← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 54

Sashe 23

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gabana ba." Naja da take jin kamar ta rufe ni da duka ta ce. "Ƙaton gida da hawa manyan motoci su ne a gabanki ko? Ki faɗa mini matar da kika sani da always mijinta ne yake saka mata data da katin da za ta yi waya, idan za ta je unguwa ko'ina ne ya ba ta transport, na tabbata da za ki cikiya kafin ki samu ɗaya sai kin samu 50 da ba a yi musu. Ke fa tsabar daɗi ko sana'a ba ki taɓa gwadawa ba, saboda ba ki da buƙatar komai, yi miki ake kina daga kwance ƴar gata. Kuma ko ma ba wannan ba, kwanciyar hankali ya fi komai a rayuwar nan, ka ci ka sha, ka yi ibada ba wani tension ka yi baccinka, me ya fi wannan daɗi? Anas shi ne gatanki, shi ne suturarki, shi ne rufin asirinki, ko kaffara ba zan yi ba idan kika rabu da Anas ba za ki taɓa samun miji kamar shi ba, don irinsu a yanzu ba su da yawa, sun yi ƙaranci." Da sauri na ce. "Zan samu wanda ya fi shi mana, sosai ma." Murmushin takaici ta yi ta ce. "Ban san lokacin da kika koma mayyar kuɗi ba, idan kuɗi kike nufin za ki samu wanda ya fi Anas za ki samu sosai ma, amma samun mai nagartar shi ne zai yi miki wahala. Ana cewa mazan aure sun yi ƙaranci, ba ƙaranci suka yi ba, samun nagari nagartacce ne ya yi wahala. Kin gan ni nan, ban rasa mijin aure wanda zai aure ni ba, amma na rasa nagartacce wanda nake da yaƙiyin zai riƙe ni saboda Allah ya kyautata mini, wanda ya san ma mene ne auren, don matsalar da take damun mu yanzu majority ana auren ne kawai ba don an san mene ne shi ba, ba don an ɗauke shi ibada ba, ana yin shi ne don wata buƙata, ko a bi kyau, ko kuɗi, ko neman ɗaukaka, ko dan a ce mutum ya yi auren shi ma, gabaɗaya ba ga matan ba, ba ga mazan ba, duk an daina aure saboda Allah da bauta masa, ƙalilan ne masu yi don haka. Wasu kuma ilimin zaman auren ma da yadda za su tafiyar da junansu a zamantakewar auren ne ba su da shi. Rimi-rimi za ki ga mutum ya zo mini da gaske da niyyar aure, amma daga mun yi dogon zama zan gane ba za mu zauna inuwa ɗaya ba, masu kuɗin da masu kyan da talakawan duk suna zuwa, amma samun nagartaccen a ciki ya yi wahala, saboda Juma'ar da za ta yi kyawu tun daga Laraba ake gane ta. Maza na gari sun yi wahala Hafsah, ki riƙe mijinki gagam wallahi, idan ba haka ba za ki yi da na sani mara amfani, za ki yi nadama a lokacin da time ya ƙure miki, za ki yi saki na dafe. Yanzu da za ki yi shela ki fadi halin Abban Sultan ki ce idan da mai son shi za ki bari ta aure shi sai kin ga mata dubu sun zo, kuma da kike ta cewa talauci ai shi ba talaka ba ne, yana da rufin asirinsa, bai taɓa gazawa ba tunda kuka yi aure. Na ga gidan hayar da kuka fara zama kafin Allah ya hore masa ku yi naku, abokan hayar taku sha'awar ku suka dinga yi, yadda yake kula da ke da tattalin ki, ya ba ki lokacinsa. Mama kullum cikin sam barka take yi miki, kullum aka tashi zance aka ce maza sun zama ƴan kansu yanzu sai ta bayar da misali da ku, ta ce ƙawar Naja kuwa ta yi dace da mijin marainiya, Allah ka ba wa ƴaƴanmu irinsa." Baki na taɓe don ni gabaɗaya hankalina yana kan yadda za a yi na fito fes a taronmu na ce. "Sai faɗar alkhairinsa kike amma ban ji kin faɗi aibunsa ko ɗaya ba, mutumin da yake zuba mun uban kulle, kamar wata kayan kadara." Numfashi ta sauke ta ce. "Alkhairin nasa ne ya fi aibun yawa, kulle kuma tabbas na san yana da shi, kuma da ma ai ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, amma duk da haka ai ba ya hana ki zuwa biki ko sunan dangi da na maƙota, duk abin da ya faru na jaje yana barin ki, ki je, fita ce haka barkatai babu dalili yake hanawa, ko so kike ya bar ki kina wuni a maƙota da gantali a unguwa?" Hararar ta na yi na ce. "Ban sani ba, tunda ba ke ake turkewa a gidan kamar akuya ba ai dole ki ce haka. Nan gidan Maman Sadik ga baki ga hanci, jikin gidana amma sai na yi watanni ban je mata ba, tun suna shigowa su har sun gaji sun daina saboda ba na zuwa." "To me za ki je ki yi musu? Na ga Asma'u cousin ɗita da suka zuna a bayan layin nan yabon ki ta dinga yi, lokacin da aka yi wani faɗa har da zuwa police station, a saboda irin yawon gulmace-gulmacen nan da ake yi na bin gidan maƙota kullum, ta ce kin huta abinki, ko me za a yi na tashin hankali babu ke a ciki, asirinki a rufe. Amma ke kin raina hakan ko?" Na ce. "Ai shi saboda kar na fita na ga halin da duniya da take ciki ne ya sa yake kullen, kar kuma na ga yadda maza suke bauta wa matansu tunda shi ba ya yi." Naja ta ce. "Ko? To kar ki nutsu ki san inda yake yi miki ciwo, duk da zan yi miki uzurin rashin sanin halin da duniya take ciki, na rayuwar ƙarya da packaging da mutane suka ɗaura wa kansu, shi ya sa kike ganin kamar su waɗancan matan komai gaskiya suke faɗa. Tunda babbar wayar ma ba ki daɗe da fara riƙe ta ba." Cikin ƙosawa da jawabanta na ce. "Su fa ba maƙaryata ba ne, saboda sun sassan gidajen juna suna zumunci, idan ƙarya suke ai ba za su bari a je inda suke ba." Jinjina kai ta yi ta ce. "Ni fa ban ce ba masu kuɗi ba ne, amma ba zai yiwu a ce duka group ɗin ke kaɗai ce talaka kamar yadda kike faɗa ba, kuma masu kuɗi wanda suka tashi a cikinsa ba za su yi irin wannan banzar rayuwar ba, ta komai naka sai ka tura a group an gani, ka yi son a sani, sai dai ko ƴan taka haye ne ƴaƴan Malam Shehu suka auri masu kuɗi, shi ne ba a saba da rayuwar ba ake nuna wa duniya, ko kuma duk packaging ne kashe kai ake a yi abin ƙaryar. Kuma ko da ma masu kuɗin ne kina da tabbacin kowacce tana zaune lafiya cikin kwanciyar hankali kamar ki? Wata ƙila mijinta mai duka ne, wani ɗan shaye-shaye, wani mai bin mata ko maza, wani ma kuɗin ba na halak ba ne, ba ki san ta yadda suke samun su ba." Ɗaga mata hannu na yi na ce. "Kar ki yi musu mugun fata kuma." Murmushi ta sake yi ta ce. "Misali kawai nake ba ki, ba wai ina nufin hakan ba ne, kawai dai ina faɗa miki ne don na san ba za a rasa ba. And lastly yanzu ƙwarya ta bi ƙwarya ake yi, idan kina tunanin za ki kashe aurenki ki fita ki auri mai kuɗi to kin yaudari kanki, don kowa ɗan'uwansa yake aure, talaka sai talaka mai kuɗi sai mai kuɗi, sai dai ikon Allah da tsananin rabo ne yake saka mai kuɗi ya auri talaka." Miƙewa na yi a fusace na ce. "Ya ishe ki haka wannan cin fuskar da kike mun!" Ita ma miƙewar ta yi ta ce. "Idan na ci miki fuska ai kaina na ciwa Hafsah, gaskiya nake faɗa miki, kuma da ma an ce ɗaci gare ta, ki zauna, ki nutsu, ki yi nazari da kyau don Allah, ko don ƴaƴanki da ke kanki. Zan kira Anas mu yi magana da shi idan na koma gida, zan ce masa ni na hana ki tafiya, na san ba zai ƙi mayar da ke ɗakinki ba in sha Allah. Duk da na ga ransa a matuƙar ɓace ya bar gidan nan lokacin da na shigo, don ba na jin ma ya lura da ni. Please ƙawata ki watsar da mutanen can, ki manta da su, ki bar group ɗin ki goge numbers ɗinsu, ke ki canza sim ma gabaɗaya yadda ko sun kira ba su same ki ba, idan ba haka ba wallahi za su kai ki su baro." Na ce. "Na ji na gode." Bi na kawai ta tsaya tana yi da kallo na wasu sakanni. A sanyaye ta ce. "Idan kika bar Anas ba shi kaɗai kika butulcewa ba, har da ubangijin da ya tsamo ki daga cikin jarrabawar rayuwa, ke kuma kike ƙoƙarin siyen ta da kuɗinki. Kina da iliminki na addini daidai gwargwado, kin san arziƙi da talauci duk na Allah ne, a kullum Ubangiji cikin raba arziƙi yake da ƙwace shi, babu wanda aka haifa da dukiya, kowa da kika gani a nan gidan duniya ya samu kuma a nan zai bar shi. Don haka wannan kaɗai ya ishe ki darasi a rayuwa. Ƴaƴa da miji na gari da lafiya su ne babban arziƙi a duniyar nan, kuma duk Ubangiji ya ba ki su, maimakon ki gode masa sai ki raina?" Shiru na yi don zuwa yanzu maganganunta sun fara ratsa ni sosai, ganin haka ta dafa kafaɗata ta ce. "Zan tafi, ina fatan za ki yi amfani da dukkan shawarwarin da na ba ki, sannan kuma don girman Allah kar ki ƙara kwatanta haukan zagin Anas, bare ki taɓo iyayensa, ina jiye miki siyen ticket ɗin wutar jahannama da hannunki, tunda kin san hukuncin mai aikata abubuwan da kike yi a musulunci. Don haka idan kunne ya ji jiki ya tsira!" Daga haka ta ɗauki jakarta ta juya ta fice. Kasa kataɓus na yi na bi bayanta da kallo kawai cikin mutuwar jiki, gabaɗaya ta gama ɗaure ni da jijiyoyin jikina. Na shafe kusan mintuna biyar kafin na ja ƙafata na shiga ɗaki. Ringing na tarar wayata tana yi, na ƙarasa na lalubo ta
Chapter 23 · 0% Book details