← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 54

Sashe 8

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitowar Abban Sultan daga É—aki ya katse mini tunanin da nake yi, ban ko motsa ba bare na nuna na san da wanzuwar shi a gurin har ya zauna a kujerar da take fuskanta ta.
"Magana na zo mu yi Hafsah." Na ji ya faÉ—a ba yabo fallasa.
Kai kawai na ɗaga na kalle shi ban ce komai ba. Bai damu ba don ban ga alamar hakan a fuskarsa ba ya ce. "Tun shekaran jiya nake ta son na ba ki kuɗin da kika ce za ki yi amfani da su a bikin Naja, amma ganin kin ƙi ba ni fuskar ma da za mu yi magana ya sa kawai na kira ta na ce ta tura mini account number ɗinta na tura mata kuɗin ankon sai ta bayar a kawo miki, amma sai na ji saɓanin abin da kika faɗa mini daga gare ta, ta tabbatar mini babu wani bikinta da za a yi. Hafsah me za ki yi da kuɗi da har kika zaɓi yi mini ƙarya don na ba ki? Abin da ba ki taɓa yi mini ba, me na rage ki da shi a zaman mu?" Ya ƙarashe maganar muryarsa na bayyana fusatar da ya yi da abubuwana.
Da sauri na ɗaga kai na kalle shi, wata irin kunya da takaici masu tsanani ne suka lulluɓe ni, kamar na fasa ihu saboda jin ya gano ƙarya da na yi masa. Duk yadda na so ɓoye halin da nake ciki don kar ya gane amma na kasa, haɗe rai na yi tare da ƙoƙarin yin pretending ɗin ni gaskiya na faɗa masa, ɗaga mini hannu ya yi fuskarsa ɗauke da madaukakin ɓacin ran da na jima ban gani a tattare shi ba ya ce. "Don Allah! Na haɗa ki da girman Allah ki faɗa mini Gaskiyar abin da yake damun ki Hafsah, ki faɗa mini mene matsalar da ta saka kika aro wasu sabbin halayen da ba naki ba kike aikatawa, wanda ba za su amfani rayuwarki da komai ba sai dai ma su kai ki ga hallaka? Kin canza mini kin canza wa ƴaƴanki, kin daina yi musu walwala, girki sai kin ga dama kike yi, haƙƙina kuwa an kusa sati rabon da ki ba ni, kuma da iliminki kin san hakan ba daidai ba ne, ba ki da abokin hira a kodayaushe yanzu sai wayarki, na zura miki ido na ga iya gudun ruwanki amma na ga abin naki ba na ƙare ba ne, don haka yanzu na zo masalaha nake nema, don Allah ki yi haƙuri da ko ma mene ne ki zo mu koma rayuwarmu kamar da, mai cike da farinciki da ƙaunar juna." Ya ƙarashe maganar tare da matsowa daf da ni ya kama hannuna a cikin nasa ya fara murzawa, ina jin sassanyar ajiyar zuciyar da ya sauke. Ban ce komai ba sai ƙasa da na yi da kaina, bakinsa a daidai satin kunnena cikin sassanyar murya ya ce. "Please my love! Ko don su Sultan ba don ni ba." Ban san me ya ba na ji jikina ya yi wani irin yi mini sanyi ba, kai kawai na ɗaga masa don na kasa sarrafa harshena gurin furuci. Murmushi ya yi tare da rungume ni a ƙirjinsa ya ce. "Na gode sosai Ummu Sultan ɗita." A hankali na motsa leɓɓena na ce "Ni ma na gode." Ban gama rufe su ba ya ɗora bakinsa a kansu, kiran sallar isha'i ya sa ya sake ni ya tashi, har lokacin murmushi yake wanda yake bayyana tsananin farincikin da yake ciki, duk da gangar jikinsa ta daɗe da alamta mini hakan, ta hanyar yadda ya dinga sakin ajiyar zuciya da abubuwan da ya yi mini cikin rawar jiki.
"Zan je masallaci, ki yi mini tanadi kafin na dawo." Ya faÉ—a tare da ficewa ba tare da ya jira amsa ta ba.
Dogon numfashi na ja na sauke cikin wani irin yanayi da ban san ya zan fasalta shi ba, ina son mijina sosai so mai tsanani, kamar yadda na san bayan mahaifana babu mai so na sama da shi a duniyar nan.
Yadda ya zauna a gabana da farko cikin ɓacin rai kawai na tuno, amma cikin lokaci kaɗan ya haƙura ba tare da na ba shi haƙuri ba, ya mayar da laifin kansa duk da tarin wanda na yi masa, ya ba ni haƙuri a madadin ni na ba shi, ƙaryar da na yi masa ma da ya fahimci na ji kunya sai ya bar maganar. Anya kuwa irin mijina suna da yawa a duniya? Ba na jin akwai matar da za ta fi ni dacen miji mai kulawa da nuna tsantsar soyayya a zamanin nan, ga shi da tarin ilimin addini da aiki da shi, a kodayaushe shi mai ƙoƙarin ganin ya kyautata mana ne.
'Da ya zo a mai kuÉ—i da sai jin daÉ—i da farincikinmu ya ninka haka.' Wani sashi na zuciyata ya ce mini haka. GyaÉ—a kai na yi kamar mai magana da wani na ce. "Tabbas haka ne, domin kuwa kuÉ—i shi ne kaso ma fi rinjaye na jin daÉ—in rayuwa."
Tunanin kar a ɗauke wuta ga wayata babu chaji ya sa na miƙe na soka, sannan na fita waje don yin alwala.
Ina kan darduma suka dawo shi da su Sultan, da gudu suka shigo É—akin Sufyan ya faÉ—a kan cinyata yana faÉ—in. "Mami mun dawo." Kansa na shafa na ce. "Ka kusa karya mini cinya Babana, ko kai ba ka san ka girma ba ne yanzu?"
"Ta ina zai sani tun da kin ƙi yi masa ƙani?" Abban Sultan da ke tsaye yana kallon mu hannunsa harɗe a ƙirjinsa ya faɗi haka.
Kallon shi na yi na juya masa ido na ce. "Ai daga kai ne." Ya ce. "Ko?" Na gyaÉ—a masa kai kawai. Murmushinsa ya yi mai kyau bai ce komai ba.
Shi ya yi wa Sufyan wanka bayan mun ci abinci, ya kwantar da su da wuri tun kafin lokacin da suka saba kwanciya. Duk wani abu da ya kamata na yi a lokacin shi ya yi, ni dai ina zaune ina ta sana'ar tawa wato tunani.
A haka ya dawo ɗakin ya same ni, bayan ya zauna a kusa da ni ya dube ni a tsanake ya ce. "Tun ɗazu na lura da yanayinki Hafsah kamar kina cikin damuwa sakamakon abin da na faɗa miki, ko kuma kina jin kunyar abin da kika aitata. To in dai ni ne komai ya wuce, ba zan ƙara taho da maganar ba in sha Allah, ki kwantar da hankalinki ki saki jikinki mu koma kamar da, kuɗaɗen da kika tambaye ni kuma duk da ban san me za ki yi da su ba, amma na san tunda kika tambaya kina da buƙatar su, don haka da yardar Allah jibi zan ba ki 5k, sai ki yi amfanin da za ki yi da ita." Cikin farincikin samun kuɗin ɗinkin da nake ta tunanin ta yadda zan samu idan Maman Nasmah ta aiko mini da atamfar na saki ajiyar zuciya. Fuskata ɗauke da yalwataccen murmushin da na daɗe ban yi ba na ce. "Na gode sosai mijina." Yana murmushin shi ma ya ce. "Babu komai ƴar aljannatah, duk abin da kike so a duniyar nan ba zan taɓa ƙin yi miki ba matuƙar bai fi ƙarfina ba."
Daga haka muka shiga fagen da muka daɗe rabon mu da shi, sai a lokacin na gane ni ma ba ƙaramar kewar shi na yi ba. Bayan komai ya lafa ya yi bacci na ji ni ba zan iya baccin ba idan ban kunna data na ga halin da group ɗinmu yake ciki ba da abubuwan da aka tattauna, ina son group ɗin sosai, ba ma ni kaɗai ba, duk wanda yake cikinsa yana mugun son shi, saboda gida ne mai matuƙar shiga rai, kullum cikin hira muke kamar ƴan'uwan juna ba haɗuwar media ba. A hankali na zare jikina daga na Anas na sauka daga kan gadon na fita parlour na ɗauki wayata, zama na yi a kan kujera na kunna data. Messages na gani sama da goma Maman Nasmah ta yi mini, da sauri na shiga na fara dubawa. Hoton Atamfa ta turo mini ta ce ga shi har ta je gidan admin ta karɓo mun, sai kuma hotunan da suka yi a gidan admin ɗin da video. Cikin rawar jiki na buɗe na shiga kalla. Sai da zuciyata ta yi wani zillo tsabar haɗuwa da tsaruwar parlour'n da aka yi musu wani video, kusan gabaɗaya parlour'n sai da ya fito, saboda juyin da Maman Nasmah take yi da wayar tana cewa "Yau dai ga ni a gidan Aunty Billy Admin." Cikin dariya. Parlour ne wanda ya gama tsaruwa tun daga kan ginin shi da irin ƙawar da aka yi masa, da kuma kayan alatun da aka wadata shi da su, wanda kallon su kaɗai ma ya isa ya saka mutum farinciki. Wani ɗan ƙundulen abu da ya tsaya mini a maƙoshi na haɗiye tare da ɗaga kaina na bi akurkin parlourna da kallo kasancewar da akwai NEPA har lokacin, hakan ya sa na ji wani abu mai ɗaci yana yi mini yawo a ƙirji.
"Dole ne fa duk rintse duk wuya ni ma na fara rayuwa a irin waɗannan tafka-tafkan gidajen nan kusa, ko ta halin ƙaƙa." Na faɗa a fili kamar zan rusa kuka. Sauran hotunan na ci gaba da kallo, har da wanda suka yi a farfajiyar gidan, iya motocin da suke fito ta cikin hoton sun kai shida a cikin wata ƴar rumfa, ga wasu irin fitulu da suka haskaka gurin tamkar rana. Abayoyi duka a jikinsu, wanda ko ba a faɗa ba na san masu tsada ne, ga shi sun dace da jikinsu ɗan kuɓul irin na masu hannu da shin. Voice ɗinta wanda shi ne last a cikin messages ɗin da ta mun ba ƙaramin razana zuciyata ya yi ba. Idanuna na waro waje kamar zan zubar da su a ƙasa na ƙara maimaita saurara don jin ko kunnena ne bai ji mini daidai ba, amma still abin da na ji da farko shi ya ƙara mamaye masarrafar jina...✍️

*Zeey Kumurya ✍️*
[3/8, 1:36 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

6.
Chapter 8 · 0% Book details