← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 54

Sashe 38

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

turo mini. Amma sai na ga lambar Anas ce. Ban san me ya sa ba na ji zuciyata ta doka, jikina na mazari na buɗe amma sai na ga babu komai, ba abin da aka rubuta. Umarnin kiran shi zuciyata ta ba ni, bijire mata na yi cikin takaicin yadda na damu, cikin haushi na ja tsaki tare da taɓe baki ina faɗin. "Goge lambarsa ma zan yi, kar zamanta a cikin wayata ya shafa mini salalan tsiyar talauci." Bayan Azhar na karɓo wayata daga chaji na ga an kikkira ni da baƙuwar number har two missed call. Bin bayan kiran na yi, tana shiga na ji an katse an kira. Kafin na yi magana na ji wata irin murya mai sanyi da kamewa ta yi sallama. Amsawa na yi tare da faɗin. "Wa ke magana?" Bai amsa ba ya ce. "Da fatan ina magana da tauraruwa mai hasken da ya haskake zuciyata tun kafin na gan ta a zahiri?" Shiru na yi ina maimaita kalamansa a cikin raina, sai da ya ƙara magana sannan na ce. "Ai gabaɗaya ka sani a duhu ne, har na fara tunanin ko wrong number ka kira." Murmushi ya yi mai sauti wanda na ji shi har cikin kaina ya ce. "Ai zuciya ba ta taɓa mistake akan dukkanin abu mai muhimmanci a gare ta, ke ce wadda nake nema Hafsah." Ya yi shiru na wasu sakanni alamar ba ya iya dogon zance sannan ya ci gaba da magana. "Sunana Mansur Ibrahim Idonnera, ƙawarki takwararki ce ta ba ni numbernki, tunda ta tura mini hotunki na gani na rasa sukunina gabaɗaya, tun lokacin har yanzu ina kwance ina ta tunaninki ne kawai, sai yanzu da kika ɗaga na ji wannan zazzaƙar muryar taki na ji na fara samun nutsuwa." Ƙaƙƙarfar ajiyar na sauke, da ma ina ta addu'a Allah ya sa shi ne wanda Maman Nasmah ta ce za ta haɗa mu, don muryarsa kaɗai ta tabbatar da yanayinsa, yadda yake magana a kasalance yana jan numfashi ba ƙaramin burge ni ya yi ba, daga ji babu tambaya jiƙaƙƙe a can ƙasan tekun kuɗaɗe, ga sunansa kuma da ya ƙara tabbatar mini da haka. Murmushi na yi tare da kwanciya don wayar ta fi armashi na ce. "Duk wannan yabon ni kaɗai?" Ya ce. "Kin fi gaban haka ma zinariyar mata, yanzu dai ki sanar mini na karɓu ko sai na ƙara zage damtse kar zuciyata ta buga." Siririyar dariya na saki tare da ƙanƙame wayar ban ce komai ba. "Dariya mai daɗi da saka nishaɗi." Ya faɗa ƙasa-ƙasa kamar mai raɗa. Hakan ya haifar mini da tashin tsigar jiki. Lumshe idona na yi na ce. "Idan akwai abin da ya fi karɓuwa ma ka yi shi a gurina." Ya ce. "Wow, thank you, dole na bayar da tukuicin amsar nan." Murmushi na yi na ce. "Ai kai ne tukuicin." Ya ce. "Bayan ni ma akwai buƙatar wani, ki tura mini account number ɗinki na saka mini tukuicin, ko kuma ki faɗa mini wani abun da kike so na saka a kawo miki." Cikin jin daɗi na ce. "Na gode, amma account ɗina ba ya aiki yanzu." Don ba zan ce ban da shi gabaɗaya ba ya raina ni." Ya ce. "Zinariya guda ba account kuma nake zaune, bari na kira wani na haɗa ku, sai ki je bank ɗinsu ya buɗe miki duk lokacin da kike so, ni yanzu ba na Nigeria ne amma da ni zan zo na kai ki da kaina." Na ce. "Babu komai, hakan ma ni ce da godiya." Daga haka muka yi sallama bayan ya ce zai tura mini kati. Ina ta rawar murna na samu irin mijin da nake so message ya shigo wayata, ina dubawa na ga credit ne na 20k, murza idona na yi don ƙara tabbatarwa ko shi ne bai ganar mini daidai ba, amma still haka na gani. Waro ido na yi na yi tare da dafe ƙirjina na ce. "Katin dubu ashirin? Katin waya na kira kawai!" Gabaɗaya sai na ruɗe na susuce, na kira Maman Nasmah na sanar mata ba ta ɗaga ba. Sai na hau online na shiga chat ɗinmu, na ga ta tuttura mini hotunan Mansur, cikin azarɓaɓi na buɗe cike da matsuwar son ganin yadda kamanninsa da komai nasa za su kasance........✍️
Chapter 38 · 0% Book details