Sashe 50
Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
*Zeey Kumurya*âœï¸
[3/8, 1:45 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGH PENS*
(FREE BATCH)
*26.*
Kallon kowacce kusurwa ta ɗakin ta yi sannan ta yi ƙasa da murya ta ce. "Kafin na ce komai, babu CCTV camera a parlourn nan?" Ina bin bango da kallo na ce. "Ban sani ba, amma kamar babu." Miƙewa ta yi ta ce. "Tashi mu je bedroom ɗinki dai, sai hankalina ya fi kwanciya." Ban ce komai ba na miƙe ta bi ni a baya.
Bayan mun shiga mun zauna ta ce. "Bari na kira Zuhura video call, don ki fi tabbatar da abin da na faÉ—a, ki kuma fi yarda da ni."
"Wace ce Zuhura?" Na tambaya ina mayar da numfashi.
Ba ta ba ni amsa ba, ta yi latse-latse a wayarta, bayan ta yi ringing an ɗaga ta yafito ni da hannu, na leƙa na ga wadda ta nuna mini hotonta tare da mijina ce fuskarta ta bayyana a kan screen ɗin wayar, gaisawa kawai suka yi ta katse kiran. Hawayen fuskata da ya fara bushewa na goge na ce. "Na riga na yarda da ke tun a fari, ki faɗa mun hanyar da zan bi na rabu da wannan ƙaddararren auren shi ne kawai damuwata." Taune lip ɗinta ta yi ta ce. "Ba ni da yaƙini ɗari bisa ɗari abin da zan faɗa miki zai saka auren ki ya mutu, amma ina da tabbacin idan kin yi komai cikin nutsuwa da wayo da dabara to tabbas za mu yi nasara. Abin ba wani mai wahala ba ne, kawai idan ya dawo ki saki jikinki da shi, ki nuna masa kin yi accepting rayuwar gidansa, ka da ki sake ko da wasa ki nuna wata alama da zai gane plan kika shirya." Jinjina kai na yi na ce. "In sha Allah."
"Good!" Ta faɗa tare da sauke da numfashi sannan ta ci gaba da magana. "Ki ba shi abinci da abin sha da kanki, a cikin drink ɗin zan kawo miki wata ƙwaya ki saka masa, wadda za ta bugar da shi ya fita daga hayyacinsa." Waro ido na yi na ce. "Bugarwa kuma?" With confidence ta ce. "Eh mana, amma ba maye zai yi irin na mashaya ba, kawai za ta hau masa kai ne, ya yi ta abubuwa ba tare da ya sani ba. A lokacin za ki yi amfani da wannan damar, ki ɗauko biro da takarda, ki ba shi ya rubuta miki saki har uku, ki kuma saka ya furta da bakinsa ki yi record, don ya zama hujja." Cikin ɗaurewar kai na ce. "Ban gane ba? Mene ne hukuncin sakin a musulunci? Duk abin da zan yi ba na so ya shafi addinina fa?" Murmushi ta yi ta ce. "A addinance kin saku, saboda ko asiri aka yi wa namiji ya saki matarsa malamai sun ce sakin ya yi, haka ma wanda ya sha abun bugarwa." Cikin tantama na ce. "Wannan ai shi ya sha don karan kansa ya bugu, akwai banbanci da saka masa aka yi ba bisa son ransa ba."
"Amma babu banbanci da wanda aka yi wa asiri ko?"
Shiru na yi ina nazari, zuciyata tana son karɓar abin da Karima ta zo mini da shi, amma kuma ba na son a yi sakin ina murna kuma daga baya a zo a samu matsala, ko kuma shi ya dage bai sake ni ba.
Dafa kafaɗata ta yi cikin karya harshe ta ce. "Kar ki ji tantama ko ɗar a cikin ranki, wallahi indai kika yi yadda na ce kin saku, amma idan zuciyarki ba ta aminta ba za ki iya tambayar malamai ki ji." Wahalallen numfashi na sauke na ce. "Na gamsu mana, kawai ina tunanin matsayin abin da zan aikata ya yake a gurin Ubangiji, ina da zunubi ko ban da shi?" Cikin ƙarfafa gwiwa ta ce. "Ba ki da zunubi, saboda mijinki ba mijin aure ba ne, kina da ƙaƙƙarfar hujjar da idan kika kai shi kotu musulunci ya ba da damar alƙali ya raba aurenku, kawai don ya fi ki power ne ya sa ko kin kai shi ƙarar ba za ki yi nasara ba, wannan abin da na faɗa miki shi ne kawai mafita a gare ki." Shiru na yi don gabaɗaya na rasa ta cewa, kaina ya kulle ban ma san matsayar da zan yanke akan al'amarin ba. Miƙewa ta yi ta ce. "Ki yi tunani, amma ki sani ba zan taɓa faɗa miki abin da ba shi ba ne ko kuma wanda zai cutar da ke ba, taimakon ki kawai zan yi saboda Allah, don a yadda Zuhura ta ba ni labarin baƙinciki da ƙuncin da ta shiga a gidan nan ko maƙiyina ba na fatan ya kasance a cikinsa." Tashi na yi ni ma na ce. "Na gode sosai Aunty Kareema, kuma na ji daɗin da ba zai misaltu ba, Allah ya saka miki da alkhairi da wannan hanyar da kika samar mini, in sha Allah zan yi duk yadda kika ce, ba zan ba ki kunya ba." Murmushi ta yi ta ce. "Babu komai Aunty Hafsah, ko babu wata alaƙa a tsakaninmu na gan ki a cikin wannan halin zan taimaka miki, bare kuma yadda muke da ke. Ki jajirce ki cire tsoro da fargaba, yadda duk wayonsa ba zai taɓa gano ki ba, idan har kin amince za ki yi zan kawo miki ƙwayar da za ki zuba masa ki ajiye har ya dawo ɗin." Da sauri na ce. "Na amince, don ni kawai burina a yanzu na bar gidan nan." Ta ce. "In sha Allah Ubangiji zai ba ki nasara, ai ya ga zuciyarmu, niyyar alkhairi muka yi ba na sharri ba, don a munin abin da mijinki yake aikatawa zama da shi ya haramta, ko abota da fasiƙi Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya hana, bare kuma zaman aure da shi." Cikin gamsuwa na ce. "Haka ne, amma ya zan yi da shi bayan ya dawo cikin hankalinsa? Kin san a jahilcinsa ko babu aure a tsakaninmu ba zai ƙi mu ci gaba da zama a haka ba, tunda da ma don na zame masa garkuwa da kare mutunci kawai ya ajiye ni."
"Kar ki damu da wannan, idan cikin dare kika samu damar aiwatar da plan ɗin kar ki nuna masa komai sai da safe, idan kuma da rana ne ko yamma ta kwana gidan sauƙi, kawai ki kira ni a waya, za mu shigo ni da mijina, sai ki fara pretending ɗin ruɗewar ya sake ki kina faɗa mana, na san ba zai nuna ba haka ba ne, gudun kar a gane shi mutumin banza ne, don idan ya musa kika nuna takarda ga kuma voice ɗinsa da kika yi record za a tuhume shi ya aka yi haka ta faru? Na san ba zai taɓa cewa ke kika shirya sakin ba ko kuma abu ya sha ya bugu, saboda idan ke ce kowa zai gane akwai wani ɓoyayyen abu kenan, idan kuma buguwa ya yi za a ce shaye-shaye yake yi da ma." Komawa na yi na zauna saboda jirin da na ji yana kwasa ta, a raunane na ce. "Ya Allah! To Ubangiji ya sa yadda muka tsara komai ya tafin mana daidai kar a samu tangarɗa, amma abin da kamar wuya, musamman yadda ya san ba san zama da shi nake yi ba." Watsa hannunta ta yi ta ce. "Wannan kuma ya rage naki, dabara ta rage ga mai shiga rijiya, ke za ki san yadda za ki yi ki yi masa abin da zai aminta da gaske har cikin ranki kin haƙura za ki zauna da shi, ki yi amfani da baiwar ki ta mace da Allah ya hore mana ta kissa da kisisina." Jinjina kai na yi na ce. "Na fahimta, da yardar Allah zan yi iya yina." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Allah ya ba da sa'a, ya tabbatar mana da nasara." Na amsa da. "Amin." Daga haka muka yi sallama.
Tun bayan da ta tafi na zauna nai ta ƙullawa da kuncewa. Tunda na zo gidan ban taɓa jin nutsuwa ta saukar mini a zuciya ba sai yau, na ji kamar har an yi sakin an gama.
Washegari na fara aiwatar da abin da na tsara, na kwashe duka kuɗaɗen da ya bar mini na ɓoye, na fara yin kwalliya sosai yadda idan ya dawo zai fi aminta na kwantar da hankalina. Na je aka yi mini kitso da ƙunshi, na siya garin kunun sabaya da na ga ana tallah na fara sha. Cikin sati biyu na fara sauyawa, na murje na yi kyau. Duk da cikin raina fargaba ce fal amma haka na danne ta, ban bari ta yi tasiri ba bare ta saka ni rama.
Sati uku da yin maganarmu da Kareema sai ga shi tsubul ga shi an jeho shi da safe, a lokacin ina kwance a parlourn ƙasa ina kallo.
Dam! Ƙirjina ya buga, cikin faɗuwar gaba na tashi zaune ina ƙirƙiro murmushin da bai kai zuci ba. Fuskata a sake na kama Haɓa na ce. "Zuwa babu sanarwa? Sannu da zuwa." Kallo na ya yi ba yabo ba fallasa ya ce. "Yawwa." Tare da wucewa ya nufi sama. Ajiyar zuciya na sauke cikin sanyin jiki na miƙe na bi bayansa don fara aiwatar da plan ɗina. A ɗakin kusa da nawa na tarar da shi yana waya. A raina na ce. 'Tsabar jaraba ko zama bai yi ba har ya fara ƙaddararriyar wayar da na lura ba shi da aikin da ya fi ta idan yana gida.' Wani kallo ya mun bayan ya gama ya ce. "Lafiya?" Fuskata ɗauke da yalwataccen murmushi na yi fari na ce. "Don mace ta zo gurin mijinta sai a tambaye ta a ce lafiya?" Taɓe baki ya yi ya ci gaba da sabgoginsa. Hakan bai sa na karaya ba, na ƙarasa kusa da shi na ce. "Ka yi haƙuri idan kana ganin kamar na takura maka, na san idan ka fita ne bai zama lallai na sake ganin ka nan kusa ba, ni kuma akwai maganar da nake son mu yi da kai." Ba yabo ba fallasa ya ce. "Ina jin ki." Numfashi na sauke na ce. "So nake ko sau ɗaya ne ka tsaya mu yi hoto tare." Yamutsa fuska ya yi ya ce. "Akan me? Ke ni fa ban da lokacin wannan shirme-shirmen." Karyar da murya na yi na ce. "Na sani, amma hakan mafita ne a gurinmu gabaɗaya, idan muna yin hotuna ana gani babu wanda zai gane irin zaman da muke yi, kowa ya san kai mijina ne ni matarka ce, kullum aka zo gidana ba a ganin ka, ba a taɓa ganin mu ko tare ba ko da a hoto ne, me kake tunanin zai zo zuƙatan mutane? Za a gane ni da masu aikin da ka ajiye ɗaya muke, gadin gida kawai nake yi kamar yadda abun yake." Ɗage kafaɗa ya yi ya ce. "Shikenan ɗauko wayar taki ki yi mana ki yi ki fice, ina buƙatar kaɗaici don akwai abin da zan yi." Wani abu da ya tsaya mini a maƙoshi na haɗiye na ce. "Kafin mu yi hoton na fi son sai na fara fatanta maka rai, yadda nishaɗin zai bayyana har a kan fuskarsa." Tsaki ya ja alamar na fara isar shi ya ce. "Na hutacce ki, don ni babu wani abu da za ki yi ya faranta mini rai, idan za ki ɗauki hoton ki ɗauka ni ki daina ɓata mini lokaci a banza."
"Har abin da kake yi da jinsin naka ba zan iya yi maka ba?" Na tambaya cikin danne tsoron da yake ƙara mamaye dukkan zuciyata.
Ƙura mini ido ya yi, ni kuma na dinga murmushi tare da addu'ar Ubangiji ya sa kar ya gano ni. Fuskarsa a tamke ya ce. "Me ya canza miki ra'ayi?" Kallon gefen ido na yi masa na ce. "Kaɗaici, na ci abinci mai kyau, na sha abin sha mai kyau, ina rayuwa a guri mai kyau, me kake tunanin jikina zai fara buƙata bayan wannan?" Watsa hannunsa ya yi ya ce. "Amma na ba ki damar yin mu'amala da duk namijin da kike so ko?" Girgiza kai na yi na ce. "Na sani, amma kishin kaina da na aurena ba zai bar ni na aikata hakan ba, kai dai da kake mijina kawai nake da buƙata, kuma ko ta kowacce hanya ce zan amince maka." Murmushi ya yi ya ce. "Da ma da shirina na ko ki amince ko kar ki amince sai na yi nake tafe, amma tunda kin samar wa kanki masalaha ki je ɗakinki ina nan zuwa idan na gama abin da nake yi." Miƙewa na yi na ce. "Ina jiran ka." Daga fice na bar shi.
A kan carpet na zube a parlour ina sakin ajiyar zuciya, wani irin bugu zuciyata take mini kamar za ta fasa ƙirjina ta fito, sosai nake tsoron tarwatsewar plan ɗinmu, don shi ma tantirin ɗan'duniya ne idonsa tar yake kallo na.
Na daɗe a zaune kafin na ba wa kaina ƙwarin gwiwar tashi na ɗauko juice na jefa ƙwayar da Kareema ta kawo mini na jijjiga na mayar na rufe na saka a cikin fridge ɗin ɗakina.
Sai wajen Æ™arfe uku ya shigo, lokacin ban jima da fitowa daga wanka ba. Cikin faÉ—uwar gaba na dube shi na ce. "Sai yanzu?" GyaÉ—a mini kai ya yi tare da fara cire kayan jikinsa. Addu'ar neman tsari na shiga yi a cikin raina, don a wannan gaÉ“ar dole É—aya a cikinmu ne zai yi nasara, ko ni na yi nasara ko kuma shi ya samu damar aiwatar da mummunar ta'adarsa a kaina. Tunanin yadda zan gabatar masa da abinci da juice É—in ba tare da ya yi zargin wani abu ba na fara yi, har ya kammala cire kayan ya tunkaro ni ban samu wata matsaya ba, sosai fargaba, tsoro da firgicin kar na je garin neman riga na rasa ido suka cika zuciyata.........âœï¸