farinciki kuma ya faru ya fi ka nuna murnarsa.
Maman kuwa tsabar daɗin da ta ji rabon kuɗi ta dinga yi wa masu aikinta, ta rasa ina za ta saka ranta don farinciki. Ta san duk inda Anas yake yanzu yana cikin ƙololuwar ɓacin rai da takaicin Hafsah. Don haka za ta yi amfani da wannan damar ta kai kanta gare shi, ta nuna masa soyayya da kulawa, ta share masa hawayen baƙinciki jakar matarsa, za ta je masa a mutuniyar kirki mai kamewa. Babban abin da zai yi mata cikas aurenta, rabon ta da mijin nata kuma kusan watanni biyar baya kenan, shi ma a lokacin da ya zo kwana ɗaya tak ya yi ya ƙara gaba. Ko time ɗin da za su yi magana ba ta samu ba bare ta je masa da buƙatarta. Ita a yanzu ko ƙasar da yake ma ba ta sani ba, bare ta kira shi su yi magana. Tsakaninta da shi kawai kuɗin da yake sakawa a tura mata duk wata ne, sai lokaci zuwa lokaci idan ta je kamfanunnunwansa ta samu information a kansa cikin wayo da dabarar kar ma'aikatan nasa su gane ita da banza duk ɗaya ne a gurinsa, sun ma fita muhimmanci. Tunda su ba a sati ba su yi magana ba saboda sabgar kasuwancinsa. Hafsah kuma ta san yadda za ta yi da ita akan ƙaryar da ta dinga zabga mata a game da mijin Aunty Billy, ta san me za ta yi yadda asirinta ba zai tonu ba.
Chapter 36 · 0% Book details