← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 54

Sashe 7

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Bayan Magriba ina zaune a parlour ina chatting da ƙawayena na ga messages suna ta shigowa na group ɗinmu na *Zumuncinmu*, da sauri na shiga group ɗin don ganin abin da ake tattaunawa akai. Da message ɗin wata Maman Ayman na fara cin karo, ta turo video na wata tsaleliyar waya a cikin kwalinta kamfanin iphone. Ban san lokacin da na tashi zaune daga kwancen da nake ba saboda tafiya da ni da wayar ta yi. Babu abin da ya fi jan hankalina sama da cewar da ta yi mijinta ne ya siya mata saboda yadda ta ci burin taron da za mu yi, don ta je da sabuwar waya ta sha pictures. Ci gaba da bin chat ɗinsu na yi ina karantawa da saurarar voice note, congrats akai ta yi mata, daga baya kuma aka koma maganar kuɗin wayar, wanda ba ƙaramin gigita ni suka yi ba saboda yawan su da na ji.
'Wayar kawai aka siya da waɗannan maƙudan kuɗin?' Na tambayi kaina a kiɗime.
Ban kai ga samun amsa ba na ƙara cin karo da wani abun da ya ruɗa zuciyata, Maman Nasma ce ita kuma ta turo tsaleliyar mota ta ce mijinta ya siya mata a yau ɗin nan. Hannuna har rawa yake yi gurin yin zooming ɗin motar yadda zan fi ganin ta da kyau. Ko a kan titi ban taɓa ganin motar da ta tafi da imanina irinta ba. Na kwashe mintunan da ban san adadinsu ba ina aikin kallon mota da waya, sannan na haƙura ba don na gaji ba na yi musu fatan alkhairi kamar kowa. Ina ƙoƙarin fita daga group ɗin na ga Admin ta yi tagging ɗina ta ce. "Maman Sultan ke kaɗai ce ba ki siya atamfa ba fa har yanzu, ga shi lokacin abun yana ta gabatowa, kar ki rasa ɗinki fa." Wata matsananciyar kunya ce ta lulluɓe ni, lokaci ɗaya na ji gumi ya fara tsatstsafo mini kamar sabuwar ɓarauniyar da aka kama dumu-dumu tana sata, ga shi na rasa amsar da zan ba ta.
Ina nan zaune kamar an dasa dutse na ga Maman Nasmah ta ba ta amsa da faɗin. "Sorry Admin, account ɗinta ne ya samu matsala shi ya sa ba ta turo ba, ta faɗa mini da muka yi waya ɗazu. Wata sassanyar ajiyar zuciya na sauke ganin abin da ta ce, ko kusa tunanin faɗar hakan bai zo mini ba, to account ɗin ma ba ni da shi, ban san ya abubuwan suke ba bare na shirya maganar da za ta saka a yarda. Fita na yi daga cikin group ɗin ban ce komai ba, ina ƙoƙarin barin Whatsapp ɗin gabaɗaya na ga Maman Nasmah ta mini magana ta pc, buɗewa na yi na ga ta ce ta tura kudin atamfata, na bar shi ba sai na biya ba.
Wani irin farinciki da murna ne suka lulluɓe ni, ban san lokacin da na yi mata voice note cikin rawar jiki na dinga kwarara mata godiya ba, na manta sha'af ni ma pretending nake ni matar mai kuɗi ce kamar su, reply ɗin da ta yi mini da faɗin. "Mene abin godiya akan 15k Maman Sultan? Kamar wadda na ba wa 15 millions?" Shi ya dawo da ni cikin nutsuwata daga gigicewar murnar da na yi. Takaici ne ya lulluɓe ni na bayar da kaina da na yi, don duk wanda ya saurari voice ɗin da na yi mata zai gane ba ƙaramar ruɗewar farinciki na yi ba. Nuna mata na yi ai shi alkhairi ba ya kaɗan, don haka dole na yi murna, daga nan na kashe data ina jin zuciyata cikin yanayi biyu, na farincikin biya mini kuɗin atamfar da Maman Nasmah ta yi da kuma fargabar Allah ya sa kar abin da na yi ya sa ta gane ni matar talaka ce.
Chapter 7 · 0% Book details