Sashe 43
Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Yaye mayafin fuskata na yi ina murmushi na shiga bin ɗakin da nake da kallo. A hankali na miƙe na fara shafa ƙaton gadon da duk girman shi a ɗan gefen ɗakin yake. Daga baya na koma gurin wardrobe da madubi, na daɗe a tsaye kafin na fita ƙaton parlour'n da ya ji komai na more rayuwa. Wani tsalle na doka cikin tsananin farinciki, yau ni ce a gidan da nake mafarkin kasancewa a cikinsa matsayin mallakina? Tsabar zumuɗi har wani irin tsiko nake jin jikina yana mun. Ɗayan bedroom ɗin da ke manne da wanda na fito na shiga, shi ma kamar shi yake a komai da komai, banbancinsu kawai kowanne furnitures da kalar shi. Ban wani jima ba na fita, ƙofar da na gani tana facing ɗina na shiga, haɗaɗɗen dinning area na yi tozali da shi. Cike da ƙauyanci na je na fara tattaɓa abubuwan ina sunbatu ni kaɗai. Daga nan da na fita hawa na biyu na sauka, shi kuma ƙaton parlour ne kawai da ya ji komai, sai kitchen da toilet a cikinsa. Sai da na leƙa ko'ina sannan na sauka ƙasa. Shi kuma kamar hawa na uku yake, parlour, da two bedrooms kowanne da toilet a cikinsa, sai kitchen da dinning area. Gabaɗaya komai na gidan sabo ne, ko'ina kuma kalarsa daban. Ta window na leƙa na hango wasu apartments ɗin daban daga can nesa, amma duk da ban je na gani ba na san wanda nake ciki duk ya fi su girma. Sai da na gama kalle-kallen nawa zan koma can saman na ga wata ƙofar daban ta cikin parlour'n, da sauri na je na buɗe, sai na ga wani parlourn ne daban shi ma, mai kyau amma bai kai sauran girma ba, da toilet a cikinsa. Ban jima ba na koma saboda kar Ango ya shigo ya tarar da ni a ji kunya. Bayan na zauna na ɗauko jakata na ɗauki wayata na duba time, sai na ga ƙarfe goma na dare ma ta wuce. Cikin mamakin abin da ya hana Mansur zuwa har lokacin na kira shi. Har missed call uku na yi masa amma bai ɗauka ba. Ban kawo komai a raina ba na ci gaba da santin gidana, sai wajen 11 na tuna ko sallar Magriba ban yi ba. Da sauri na miƙe na shiga haɗaɗɗen toilet ɗin ɗakin don ɗauro alwala, da ƙyar na iya kunna fanfo na yi na fito. Bayan na idar na ciro sabbin wayoyina daga kwali na jona su a chaji. Tsohuwar kuma hoton shi na lalubo na shiga kalla don ya ɗebe mini kewa. Abin da ya fi burge ni da shi yadda bai taɓa kyara ta ko nuna mini ƙyama ba kasancewata talaka, da kuma tunda muke da shi bai taɓa yi mini maganar banza ba, duk da ya san ni bazawara ce, kamar yadda aka ce wasu mazan suna yi ko da auren mace za su yi. Hakan ya ƙara mini ganin girman da darajar shi, na tabbatar so na tsakani da Allah yake yi mini. Har sha biyu ta wuce ina zaune a gurin, zuwa lokacin na fara fargabar ko ba lafiya ba? Yadda ya nuna mini ya matsu a kawo masa ni, amma fiye da awa biyar da kawo nin babu shi babu dalilin shi, sannan ina ta kiran shi bai ɗauka ba, shi kuma bai kira ni ko ya yi mini text ya sanar mini abin da yake faruwa ba. Sai da gyangyaɗi ya fara ɗiba ta sannan na tashi na koma kan gadon na kwanta, gabana na dukan tara-tara. Tun ina ɗaukar abin wasa har na ga ya wuce hankali ganin har 2 bai shigo ba. Na dinga kiran shi da tura masa text amma shiru. Duk da tarin gajiyar da ke addaba ta amma sai na kasa bacci, sai wajen asuba wani wahalallen bacci ya kwashe ni, wanda cikinsa na dinga mafarkai wai wani mugun abin ne ya samu mijina. A firgice na farka ina faɗin. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Gabaɗayana na yi sharkaf da gumi. Jin kamar ana buga ƙofar ɗakin ya sa na tashi sauri na je na buɗe, cikin raina ina addu'ar Allah ya sa shi ne. Saɓanin abin da na yi zato na tarar, wata yarinya ce tsaye a bakin ƙofar, kanta a ƙasa ta ce. "Ina kwana Hajiya?" Ina zazzare ido na ce. "Lafiya ƙalau." Cike da ladabi ta ce. "Mu ne masu aikinki da alhaji ya ce a samo, sauran suna ƙasa, mun kammala abin kari ne na ce bari na zo na sanar miki." Kallon ta na yi na gan ta a tsabtace take babu ƙazanta a tattare da ita, numfashi na sauke na ce. "Ok, a cikin gidan nan kuka kwana ne?" Ta ce. "A'a yau muka zo, amma maigadi ya nuna mana ɓangarenmu da za mu dinga kwana mun kai kayanmu can." Gyaɗa kai na yi na ce. "Ya sunanki?" Ta ce. "Laure." Na ce. "To sannun ki, je ki na gode." Har ta juya na kira ta, ta dawo tare da rusunawa, umarni na ba ta akan ta kira mini maigadin.
Sai da na yi sallar asuba don lokacin kusan goma saura sannan na sauka ƙasan, na tarar da shi zaune akan carpet. Kamar zai yi sujjada saboda duƙawa ya ce. "Barka da fitowa ranki ya daɗe." Hakan ya fasa mini kai, na zauna a kan kujera tare da harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya. Ban amsa masa ba na ce. "Maigidan nan ya shigo jiya ne?" Ya ce. "A'a, ai da ma ya sanar mini ba zai kwana a gidan ba, wani uzuri ne ya tasar masa ya yi ƴar tafiya, amma ba zai jima ba zai dawo, na ɗauka ya sanar miki ne ma." Ajiyar zuciya na sauke jin yana lafiya ƙalau, amma me ya sa ni bai faɗa mini zai yi tafiya ba? Kuma wanne irin uzuri ne da har ya fi kasancewarmu a daren farkon aurenmu muhimmanci? Ya zaɓi ya je ya yi shi, ni kuma ya bar ni na kwana ni kaɗai ƙwallin ƙwal, babu waya babu komai? Rashin mai ba ni amsa ya sa na sallami maigadin. Hankalina ya ɗan kwanta da na ji lafiya lau yake, hakan ya sa na saka masu aiki suka kawo mini abinci na karya. Bayan na gama suka kwashe kayan. Wajen sha biyu na yi wanka na shirya na fita harabar gidan don ba wa idona abinci, duk yadda na dinga ganin girman gidan Maman Nasmah da na Aunty Billy wannan ya fi shi, don kafin na gama zagaye shi sai da ƙafafuna suka yi liƙis da gajiya. Part ɗin masu aiki maza daban na mata daban, ɗakin gateman da toilet ɗinsa shi ma daban, sai wasu extra parts guda biyu. Ga swimming pool da garden mai kyau da ya ƙawatu.
Har bayan azhar ina ta kiran layin Idonnera ba ya É—auka, tun ina yi masa uzuri har abun ya fara damu na, don abincin rana ma kasa cin shi na yi. Duk tasirin farinciki da murnar kasancewa ta a gidan da na daÉ—e ina mafarkin kasancewa a cikinsa sai na neme su na rasa. Na ji mijina kawai nake son gani mu sha soyayya, ya ba ni dukkanin kulawar da ya ce ya tanadar mini.
Da yamma Inna ta aiko wasu ƴan'uwanmu da kayan lefena, suka zo suka dinga kwakwazo da zuzuta gidana gami da santi. Ban bari sun gane halin da nake ciki ba, da suka tambaye ni ina angon na ce musu bai jima da fita ba. Sun yi abinci sun yi nak, amma da za su tafi har da ƙara yin gurin shi, saboda sun gan shi available. A cikin kuɗin hannuna na ba su 10k, na saka ɗaya daga cikin driver's ɗin ya mayar da su gida. Har raba ban iya cin abinci ba. Na dinga tambayar kaina wacce irin amarya ce ni? Har na kwana na wuni ko muryar ango ban ji ba bare na saka shi a idona. Ga shi ina ta kiran Maman Nasmah layinta ba ya tafiya ita ma. Na hau online na yi mata magana not respond, ban ga ma alamar ta hau ba har na gaji na sauka. Daren yau ko rintsawa ban yi ba. Washegari ana yin Sallah na kasa haƙuri na kira mai gadi, na ce masa anya lafiya kuwa Alhaji yake? Amsar da ya ba ni ce ta kusa saka ni suman tsaye, wai ƙalau yake, ai da ma ko kwana biyu ba ya yi a ƙasar nan, idan ya tafi kuma yana yin watanni, amma tunda da ni yanzu may be ya daina daɗewa. Duk da haka ban ji hankalina ya kwanta hundred percent ba, don a soyayyar da ya nuna mini da zumuɗin kasancewa da ni na san ba ƙaramin abu ne ya hana shi zuwa gare ni ba. Haƙuri na ba wa kaina tare da yi masa uzurin wani babban abin ne ya riƙe shi. A ranar na mayar da komai nawa kan sabuwar wayata, na yi videon gidana da abincin da masu aiki suka girka na tura a group ɗinmu, na ce ga shi a saka mini albarka mun tashi mun koma sabon gida. Ai kuwa na ga ruwan comments kamar yadda nake burin gani a baya.
Zan wuni a kwance ina kallo ko chatting, ga masu aiki za su yi mini komai, ga ƙaton gida da kayan alatu, ga ishashshen kuɗi a hannu da account ɗina, zan saka datar ko nawa nake so na shiga social media na yi kalle-kallena, ga abinci sai wanda na zaɓa zan ci, nama cikin freezer, drinks kala-kala a cikin fridge, zan yi video a background mai kyau na saka a status, mutane sui ta wow wow, amma rashin miji da rashin sanin halin da yake ciki ya sa na kasa farinciki da walwala. Duk yadda na zo tanƙwara zuciyata ta kasance a cikin nishaɗin samun abin da take da buri amma abu ya gagara. A haka har na yi sati da tarewa. Wani abu da ya ƙara ɗaure mini kai babu wanda ya zo ya ce yau shi ɗan'uwan maigidan ne, daga ni sai masu aiki muke rayuwa. Ga Maman Nasmah ita ma har lokacin wayarta ba ta shiga, kuma ba ta hawa online. Har yunƙurin zuwa gidanta na yi, amma rashin address da kuma ba zan gane ba ya saka na fasa, don duk zuwan da na yi masu napep kawai nake nunawa address ɗin su kai ni, yanzu kuma ban da wanda ta turo mini, don tun a waccar tsohuwar wayar tawa ne. Ga shi ban san sunan mijinta ba, bare na faɗawa wani a cikin ma'aikatan gidan ya kai ni, tunda abokin Mansur ne ba za su kasa sani ba.