← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 54

Sashe 53

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

nuna Kareema ya ce. "Wannan ce mai ɗakin tawa, wannan kuma ta nan gidan jikin gidanka ce, mun fito muka haɗu da ita za ta shigo ita ma." Sheshsheƙar kukana ce ta hana shi maganar da ya buɗe baki zai yi, da sauri Maman Hanif ta ce. "Kamar kuka ko?" Kareema ta ce. "Eh, Aunty Amarya ce kuma take yi, lafiya?" Ta ƙarashe maganar idanunta a kaina. Cikin pretending ina cikin matsanancin tashin hankali na ɗora hannuna akai na ce. "Don Allah ku ba shi haƙuri, ni na ba shi ya ƙi haƙura, ku taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ku!" Cikin mamaki Maman Hanif ta ce. "A'a, me ya faru? Ba rakiya za ki yi masa ba da ma ganin kun da muka yi?" Girgiza kai na yi na tashi a haukace na cilla mata takardar hannuna na ce. "Duba ki gani, wai ya sake ni, kuma ban da kowa, ban da wani sauran gata sai shi, don darajar Allah ku ce masa ya mayar da ni. Ya ɗauki wani matakin a kaina kowanne ne zan jure amma ban da wannan, ba zan iya ɗauka ba, ya yi mini tsauri da yawa." A firgice ta miƙe ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Har saki uku!" Tashi ya yi shi ma ya ce. "What?" Tare da tsare ni da ido cikin wani irin yanayi. Sai a lokacin mijin Kareema ya yi magana ya ce. "Subhanallahi! Ashsha! Saki kuma? Alhaji me ya yi zafi?" Karɓar takardar Kareema ta yi fuskarta ɗauke da tashin hankali ta ce. "Ko dai ba ki gani daidai ba ne Aunty Hafsah?" "Zan fi kowa farinciki idan haka ne, shi ya sa na ba ku, ku duba ku gani ko idona ne yake yi mini gizo." Na faɗa ina ƙara rushewa da kuka. Dafe kanta ta yi tana salati, Maman Hanif da sosai ruɗu ya bayyana a kan fuskarta ta ce. "I'm speechless!" Satar kallon Idonnera na yi na ga ko motsi ya kasa yi, alamun suman tsaye ya yi saboda tsananin mamaki. A hankali na sauke numfashi tare da ɗauke idona daga kansa, mijin Aunty Kareema da ya karɓi takardar ya duba ya ce. "Aikin gama ya riga da ya gama, har saki uku! Irin wanda Allah ba ya so, garin yaya haka ta faru Alhaji? Da na san abin da za mu tarar kenan da ba mu shigo ba." Dogon numfashi ya ja ya sauke, yana karɓar takardar tare da dubawa ya ce. "Ƙaddara ce kawai, ka san aure rai ne da shi, idan Ubangiji ya rubuta ya ƙare ko second ɗaya ba zai ƙara ba sai an rabu, ko ana so ko ba a so." Mijin Kareema ya ce. "Haka ne, Allah ya sa mu dace mu fi ƙarfin zuciyarmu, har an shiga sallar Magriba, mu za mu tafi Allah ya kiyaye gaba." Zubewa na yi a ƙasa na ɗora hannu aka, ina kuka na ce. "Kar ku tafi ku bar ni ba ku saka ya mayar da ni ba don Allah." Cikin tausayawa Maman Hanif ta kama ni ta miƙar da ni tsaye, tana gyara mini hijabin jikina ta ce. "Ki yi haƙuri, ki yadda da ƙaddara, shi ne cikas imani." Ban ce komai ba na ci gaba da kukan da babu yadda za a yi mutum ya ce ba har cikin zuciyata yake ba. Sosai na hangi mamaki da ruɗu da shock a fuskar Alhaji Mansur, bi na kawai yake yi da wani irin kallo da na kasa gane ma'anarsa. Bai kuma magana ba ya juya ya fita bayan ya yar da takardar. Lallami da ban baki Maman Hanif tai ta mun kamar za ta yi kuka, sai haƙuri take ba ni, gami da yi mini nasiha. Kareema kuwa ba ta koma gida ba sai da ta tabbatar na bar unguwar, ko tsinke ban ɗauka ba daga ni sai jakata, ko kayan sakawa ban bi ta kansu ba, ni dai tunda burina ya cika ji nake kamar an tsunduma ni a cikin aljanna, sai godiya ga Allah kawai nake yi.
Chapter 53 · 0% Book details