Sashe 3
Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Saukar da idona na yi a kan wardrobe É—inmu, wadda na san a irin gidansu Maman Fa'iz ko a É—akin mai gadi ba za a saka irinta ba. Komawa na yi na kwanta, saboda tsabar tunani kaina har wani juya mini yake yi. A lokacin Anas ya shigo É—akin bakinsa É—auke da sallama, na amsa masa ciki-ciki. Bai damu ba ya dube ni cikin kulawa tare da faÉ—in. "Ya kika kwanta kuma ba ki saki net ba? Duk da akwai Nepa ai sauro yana yawo." Na ce. "Zan saki ne." Yana sakin net É—in ya ce. "Kin je kin tofa wa su Sultan addu'a ne?" Cikin Æ™osawa da maganar tasa na ce. "Eh." Ya ce. "To bari na kakkashe Æ™waiÆ™waye na zo mu yi magana, don wannan yanayin da kike ciki na san ba Æ™alau ba my love." Baki kawai na taÉ“e ban ce komai ba, ya gama abin da zai yi ya hawo kan gadon ya ja ni jikinsa ya ce. "Don girman Allah ki faÉ—a mini abin da yake damun ki, wallahi ganin ki a haka gabaÉ—aya ya hautsina zuciyata." Na ce. "Ba komai fa, ka yi baccinka kawai." Ƙasa ya yi da murya kamar kodayaushe idan yana rarrashi na ya ce. "Ba ma haka da ke, kar mu fara a yau, kin san babu yadda za a yi na iya yin bacci kina cikin É“acin rai, ko kun samu saÉ“ani da wani ne ta waya? Na ga da tana hannunki kina ta tsaki." Hararar shi na yi na ce. "Ko É—aya, tunda na ce maka babu komai ka Æ™yale ni mana!" Shiru ya yi kawai, duk da duhu ne amma na san kallo na ya tsaya yana yi. Barin jikinsa na yi na koma can Æ™arshen gado ina jan tsaki a cikin zuciyata. Don ni gabaÉ—aya gani nake shi ne matsalata, da ya zo a mai kuÉ—i ai da yanzu ba na cikin fargabar fita kunya a cikin group É—inmu. Ina jin shi yana sassauke numfashi na yi banza da shi. Na san abu biyu ne ya haÉ—ar masa, baÆ™on halin da na tsiro da shi da kuma tabbacin rashin samun haÉ—in kaina da zai yi idan ya buÆ™ace ni, don ba Æ™aramin tanadi ya yi wa wannan daren ba, saboda yau da safe na yi wankan tsarkin hailar da na yi kwanaki biyar ina yi, tun kafin ya fita yake É—oki, da rana ma da ya muka yi wayar da muka saba yi kullum idan ya fita sai da ya yi mini zancen. Na É—auka ya haÆ™ura amma sai na tsinkayi muryarsa a raunane yana faÉ—in. "Shikenan Hafsah tunda haka kika zaÉ“a, ba zan takura ki dole sai kin faÉ—a mini abin da yake faruwa ba tunda kin É“oye, amma don Allah ki daina bayyana É“acin ranki, kin fi kowa sanin yadda hakan yake taÉ“a ni sosai ya kuma sanya ni a cikin damuwa, ba ki ji yadda nake ji a cikin raina ba, gabaÉ—aya na rasa nutsuwata, don Allah ki yi mini wannan alfarmar." Ture tausayinsa dake Æ™oÆ™arin mamaye ni na yi na ce. "Shikenan, in sha Allah zan yi hakan." Ajiyar zuciya ya sauke mai Æ™arfi tare da faÉ—in. "Na gode tawan, Allah ya yi miki albarka ya ji Æ™an Umma, ya raya mana su Sultan, ya kawo Æ™annensu dozen masu albarka." Ya Æ™arashe maganar cikin sigar tsokana. A daÆ™ike na ce. "Amin." Ban yi niyyar tanka masa ba, amma don ya Æ™yale ni na samu na yi tunanin sama wa kaina mafita na biye masa muka yi magana. Sai dai abin da nake so É—in bai samu ba, don jin shi kawai na yi a jikina a maimakon na ga yana shirin yin bacci. 'Mutum sai jarabar tsiya amma ba ko sisi.' Na faÉ—i haka a cikin raina cikin takaici da haushin shi da yake Æ™ara cika mini zuciya.......âœï¸