Sashe 2
Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dif! Wayar ta ɗauke babu chaji, dogon tsaki na ja na dangwarar da ita a kan dardumar da nake kai. Dama na san hakan za ta iya faruwa, shi ya sa na ƙi hawa online ɗin tun ɗazu. "Mamy me ya faru kike ta tsaki yau?" Cewar Sultan da ya miƙe da plate ɗin abincin da suka gama ci a hannunsa. A kufule na ce. "Ubanka ne Sarkin tambaya ɗan gidan tanbai." Cikin rawar murya kamar zai yi kuka ya ce. "Ki yi haƙuri don Allah." Ban ce komai ba amma jikina ya yi sanyi, miƙewa na yi na ce. "Ku je ku yi alwala ku zo ku yi Sallah, kar ku manta da addu'ar da na ce ku yi wa Abba kun ji yaran kirki." Gyaɗa mini kai suka yi suka fice a tare bayan Safyan ya ɗaukar musu fitila. Kwanciya na yi a maimakon zikiri da na saba yi a irin wannan lokacin, na fara tunanin da ban san ranar gama shi ba, babban takaicina rashin sanin pic ɗin da na tura ya tafi ko bai tafi ba. A haka mijina ya shigo ya same ni. Duk da ban kalli fuskarsa ba amma na san ɗauke take da murmushin da yake shigowa da shi a kullum, a zuci na amsa masa sallamar da ya yi, saɓanin da da nake tashi da hanzari na tarɓe shi. Kunna torchlight ɗin wayarsa keypad ya yi yana faɗin. "Ina ƴar aljannar tawa take ne?" Harara na zabga masa a duhu tare da jan tsaki a zuciyata na rufe idona, cikin raina ina tambayar kaina me ya rufe mini ido lokacin da ina budurwa na amince na aure shi? Ban kai ga ba wa kaina amsa ba na ji yana faɗin. "Subhanallahi! Hafsah ba dai ba ki da lafiya ba?" Saboda in dai ba cuta nake ba, ba ya taɓa zuwa ya tarar da ni a kwance a irin wannan lokacin. Buɗe idona na yi tare da tashi zaune kamar an yi mini dole na ce. "Sannu da zuwa." "Yawwa, me yake damun ki?" Ya yi maganar yana taɓa goshina, muryarsa da alamun ruɗewar da yake yi a duk lokacin da ban da lafiya. Ture hannunsa na yi na ce. "Babu komai." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Kin tabbata my love?" Wani kallo na yi masa tare da faɗin. "Sai aukin soyayya amma babu ko sisi." Yadda na yi maganar dama na san ba zai ji abin da na ce ba. Zama ya yi a kusa da ni yana ƙoƙarin janyo ni jikinsa ya ce. "Ban ji me kika ce ba." Na ce. "Cewa na yi ƙalau nake." Ya ce. "Amma me ya sa na gan ki a haka? Don Allah ki faɗa mini idan ba ki da lafiya mu je chemist ɗin Kamilu ya duba ki." "Lafiyata fa ƙalau." Na faɗa cikin zunɓura baki. Tsayawa kawai ya yi yana kallo na, daga baya ya sauke numfashi ya tashi ya fita daga falon. Raka shi na yi da wani mugun kallo, a fili na ce. "Wai chemist? In ma cutar nake da gaske ba za a kai ni asibiti ba sai wani chemist." Ranar da su Maman Nasma suke zancen family doctor a group ce ta faɗo mini a rai, ƙwafa na ja na koma na kwanta ina wadaran auran talaka a cikin raina. Ina jin shi suna ta hira da ƴaƴansa a tsakar gida, suna biya masa karatun da aka yi musu a makaranta, yana gyara musu inda suka yi kuskure. Tare suka je masallaci suka yi sallar isha'i. Bayan sun dawo ya ƙara tisa ni a gaba da tambayar abin da yake damu na cikin kulawa, banza na yi da shi na juya masa baya. Ya bar ni na ji da rashin chajin wayata ma amma ya bi ya ishe ni, na san yanzu ana can ana ta shan hira a group. Gabaɗaya sai ya tashi hankalinsa, ya dinga lallaɓa ni da roƙon na faɗa masa idan wani laifin ya yi mini ya ba ni haƙuri, sai da na gaji da magiyara sannan na ce masa gajiya ce kawai take damu na. Ko rufe baki ban gama yi ba ya tashi ya ɗauko mini maganin gajiya da ruwa a cup ya kawo mini na sha, sannan ya ce su Sultan su mammatsa mini ƙafata shi zai fita ya wanke musu uniform da takalma. Sai da ya yi wanke-wanken kwanukan da muka ɓata ya dawo ɗakin. Sannu ya yi mini tare da faɗa mini abubuwan da ya yi, na ɗaga masa kai kawai cikin ƙosawa. Bai zauna ba ko ya nemi abinci ya kama su Safyan ya yi musu wanka shi ma ya yi. Ya kai su ɗakinsu ya shirya su ya kwantar da su. A lokacin aka kawo wutar nepa, cikin tsananin farinciki na miƙe na rarumi wayata na nufi socket na soka chaji. Daidai lokacin ya dawo falon yana faɗin. "Bari na goge wa su Sultan uniform ɗin da na wanke yanzu, da safe kin huta aikin ya yi miki sauƙi, ga ruwan wanka can na haɗa miki, ko ba za ki iya zuwa toilet ɗin ba na kai ki?" Kallon shi na yi ba yabo ba fallasa na ce. "Zan iya, ka zo ka ci abinci, na ga tunda ka dawo ko ruwa ba ka sha ba." Ya ce. "Zan ci ne, so nake na gama duk ayyukan don gobe ki samu hutu da bacci ishashshe, kar gajiya ta ƙara damar mini ke." Taɓe baki na yi a raina na ce. 'Hutun ai na banza ne tunda ba a gidan da ya amsa sunan gidan hutu nake ba.' Daga haka na miƙe na fice daga falon. Bayan na fito daga wanka na zarce ɗakin baccinmu, ina cikin shiryawa na ga wata ƙaramar baƙar leda a kan mudubi. Ɗauka na yi na duba abin da yake cikinta, biscuit ne ɗan goma-goma guda biyar da alawa ita ma guda biyar ɗin. Na su Sultan ne da yake siyo musu kullum, idan za su school na ba su bibbiyu, islamiyya ma haka. Taɓe baki na yi na mayar na ajiye. A fili na ce. "Aikin kenan, kullum siyayyar yara ba ta wuce ta Naira ɗari, wasu kuwa komai katan-katan ake dire wa ƴaƴansu, abubuwa masu tsada ma ba ƴan goma da biyar ba." Har na gama shirina ban daina mita ni kaɗai a cikin raina ba, don ban da wani buri a duniya a yanzu da ya wuce na buɗe ido na gan ni a cikin ƙaton gida, mai ɗauke da komai na kayan alatu da abubuwan more rayuwa irin wanda matan cikin group ɗinmu suke ciki. Idona gabaɗaya ya rufe, babu abin da ƙwaƙwalwata take ganewa sai wannan tunanin. Da na koma falo ko sannu ban yi wa Anas ba na zauna na janyo wayata na kunna. Hakan bai hana shi duba na ba cikin murmurshi tare da faɗin. "Kin yi kyau autar matana." Haɗe rai na yi na ce. "Ka faɗa ne kawai don na ji daɗi, amma ka san ba a kyau sai da kayan kyau." Cak ya tsaya da gugar da yake ya zuba mini ido, cikin wani irin yanayi ya ce. "Me yake damun ki ne yau Hafsah? Ban gane me kike nufi da wannan maganar ba? A da idan na ce kin yi kyau murmushi kike yi tare da yi mini godiya ki kuma ba ni tukuci da abin da kika san ina matuƙar so." Cikin ko in kula da yanayin da na gan shi na ce. "Lokacin ban gane halin da duniya take ciki ba ne sai yanzu." "Wanne hali kuma? Ai ƙara saka ni a duhu kika yi." Ya tambaya fuskarsa da alamun damuwa. "Ka ci gaba da abin da kake yi kawai." Na faɗa hankalina akan wayata lokacin da na shiga cikin group ɗinmu. Bai kuma magana ba ya ci gaba da gugarsa, hakan ya yi mini daɗi, don ko ya yi ma ba tanka masa zan yi ba. Chat ɗin da aka yi ba na nan na fara bi, na ga wanda ba su tura pic ɗinsu ba duk sun tutturo, nawa wanda na tura kuma bai tafi ba. Ban ce komai ba na fita daga cikin group ɗin, Na buɗe saƙon Maman Nasma da ta yi mini ta private. 'Takwara ina kika shige ne? Don Allah ki zo ki ba mu hoton nan naki, ko rawar ganin ki kike mana?' Na karanta abin da ta ce a cikin raina, reply na yi mata na tura, sai na ga bai yi tick alamar ya tafi ba. Kashe datata na yi na ƙara kunnawa amma still ya ƙi tafiya. Fita na yi na duba data balance ɗina, sai na ga ashe ta ƙare ne, dama tun yamma da na duba saura kaɗan. Dogon tsaki na ja na ajiye wayar. 'Kai bawa daga wannan sai wannan, Ubangiji ka raba mu da tsiya da talauci.' Na faɗi haka ƙasa-ƙasa tare da miƙewa na bar falon, ina ganin Anas yana bi na da wani irin kallo wanda na san na zallar mamakin sabbin ɗabi'un da bai san ni da su ba ne. Juyi kawai nake a kan gadona cikin rashin sanin mafita, ina tsoron kar na tura hoton Sa'adatu ƙawata na je wata ta san ta a cikin group ɗin, ko kuma tsautsayi ya sa mu haɗu da wata a zahiri ta ga ba ni ba ce. Ni kuma gaskiya ba zan iya tura hotona da na yi da wayata ba, saboda rashin fitarsa da rashin haɗaɗɗen background, sai yanzu nake jin daɗi ma da hoton bai tafi ba. Don duk waɗanda suka turo hotunansu kowacce da kyan ganin ta, alamun da manyan wayoyi suka yi ba jagwal irin tawa ba. 'Ko dai gidan Sa'adatun kawai zan shirya na je gobe ta yi mini hoton a gidanta na tura musu?' Na tambayi kaina cikin tantama don na san ba lallai ya bar ni ba, saboda ban san me ya sa ba, ba wani son alaƙata da ita yake ba. Tashi zaune na yi ina bin ƙaramin ɗakin nawa da kallo, hoton wata Maman Fa'iz ne ya faɗo mini a rai, wanda aka yi mata a gaban mudubin ɗakinta, ta cikin mirror tamfatsetsan gadonta na ƙasar waje ya fito, ga ɗakin daga ga ni ƙato ne.