← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 54

Sashe 37

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da Hafsah suka shiga cikin gida Kawu ya nisa a cikin tunani, ya kasa yarda Anas ne da wannan ɗanyen aikin, tunda Hafsah ta ce masa asiri aka yi masa amma yana tantama. Hakan ya sa ya janyo ƴar wayarsa ya lalubo numbern Anas ɗin ya kira, sai dai ba ta shiga aka sanar masa a kashe take. Ya kira ya fi sau goma, daga baya ya haƙura ya ajiye wayar, a ransa yana faɗin. 'Allah ya kyauta.' Ina zaune wajen goma Gwaggo ta shigo ta ce. "Ki taso ga wanke-wanke can ki yi da sharar tsakar gida, kuma gidan babu abin kari tunda uban naki ba ya fita yake yi ya nemo ba, sai dai ki fitar da kuɗinki ki siya." Ɓata fuska na yi na ce. "To." A shaƙe. Ina gungunin daga zuwa na za a fara takura mini na tashi na fitar tsakar gidan da ya yi buɗuɗu da ƙura da ledodi. Da ma kafin na yi aure ni nake komai na gidan, saboda Gwaggo irin matan nan ne masu mugun son jiki, ba ta son motsa jikinta ko kaɗan, ta fi son kullum tai ta jibgewa kamar kayan wanki. Ina toshe hanci saboda ƙura na share tsakar gidan da wata ficiciyar tsintsiya da ta sagar mini da hannu. Bayan na gama na wanke toilet, masan gargajiya ce kuma ta cika ta yi hani'an kamar kashin ciki zai fara malala, ga shi a buɗe take fayau babu ko ɗan murfi. Ina gamawa na dinga kwara amai, saboda ƙyanƙyami da uban warin da na shaƙa. Kallo na kawai Gwaggo take ta na taɓe baki, ba sannu bare na gode. A ranar na ce wa Kawu a samo masu kwasar masai su kwashe zan biya, don ba zan iya rayuwa da wannan toilet ɗin ba. Ya dinga saka mini albarka tare da tarin addu'oi. Saboda kullum da takaicin lalacewar banɗakin yake kwana yake tashi, ba shi da halin gyarawa ne kawai ya saka bai gyara tuntuni ba. Amma sai da ya tambaye ni ina na samu kuɗin? Bayan na ce har abinci Anas daina ba ni ya yi. Ƙarya na yi masa na ce wani abu na siyar a cikin kayan ɗakina, sai jiya aka kawo mun kuɗin na taho da shi. Washegari da safe na je na kwaso barguna da zanin gado saboda shimfiɗa, don ba zan iya kwanan kan tabarma zalla ba. Daga yadda na ga gidan na gane bai dawo ba tun fitar da ya yi, tabbacin ƙauyen ya tafi kenan. Haka rayuwa ta ci gaba da garawa, kwata-kwata bana jin daɗin zaman gidan Kawu saboda Gwaggo, ga shi komai ni nake yi da kuɗina, hakan ya sa duk kuɗaɗen hannuna suka ƙare karaf. Yau da safe bayan na gama duka aikin gidan da tulliƙar wankin kayan Gwaggo na je soro gurin Kawu. Bayan mun gaisa na marairace na ce. "Kawu ina son zuwa asibiti anjima, kwana biyu ciwon kai da na ƙirji ya dame ni." Cikin jimantawa ya ce. "Subhanallahi! Hansatu kar ki bari damuwa ta saka miki wani ciwon fa, ki yi haƙuri ki daure ki fawwala wa Allah komai, na san abin da ciwo, kuma dole ki damu ko don ƴaƴanki da ba sa gabanki." Hawayen ƙarya na fara ban ce komai ba, ya dinga yi mini nasiha sannan ya ce na tashi na tafi. Cikin farinciki da murna na shirya na fita. Direct gidan wata dilalliya a unguwarmu na je, na faɗa mata ina son zan siyar da kayana. Ta ce mu je ta gan su. Bayan ta gani ta yi musu kuɗi, ban tsaya ciniki ba na ce ta bayar kawai duk da tayin wulaƙanci ta yi musu, ga shi kuma sun sha jiki da ma kuɗin ba na kirki ba ne. Rabin kuɗin ta ba ni ta ce za ta cika sauran daga baya. Gidan gabaɗaya ya yi ƙura ya fice daga hayyacinsa, na dinga tambayar kaina ni kaɗai ina Anas ya tafi da har yanzu bai dawo ba? Ina ya kai mini su Sultan da kewar su take ta damu na? Rashin amsa ya saka ni taɓe bakina, na ci gaba da sabgogina. Har katifata na siyar, saboda babu amfanin da za ta mun, tunda wanda zan aura yana da arziƙi shi zai yi komai kamar yadda Maman Nasmah ta faɗa. Kawu kuma da ma na riga na yi masa ƙaryar na siyar komai nawa. Sai yamma lis na koma gida cikin farincikin samun ƴan kuɗaɗe. Sai dai kuɗin ba su fi sati ba suka ƙare, ciyar da kai da su labulun wanka da na wanki ba wasa ba ne. Ƙara komawa gidana na yi na tsitstsinci wasu abubuwan na ƙara siyarwa. Wasa farin girki, kafin na gama idda sai da na siyar da kusan komai nawa, kayan sakawa da ɗan abin da ba za a rasa ba ne kawai suka yi saura. Ƙarshe har wayar hannuna na siyar na siya wata ba kamfanin iphone ba, shi ne ma na ɗan samu kuɗi masu tsoka a hannuna. Yau Juma'a, wadda ta yi daidai da gama iddata. Cikin tsananin farinciki na tashi ina jin zuciyata fes kamar an yi mini bushara da gidan aljanna. Kafin Kawu ya fita soro ya janyo ƙafa ya zo ƙofar ɗakina ya ce. "Hansatu yau lafiya ba ki fito ba har yanzu?" Na ce. "Lafiya ƙalau Kawu, ina kwana?" Ya ce. "Lafiya lau, yau kin kammala idda ko?" Na ce. "Eh, kwana ɗari ba goma ya tabbata." Cikin jimami ya ce. "Kullum da lamarin nan nake kwana nake tashi, har yanzu zuciyata rawa take yi, gani nake kamar mafarki nake zan farka. Ga shi ina ta kiran shi Anas ba na samun shi, bare na roƙe shi ya taimaka ko da sau ɗaya ne ya kawo miki yaranki ki gan su, raba uwa da ɗa ba daɗi." Ban ce komai ba na fara sheshsheƙar ƙarya, irin abin yana damuwa ɗin nan sosai. Cikin tausayawa ya ce. "Ki ci gaba da haƙuri ki ta addu'a, in sha Allah hakan alkhairi ne, Allah ya kawo miki wani mijin na gari wanda ya fi shi." Ina jan hanci na ce. "Ai ni Kawu ba zan sake wani auren ba, a haka zan ta zama, na haƙura, saboda ban san ƙalubalen ƙara fuskanta ba a cikinsa." Da sauri ya ce. "Ashsha! Kar ki ce haka, ai komai ya faru da bawa da sanin Ubangiji, za ki ji daɗi ki yi farinciki a gaba in dai ba ki da haƙƙin shi. Ke dai ki ta addu'a kawai, amma kar ki kuma faɗar haka." Na ce. "To Kawu." Bayan ya tafi na kira Maman Nasmah, bayan mun gaisa na ce. "Yau Allah ya yi aure da mara kwabo, na kammala idda, da ma a addinance tun last week na yi jini uku na gama, na bari na cikashe kwanakin ne saboda lissafin mutane." Ta ce. "Bar kan ki, na taya ki murna." Na ce. "Bari ke dai, ya maganarmu?" Ta ce. "Hmm, abu fa ya lalace." Cikin faɗuwar gaba na ce. "Ban gane ba!" Ta ce. "Hmm, ashe tuntuni Alhaji Kyauta ya gaji da jira ya yi auren shi, yanzu haka suna can honeymoon ma shi da amaryar tasa." Wani irin jiri na ji yana kwasa ta daga zaunen da nake. Cikin matuƙar razani gami da firgici na ce. "Na shiga uku! Yanzu sai da na kashe auren nawa shi kuma zai ce a'a, da can me ya sa bai faɗa ba?" Cikin son kwantar mini da hankali ta ce. "Mene abin damuwa to?" Kamar zan fashe da kuka na ce. "Akwai mana, don Allah ki roƙe shi ko a ta uku ne ya daure ya aure ni, wallahi ko kaɗan ba na jin daɗin zaman gidan nan namu, ga yarana ina son na ɗauko su." Ta ce. "Ai kin fi ƙarfin zama da kishiyoyi biyu, ɗayar ma a plan ɗina kina shiga za ki fitar da ita. Rasa Alhaji Kyauta ba abin ɗaga hankali ba ne, maza masu kuɗi hamshaƙai suna nan da yawa a duniya, akwai wani abokin mijina matarsa ta rasu last year, yana ta damu na, na samo masa mata amma na mayar da abun wasa, har yanzu kuma bai yi aure ba. Don haka yanzu sai na haɗa ku, don ko shekaran jiya ma ya yi mini maganar, ba shi da matsala ko kaɗan, kuma yana da bala'in kuɗi." "Ya kai mijin Aunty Billy?" Na katse ta da faɗin haka. Tsaki ta ja ta ce. "Ya ma fi shi, ki bari na haɗa ku za ki gasgasta ni, yanzu zan tura masa hotunki da lambarki, ke ma na tura miki nasa." Cikin zumuɗi na ce. "Na ji daɗi amma, gaskiya ban san da bakin da zan gode miki ba, kin gama yi mini komai a duniyar nan." Murmushi ta yi mai sauti ta ce. "Kar ki damu ƙawata, matuƙar ina raye ba za ki taɓa zubar da hawaye ba. Abin da ba ki sani ba ma, wallahi ko mijina ne zan bar miki ki aure shi, ni dai ki yi farinciki kawai shi ne burina." Cikin mamaki na zaro ido kamar tana gabana tare da faɗin. "Mijinki fa kika ce?" Ta ce. "Eh, mene ne a ciki, kin wuce haka a gurina ai, kuma kar ki ji zancen wasa, ko a yanzu kika ce kina son shi wallahi za ki aure shi, idan kuma ba ki yarda ba ki gwada ki gani." Jinjina kai na yi na ce. "A'a, ko a mafarki ba zan taɓa auren mijinki ba har abada, mu ma bar wannan maganar." Dariya ta yi ta ce. "Kin ji an ɗaga taro sai bayan Sallah ko? Saboda azumi ya ƙarato." Na ce. "Eh, ai na ji daɗin haka, saboda kafin lokacin in sha Allah ina gidana na alfarma." Ta ce. "Ko tantama babu tawan." Mun daɗe muna tattaunawa akan yadda abubuwa za su wakana sannan muka yi sallama, zuciyata cike da so da ƙaunar Maman Nasmah, tamkar ƴar'uwata da muka fito ciki ɗaya haka nake jin ta, tunda da za ta iya sadaukar da komai nata saboda ni. Bayan na gama duka ayyukan gidan saboda sababin Gwaggo na yi wanka, ina shiryawa na ji ƙarar shigowar message. Da sauri na janyo wayar na duba, don a zatona lambar mutumin Maman Nasmah ta
Chapter 37 · 0% Book details