Sashe 29
Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*Zeey Kumurya*
[3/8, 1:40 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*15.*
Namiji na gani, saɓanin abin da mai napep ɗin ya ce mini. A fusace na juya na koma na ce masa. "Ka ce mata ne, ya kuma na ga maza?" Ya ce. "Ki yi haƙuri, na yi musu alƙawarin zan fito da ke ne, shi ya sa na ce miki mata ne, don na san idan na ce maza ne bai zama lallai ki je ba." Tsaki na ja na ce. "Matar aure ce fa ni! Idan matarka ce za ka so wasu su tare ta?" Cikin lallami ya ce. "Ki yi haƙuri don Allah, idan ba hakan ba na yi na san ba za su taɓa daina bin mu ba, ki je sai ki yi musu bayani, na san za su ƙyale ki." Numfashi na sauke tare da dafe kaina na koma, kaina a ƙasa na ƙarasa inda mutumin yake na ce. "Ga ni Malam ya aka yi?" Murmushi ya yi mai sauti ya ce. "Sannu ƴan mata." Da sauri na ɗago don jin kamar na san shi, kallon tsaf na yi masa, lokaci ɗaya ƙwaƙwalwarta ta tuno mini shi, mijin Aunty Billy ne. Cikin mamaki na ce. "Alhaji! Lafiya?"
"Lafiya ƙalau mai inganci ma kuwa." Ya faɗa yana murmushi tare da bi na da wani irin kallo.
Ajiyar zuciya na sauke ban ce komai ba, ina jira na ji ya ce matarsa ce ta aiko shi, sai na ji ya ce. "Ban san yanzu za ki tafi ba ai da na fito da ke na kai ki gida, don zaman da na yi jiran nake ku tashi daga taron na mayar da ke gida da kaina." Murmushin ƙarfin hali na yi na ce. "Babu komai ma ai Alhaji, na gode." Ya ce. "To mu je mu sauke ki ko? Sai mu ƙarasa tattaunawa a cikin motar." Cikin ɗaurewar kai na ce. "Tattauanawa kuma akan me? Na ɗauka ai Aunty Billy ce ta ba ka saƙo ka kawo mini?" Yana gyara tsayuwarsa ya ce. "Saƙon kaina ne ya kawo ni ba na Bilki ba, hasalima ba ta san zan biyo ki ba." Waro ido na yi kawai don na rasa abin cewa. Ci gaba da magana ya yi da faɗin. "Tunda kuka shigo na yi tozali da ke gabaɗaya na rasa sukuni, kuna fita na kira ɗaya daga cikin yarana na gidan na yi masa kwatancenki na ce ya sa mini ido a kanki, shi ya sanar mini da fitarki yanzu, a gaggauce na biyo bayanki don kar ki tsere mini, Allah ya taimake ni muna fitowa na ga lokacin da kike hawa napep, shi ne muka biyo bayanku." Cikin ruɗewa don ba gama fahimtar abin da yake nufi na yi ba na ce. "Akan me to? Ni fa matar aure ce." Murmushi ya kuma yi ya ce. "Wannan ba matsala ba ce, kawai yardarki nake nema, sai mu dinga komai a sirrance. Zan wadata ki da kuɗi, na siya miki motar hawa duk irin wacce kike so, sannan zan dinga yi miki komai da kike buƙata, matuƙar kika amince da ni." A gigice na ce. "Wacce irin mu'amala za mu yi alhalin ina matar aure? Ka fahimtar da ni har yanzu ban gane mai kake nufi ba."
"Calm down Baby, na ga duk kin ruɗe, ba wani abin wahala ba ne ba fa, kawai na gan ki na ji kin mun ne, kin tafi da hankalina sosai da ba zan iya haƙura da ke ba. So I decided kawai duk lokacin da nake gari zan kira ki sai mu haɗu a hotel, mu yi some hours na sallame ki, ki wuce gida, ba kwana za ki dinga yi ba tunda kin ce kina da aure." Wani jiri na ji yana kwasa ta, don duk da bai fito ƙarara ya bayyana mini ba, na gane me yake nufi. Kallon shi kawai na tsaya ina yi, ga shi dai mutum har mutum cikin kaya na kamala amma bai da halin arziƙi ashe. Girgiza kai na yi na ce. "Ba haka nake ba Alhaji, kuma gaskiya ba zan iya abin da kake nufi ba." Murmushi ya yi bai ce komai ba ya zaro wani kati ya miƙo mini tare da faɗin. "Ba zan tursasa miki sai kin amince a yanzu ba, amma ga card ɗina nan, ki je ki yi shawara, abin da kika yanke sai ki kira ni ki sanar mini. Ki ba ni account number ɗinki yanzu na saka miki 1 million ki saka kati." Zaro na yi tare da girgiza kaina, ba tare da na karɓi card ɗin ba na ce. "Ban da account." Daga haka na juya cikin sauri na shige napep ɗin tare da baiwa direban umarnin ya ja mu tafi." Bai yi musu ba ya kunna ya ja muka bar gurin. Har muka je gida zuciyata bugawa take, gabaɗaya kaina ya kulle, mamaki da al'ajabin mijin Aunty Billy sun suka kashe ni. Gefe guda kuma ina ta jinjina million ɗayan da ya ce zai ba ni wai kawai na saka kati da ita? Lallai ba ƙaramin kuɗi ne da shi ba, sai dai babu halin ƙwarai.
A ƙofar gidana na tarar da Naja a tsaye tana latsa waya. Da mamaki nake duban ta bayan na sauka daga napep, har na ƙarasa kusa da ita ba ta ɗago ba, ga dukkan alamu ba ta gane ni ba duk da akwai wutar nepa. Fuskata babu walwala na ce. "Ga ni, sai ki faɗa mini abin da za ki mini da kika azalalo ni na taho." Ta ɗauki sakanni tana kallo na bayan ta ɗago kanta ba ta ce komai ba, sai can ta numfasa ta ce. "Hafsah ke ce a haka mayafi a gefen kafaɗa? Ba da ban kin yi magana na shaida muryarki ba da ko bangaza ta kika yi ba zan gane ki ba, saboda yadda gabaɗaya kika canza." Jujjuya jikina na yi na ce. "Ya ranki?" Ta jijjiga kai sannan ta ce. "Sai da kika je taron kenan?" Na ce. "Na je ɗin."
"Me kika ƙaru da shi to don Allah ?" Ta yi maganar cikin takaici.
"Abubuwa da yawa mana, na je na ga masu kuɗi na shiga manyan gidaje, ko banza na kafa tarihi, ga kayan ƙawar da aka ba ni na saka a jikina, ban da haɗaɗɗen abincin da na ci da wanda na yo guzurinsa." Kallo na kawai take yi kamar wadda na canza mata, tsaki na ja na ce. "Kin saka ni a gaba da kallo, wai mene haka ne?" A sanyaye ta ce. "Babu komai, ga shi nan kuwa kin yi kyau abinki." Sarƙar wuyana na riƙo ina jin kaina ya ƙara kumbura na ce. "Kayan kyan ne suka saka na yi kyan ai, har da sarƙar gold fa." Kama haɓa ta yi ta ce. "Allah ya ƙara arziƙi Hajiya Hafsah, ni dai abin da zan faɗa miki duk daular da za ki je ki gano kar ki ƙara raina ƙoƙarin Anas, arziƙi ne a rayuwa kowa da yadda Ubangiji ya ga da ma ya ba shi, ke kina hangen wasu, wani kuma yana can yana hangen ki, yana cewa da ma shi ne ke." Baki na taɓe na ce. "Kuɗi abin so ne fa, ba zan taɓa daina son irin rayuwar ƙawayena da fatan kasancewa kamar su ba har abada." Ta ce. "Tom shikenan, amma ki sani hakan tamkar yake da ki ɗauki wuƙa ki daɓa wa cikinki ne, matuƙar kina tare da waɗannan matan da ba ajinki ba ne, saboda rabuwa da su shi ne kawai masalaha a gare ki."
"Abin da ba zai taɓa yiyuwa ba kuwa kenan." Na faɗa cikin haƙiƙancewa. Gyaɗa kai ta yi ta ce. "Allah ya taimaka, ga fili ga mai doki."
"Saura sukuwa mai kyau in sha Allah." Na faɗa cikin tarar numfashi. Murmushin takaici ta yi ta ce. "Ni zan wuce, da ma so nake na tabbatar da kin dawo kafin na tafi, don ba na son na ƙara jin kunya a gurin mijinki, jiya na gama yi masa daɗin bakin kin canza amma kika ba ni kunya, ya zo yau ya tarar ba ki dawo ba." Cikin gatse na ce. "Allah ya kiyaye." Daga haka na buɗe ƙofar gidana na shige. Naja ta bi ta da kallo kawai, cikin ranta tana addu'ar Ubangiji ya dawo da ƙawar tata cikin hayyacinta da gaggawa, don ta ga alamar ta yi nisan da ba ta jin kira. Ba ta bar ƙofar gidan sai da ta kira Anas ta sanar masa dawowar da Hafsah, ta kusa awa biyu a zaune a ƙofar gidan kafin Hafsah ta dawo, saboda hankalinta ba zai taɓa kwanciya ba idan ba ganin dawowarta ta yi ba, saboda ba ta son Anas ya ƙara zuwa ba ta dawo ba, don ta san hakan zai iya ƙara janyo musu wata matsalar. Ita kuma abin da take gudu kenan, ba ta son ƙawar tata ta yi rashin nagartaccen miji, shi ya sa ta ɗaukar wa kanta alƙawarin duk yadda za ta yi wajen ganin ba su rabu ba za ta yi iya yin ta da yardar Allah.