← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 54

Sashe 17

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ko sama da ƙasa za su haɗe ba zan auri talaka ba. Ga shi ana ta tagged ɗina ana cewa ni ina nawa abubuwan? Rashin abin cewa ya sa ba na yi musu reply. Duk wata tijara da rashin mutunci babu wadda ban yi wa Abban Sultan ba akan ƙin siyo mini wayar da ya yi, na daina aikin komai a gidan, tsakani na da su Sufyan sai hantara da zagi, musamman idan yana gidan, amma duk da haka ko ɗaga kai bai taɓa yi ya kalle ni ba bare ya tanka, duk da ina ganin tsantsar ɓacin rai a kan fuskarsa. Yau ya kama saura kwana biyu taronmu, da daddare bayan na dawo daga gidan gyaran jiki ina zaune a gefen gado ina kallon fatata yadda ta yi wani irin kyau da sheƙi abun gwanin burgewa. Kallon yadda jikina ya koma kaɗai ya na saka ni a cikin matuƙar nishaɗi. Kiran Maman Nasmah ne ya shigo wayata, da murmushi na ɗaga tare da yin sallama, bayan ta amsa na ce. "Ya shirye-shirye?" Ta ce. "Shirye-shirye Alhamdulillah, ai mu mun gama komai, rana kawai muke jira." Na ce. "Masha Allah, Allah ya nuna mana wannan rana dai da rai da lafiya, mu sha shagali mu mori bidirin tanadin da aka yi mata." Ta ce. "Amin, amma dai ya kawo miki wayar?" Na ce. "Hmm, ina fa! Ai da ƙyar ya siya mini, ko tanka ni ba ya yi fa." Ta ce. "Taɓ, kowa kuwa da sabuwar waya zai je gurin nan, daga mai ta million sai mai ta sama da haka, ke kaɗai ce za ki tashi da jagwal." Cikin yaƙe na ce. "In sha Allah ni ma da sabuwa zan zo, bari ya dawo gidan." Ta ce. "Allah ya sa, ki san dai duk yadda za ki yi ya siya miki atou." Na ce. "In sha Allah." Daga haka muka yi sallama ta kashe wayar. Miƙewa na yi na fara zarya a ɗakin, ina tunanin hanyar da zan bi na samu waya mai tsada irinta ƴan group ɗinmu, na ƙulla na ƙunce amma ban da wata hanya sai Anas ɗin dai. Citson yatsa na yi na ce. "Oh Allah, ni Hafsah wacce ƙaddara ce ta kai ni auren mara zuciyar da ba zai iya nemo kuɗin da zai wadata ni da shi ba? Ya mayar da ni zarra a cikin mata ni ma kamar su Maman Nasmah." Tsaki na ja na koma na zauna tare da rafka tagumi. A haka ya dawo ya same ni, na tarɓe shi da kallon banza tare da jan dogon tsaki. Bayan ya rage kayan jikinsa ya na ƙoƙarin barin ɗakin na yi tsalle na sha gabansa, ina bin shi da wulaƙantaccen kallo na ce. "Anas don Allah wai kai wanne irin mutum ne? Ko babu zuciya a ƙirjinka ne da za ka yi amfani da ita ka nemo kuɗi a duk inda suke ka yi mini abin da nake da muraɗi?" Numfashi ya sauke tare da ƙoƙarin raɓawa ta gefena ya fita amma na ƙara tare hanyar, ina hawaye na ce. "Wai mahaukaciya ka mayar da ni a gidan nan ne da sai nai ta maka magana ka ƙi Kula Ni?" "To ai ba ki da maraba da ita." Ya faɗa fuskarsa ba yabo ba fallasa. Bai jira amsata ba ya ci gaba da magana da faɗin. "Duk abin da za ki yi da cin mutuncin da za ki mun na yi wa kaina alƙawarin ba zan kula ki ba, bare na biye miki, har ki yi ki gama." Ƙugu na riƙe a harzuƙe na ce. "Ai ban da ranar ganawa idan har ba za ka yi mini abin da nake so ba, na gaji da zama sai dai na ga a yi wa wasu abubuwa ni ba a min, alhalin su ma mazajen nasu mutane ne kamar kai, ba fin ka suka yi da komai ba, abin da suke yi suke samun kuɗi kai ma za ka iya." Girgiza kai ya yi cikin tsantsar takaici ya ce."Allah ya ganar da ke Hafsah, amma ba zan gajiya da yi miki wannan addu'ar ba." Ina ƙoƙarin ƙara yin wata maganar ya hankaɗe ni ya fice, ƙwafa na yi na koma na zauna ina jijjiga jiki. Sabbin wayoyi da motocin da ƴan group ɗinmu suka tutturo mazajensu sun siya musu sai gizo suke mun a cikin kaina, babban abin da ya fi ɗaga mini hankali yadda duk wadda ta turo abu wani sashi na gidanta ya fito sai na gan shi haɗaɗɗe ginin zamani, wani parking space ma kaɗai sai a saka gidana a ciki ya zauna har da ragowa. Gabaɗaya Anas da duk wata kyautatawa, kulawa da soyayyar da yake min sun fice mini a rai, rayuwar gidan kuɗi da jin daɗi kawai nake hange. Na tabbata yadda nake kwana da wuni da tunanin ranar da mafarkina zai zama gaske idan aka auna jinina ba ƙaramin hawa za a ga ya yi ba. Duk yadda na so mu yi fitina da Anas a daren nan amma ya ƙi biye mini, ƙarshe ma ficewa ya yi ya bar mini ɗakin ya koma nasu Sultan. Da Asuba ina tashi na ɗora daga inda na tsaya, na dinga watsi da kayan ɗakina ina jifan shi da shi, tare da gasa masa duk maganar da ta fito daga bakina. Don hankalina a matuƙar tashe yake na ganin har ana i gobe taronmu amma ban mallaki sabuwar waya ba, kuma kamar yadda Maman Nasmah ta faɗa duk kyawun da zan yi a gurin, da tsadar kayan da zan saka a banza za su tashi idan ban da rantsatstsiyar waya, saboda akwai video da za a yi mana wanda kowa zai ɗaga wayarsa a ciki, so ake mu tashi kan media a taron nan namu, ai ta yawo da videos da pictures ɗinmu, mu zama topic of discussion a ranar, shi ya sa aka ce kowacce ta sako gold. Don haka duk rintsi duk wahala ba zan bari na zamo takashin baya ba, dole duk abin da za a yi ya zamto ina gaba-gaba. Yau idan na je gidan gyaran jiki shi ne za a mun lalle, amma saboda zullumin rashin waya ya sa har 8 ta wuce ban fara shirin tafiya ba. Ina kwance ina aikin kallon hotunan wayoyin da fiye da rabin ƴan group ɗin suka turo a tsakanin shekaran jiya da jiya Abban Sultan ya shigo ɗakin. Kamar an tsikare ni na tashi zaune na dirga daga kan gadon a haukace na je gabansa na haska masa rakwaɓaɓɓen screen ɗin wayata na ce. "Kalli yadda ake abin arziƙi, kalli irin wayoyin da mazajen wasu suka sissiya musu, ni kam Anas anya ka na so na kuwa? Gobe ne abin nan amma ka fitar da ni kunya abu ya gagara." Tankwaɓar da wayar ya yi ya ce. "Ban taɓa sanin ba ki da hankali ba Hafsah sai yanzu, kin taɓa ganin mutum ba shi da gashin wance ya ce sai ya yi irin kitsonta? Kin san kuɗin da mazajen nasu suke da shi ne?" Ina huci na ce. "Ai ba da kuɗin suka zo duniya ba, nema suka yi, kai ma sai ka fita ka nemo a duk inda suke." Murmushin takaici ya yi ya ce. "Kin yi nisa my love, ba za ki taɓa jin kira ba, abu ɗaya nake fata shi ne Allah ya sa ki je ki ga mazajen nasu ba su da wani abu da suke nema ido rufe, wanda ni kuma ina da shi, na san daga nan za ki dawo cikin hayyacinki." Wulaƙantaccen kallo na bi shi da shi, ina keɓe fuska kamar na ga kashi na ce. "Har akwai wani abu da talaka yake da shi da mai arziƙi zai rasa? Ai kuɗi babu abin da ba sa samar wa mutum a duniya." Girgiza kai ya yi ya ce. "Kamar yadda Ubangiji yake raba arziƙi ga wanda ya so haka yake raba lafiya da sauran baiwa ga bayinsa, don ka na da kuɗi bai zama lallai ka na da lafiya ko kuma wani abu mai muhimmanci a rayuwarka ba, na san ba za ki taɓa gane duk wani abu da zan faɗa miki ba a yanzu, balle ki yarda da ni, saboda nausawar da kika yi a cikin wani tunani na banza da wofi. Shi ya sa na tattara ki na watsar na zuba miki ido ki yi duk abin da za ki yi ki gama, zan dai ci gaba da yi miki addu'ar Ubangiji ya ganar da ke cikin gaggawa." Wawan tsaki na ja tare da galla masa harara, ina jin kamar na kikkifa masa mari. Bai ko kalle ni ba ya ɗauki abin da zai ɗauka ya fice. Rashin sanin abin yi ya sa na tafi inda na ajiye kayan da Maman Nasmah ta ba ni don na ɗauka na tasa su a gaba na kalla kamar yadda nake yi kullum ko zan ji sanyi a raina. Sai dai me? Neman duniya babu wanda ban yi ba amma babu su babu alamar su, gabaɗaya na ƙara hargitsa ɗakin, na yi wa komai filla-filla, amma ko alamar abu mai kama da su ban gani ba. A haukace na fita parlour ina sharce zufa na duba amma nan ma babu, kitchen, toilet, ɗakin su Sultan, soro babu inda ban duba ba amma ban gan su ba, har bokitin da nake zuba shara sai da na zazzage a ƙasa na duba. Amma kaya suka ce ɗauke mu inda kika ajiye....✍️
Chapter 17 · 0% Book details