← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 54

Sashe 16

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau Anas ko fita bai yi ba, takaici da mamakin Hafsah sun saka ya zauna yay ta tunane-tunane, hakan ya haifar masa da ciwon kai. Bai taɓa zaton zai ce wa Hafsah idan ta yi abu a bakin aurenta za ta aikata ba. Shi ya dafa musu abincin rana ya yi sauran aikace-aikacen gidan. Sai bayan Magriba na koma gida, na tarar ba ya nan sai su Sultan kaɗai a parlour suna homework. Da gudu suka taso suka rungume ni, Sufyan ya ce. "Mami ina kika je? Muna ta neman ki, kin tafi kin bar mu." Kayan hannuna wanda Maman Nasmah ta aiko mini da shi na ajiye a kan kujera na ce. "Unguwa na je, ku ƙarasa aikin naku na ba ku kayan daɗi." Da murna ya koma ya ci gaba. Sultan ya ce. "Mami na zubo miki abinci? Abba ya dafa mana macaroni." Na ce. "To bari na shiga na ajiye kayan nan na fito." Sufyan ya ce. "Za ki biya mana karatu yau ko Mami? Idan mun iya ki yi mana tatsuniya irin na ranar nan." Na ce. "To." Kawai. Sai da na yi Sallah sannan na baje kayan na dudduba, duk abin da ta lissafa za ta ba ni babu wanda ta manta ba ta sako ba, har da kuɗi 30k wai na transport zuwa gidan gyaran jiki, kuma ta ce gobe na tafi da atamfata za ta aiko a karɓa akai mini ɗinki. Ina ɗaga sarƙar gold ɗin da na shafe mintuna ina lailaya ta na ce. "Allah ka saka wa wannan mata da alkhairi, ka ba ni ikon faranta mata kamar yadda ta faranta mini a yau." Kamar zan zauce haka nake ji tsabar farinciki, na ƙara tabbatarwa Maman Nasmah masoyiyata ce ta haƙiƙa, don ta gama yi mini komai, tunda ta fitar da ni kunyar zuwa taron nan. Sai da na gama tsallena da rawar murnar daɗi na kira ta don na yi mata godiya, har lokacin kuma Anas bai dawo ba. Bayan mun gaisa ta ce. "Ya aka yi ya bar ki kika je kuma?" Ina murmushi na ce. "Shawararki na bi ai, na nuna masa bai isa ba, shi ne har da cewa idan na fita a bakin aure na." Maman Nasmah ta ce. "Gara da kika yi masa haka, ki ci gaba da ƙwatar wa kanki ƴanci, kar ki bari takaicin Namiji ya kar ki, namijin ma wani banza talaka da ko ɗawainiyarki bai gama iya ɗaukewa." Shiru na yi don ba na jin daɗin yadda take yawan zagin Anas da aibata shi, duk da wani lokacin idan na yi nazari gaskiya ta faɗa, amma mijina ne duk lalacewar shi, kuma ina son shi a haka. "To da kika dawo me ya ce kuma?" Ta katse shirun nawa da faɗar haka. Na ce. "Ba ya nan na dawo, har yanzu kuma bai dawo ba." Ta ce. "To kar dai ki raga masa, ni shawara nake ba ki wadda za ta fishshe ki, don so nake na ga kina rayuwa mai inganci, idan ya faɗa miki ɗaya ki mayar masa da goma zafafa, kar ki ƙara yarda ki kuma irin rayuwar bayan da kuka yi da shi, wani ladabi da biyayya duk ki zubar da su a gefe, ki daina wannan aikin wahalar da na zo na tarar da ke kina yi kin yi ciɗin-ciɗin kamar wadda aka haƙo daga rami, yadda kika ga na zo gidanki haka nake zama kodayaushe a gidana, ina daga kwance masu aiki ne suke yi mini komai. To akan me zan kashe kaina? Haka kawai na yi baƙi watarana su gan ni a ƙazance, ai abin kunya ne." Na ce. "Haka ne, na gode sosai, zan yi duk yadda kika ce." Daga haka muka yi sallama na katse wayar. Kayan ciye-ciyen da ta kawo jiya shi muka ci ni da su Sultan, na yi musu wanka na kwantar da su, sai murna suke yau na ja su a jiki kamar yadda muka saba a da. Har wajen sha ɗaya Anas bai dawo ba, har na kwanta na ji na kasa bacci, don ba ya taɓa kaiwa haka a waje, bare kuma ya fita ba na nan ya bar yara kaɗai a gidan. Ina ƙoƙarin kiran shi a waya ya shigo. Kamar babu abin da ya faru na ɓacin rai a tsakaninmu kafin na fita haka ya mun magana, ya sanar mini jiran shagon dare ya yi wa mai gidansu tunda bai samu ya yi na rana ba. Ganin haka na nuna masa kayan da Maman Nasmah ta ba ni, amma ban da sarƙar gold ɗin, saboda kar ya yi magana. Bai nuna ɓacin ransa ba ya ce Allah ya sanya alkhairi. Na yi mamakin shi sosai, don na ɗauka zai yi mini bala'i ne. Washegari da na ce masa zan koma gidan gyaran jikin bai hana ni ba, ya dai roƙe ni akan kar na yi dare irin na jiya, na ce masa in sha Allah. Sai da na yi abincin rana na kai maƙota da uniform ɗin islamiyyar su Sultan sannan na tafi. Tun ƙarfe bakwai na ga Maman Nasmah tana ta kira na, amma saboda aiki ban samu sukunin kiran ta ba, sai da na hau napep. Ta na ɗagawa ta ce. "Ya kuka yi da faƙirin mijin naki? Shi nake ta kiran ki na ji amma ba ki ɗauka ba." Cikin mamakin yadda yanzu kullum muka yi waya ko chat sai ta ji me yake wakana tsakani na da Anas na ce. "Me ya sa kika damu ne?" Ta ce. "Saboda ina son na ji halin da kike ciki mana na ba ki shawarar da za ta fishshe ki, ni fa tamkar ƙanwata da muke ciki ɗaya haka na ɗauke ki, kullum da ke kwana nake tashi, wannan mulkin mallakar da yake yi miki ji nake kamar ni ake wa wallahi." Cikin jin daɗi da ƙara yarda da soyayyar ta a gare ni na ce. "Allah Sarki ƙawata, to ki kwantar da hankalinki, don komai ya wuce a tsakaninmu ni da shi, ba ki ga yadda ya mun jiya ba, faran-faran, yau ma tare muka fito, bai hana ni ba." Kamar wadda ta firgita haka na ji ta yi magana da faɗin. "Ban gane ba! Bai ce miki komai akan daɗewar da kika yi ba?" Na ce. "Bai ce ba, kawai dai ya ce kar na daɗe yau." "Kuma kin nuna masa kayan da na ba ki?" Na ce. "Eh." Shiru na ji ta yi na wasu sakanni, daga baya ta ce. "Kin ga shawarar da nake ba ki ta yi aiki ko? Da kin ci gaba da yi masa lako-lakon nan da tuni jiya ya ƙare miki tijara, amma abin da nake so da ke kar hakan ya sa ki koma masa kamar da fa, idan ba haka ba zai ci gaba da juya ki kamar waina ne, yanzu kin saka masa tsoron ki a cikin zuciya, ya gane ko babu shi za ki iya rayuwa, tunda har ya yi miki barazana da saki kuma kika shallake, to haka ake yi wa maza a zauna lafiya da su, idan kuma kika ce za ki raga musu sai su mayar da ke baiwa, dabba ma ta fi ki daraja a gurinsu." Cikin gamsuwa da maganganunta na ce. "Tabbas haka ne, don da a da ne Anas ya hana ni abu na yi sai ya saɓa mini sosai, amma jiya har da haƙuri ya ba ni, ai na faɗa miki yana tsananin so na, ba zai taɓa iya rabuwa da ni ba." "Yawwa, to ki yi amfani da wannan son ki gara shi kamar taya, ke ma ki shigo samun mu manyan mata isassu a gidajensu, za ki ga yadda zai na rawar jiki a kanki da yi miki biyayya." Bayan mun gama wayar na yi shiru ina nazartar maganganun ta, tabbas duk abin da ta faɗa gaskiya ne, na yi kuma amanna da su, duk da na yi niyyar mu koma kamar yadda muke a da ni da Anas, don da ma dalilin da ya saka nake yi masa duk wani rashin mutunci saboda ba zai fitar da ni kunya ba ne, amma tunda na samu duk wani abu da nake buƙata na fitar taronmu ban da wata sauran damuwa. Kasa zaune ko tsaye Maman Nasmah ta yi bayan sun gama wayar, ko kaɗan ba haka ta so ji ba, ta so a ce Anas ya na dawowa ya yi wa Hafsah fata-fata ya kore ta a daren, hakan ya ƙara tabbatar mata ba ƙaramin so yake yi wa Hafsan ba kamar yadda ta faɗa. Dole ne ta ƙara ƙaimi da dagewa gurin ziga Hafsah da nuna mata mijinta ba kowa ba ne face talaka mara daraja, za ta yi amfani da son rayuwar kuɗin da Hafsah take da shi ta cimma burinta. Wani murmushi ta saki lokacin da wata idea ta to mata cikin kwanyarta kamar an zira mata ita. A fili ta ce. "Duk rintsi duk wahala dole na mallaki mijinki Maman Sultan!" Da daddare da muka kuma waya da Maman Nasmah ta ce na takura wa Anas ya siya mini sabuwar waya kafin ranar taro, kowa yana turo abin da mijinsa ya yi masa a group amma ban da ni, saboda nawa mijin ya fi kowa fatara sai ya kasa tsinana mini komai. Ya na dawowa ko bari ban yi ya zauna ba na ce. "Abban Sultan taron da na ce maka za mu yi fa saura kwana biyar, kuma gaskiya ni ina buƙatar sabuwar waya kafin ranar." Ya ce. "Ba mun gama wannan maganar ba Hafsah?" A harzuƙe na ce. "Ba wani mun gama, ni kawai ka siya mini." Ya ce. "Zancen kike so." Masifa na shiga surfa masa kamar wata uwarsa, ta inda nake shiga ba ta nan nake fita ba. Na dinga jifan shi da kausasan kalamai. Bai ce mini ƙala ba har na gaji don kaina na yi shiru ina huci. Ina hawa online a lokacin na ga an ci gaba da turo abubuwa, kowacce ta na cewa mijinta ya siya mata kaza, ya ba ta kaza, ya kawo mata kaza. Hakan ya ƙara tunzura ni, na dinga Allah wadai da auren Anas, don da na san haka masu kuɗi suke bauta wa matansu da
Chapter 16 · 0% Book details