← Book details Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 54

Sashe 40

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Mun ci gaba da shan soyayya ni da Alhaji Mansur Idonnera, idan muka fara waya har mantawa nake yi kati ake zara saboda daɗewa, ga shi kuma ya ce mini ba ya ƙasar, wani tsari yake yi da duk ƙasar da ka je da sim ɗinka za ka yi amfani, amma ba ƙaramin kuɗi ake ɗauka ba. Idan mun gama wayar mu ɗora da chatting. Sati ɗaya da haɗuwarmu amma kullum sai ya tura mini credit ɗin 20k ya ce na saka data. Hakan ya sa ni kasancewa a cikin nishaɗin da ban taɓa riskar kaina a ciki ba, tare da ƙara mantawa da Anas, su Sultan ne kullum sai na tuna su, amma shi ma ban bari yana damu na ba. Na ƙara tabbatarwa kuɗi su ne jin daɗin rayuwa, su ne gishirin zaman duniya kamar yadda ake yi musu kirari, su ne farincikin komai a rayuwa.
Yau Friday yau muka yi da shi zai zo mu haɗu, duk da ina murnar ganin shi amma da fargabar yadda zan sanar da Kawu batun shi na tashi. Ba na so ya yi zargin wani abu ko ya saka ayar tambaya a kaina, don mutum ne shi mai zurfin tunani da nazari. Ina zaune bayan an sakko daga masallaci na samu mafita, akwai wata kamar Yaya take a gurin shi, zan ce masa zan je gidanta na gaishe ta, idan ya so sai Alhaji Mansur ya je can mu haɗu. Don na san ita ba za ta hana ba, musamman idan ya zo ta ga mai kuɗi ne, don irin matan nan ne masu azababben son kuɗi. Cikin murna na shirya, bayan na rufe na ɗakina na yi wa Gwaggo sallama na fita. Na tsugunna a soro na ce. "Sannu Kawu, ya jikin?" Ya ce. "Da sauƙi Alhamdulillah." Na ce. "Allah ya ƙara afuwa." Ya ce. "Amin ya rabb." Kaina a ƙasa na ce. "Da ma gidan Inna Habi nake son zuwa na gaishe ta." Ya ce. "Da kuwa kin kyauta, ga shi kuwa Juma'a ce ga ladan Zumunci, ki je Allah ya kiyaye, ki gaishe ta." Na ce. "Za ta ji." Har na miƙe ya tsayar da ni da faɗin. "To kina da kuɗin mota?" Na ce. "Eh Kawu." Ya ce. "Kar fa ki yi tafiyar ƙafa, idan ba ki da shi ki faɗa na ba ki." Na ce. "Ina da shi wallahi." Ya ce. "Toh shikenan Allah ya kiyaye hanya, kar ki dare amma." Na ce. "To." Duk ci da kaina ɗin da nake yi Kawu bai sani ba, don shi duk a zaton shi Gwaggo ce take ciyar da ni a cikin abincin siyarwarta, saboda duk ƙi na da take yi da muguntar da yi mini a baya ba ta taɓa nunawa a gabansa, yi take kamar za ta lashe ni saboda soyayya idan a gaban idonsa ne, shi ya sa har yau bai gane makircinta ba, ni kuma ban taɓa faɗa masa ba. Na san ko da ba kullum ba zai taɓa zama bai ba ta kuɗin cefane da abin da za a dafa ba, ƙeta ce kawai ta saka ba za tana ba ni abincin ba. Ni kuma ban damu ba tunda Allah ya rufa mini asiri, kuma ba jimawa zan yi a gidan ba zan tafi gidana na alfarma.
Kawu kuwa da kallon tausayi ya bi bayan Hafsah har ta fice, ya yi alƙawarin duk inda ta tambaye shi za ta je ba zai hana ta ba, amma ba wai zai bar ta tai ta gantali ko'ina ba ne. Saboda ya san fitar ce take ɗan ɗeɓe mata kewar halin ƙuncin da take ciki.
Da sallama na shiga gidan Inna Habi, na tarar da ita a zaune a tsakar gida tana dakan daddawar miya. Ba yabo ba fallasa ta amsa mini, don ba wani kula Kawu take ba saboda talaka ne, don ita indai kaga ta shigewa wa mutum to yana da maiƙon da za ta lasa ne. Tsugunnawa na yi har ƙasa na ce. "Ina yini Inna?" Ta ce. "Lafiya ƙalau, ya Baban naki da jiki?" Na ce. "Da sauƙi Alhamdulillah." Ta ce. "Ma sha Allah, Allah ya ƙara sauƙi. Har kin yi idda ko?" Na ce. "Eh, tun wancan satin ma." Ta ce. "To Allah ya sa haka shi ya fi alkhairi, ya kawo miki wani mijin na gari, ga tabarma can je ki zauna, bari na kawo miki ruwa." Na ce. "To Inna." Bayan an yi la'asar na share mata tsakar gida da ɗaki, ta gama abinci ta zuba mini muna ƴar hira. A lokacin na sako mata zancen Mansur, ina kallon wayata da message ɗinsa ya shigo na ja tsaki. Inna ta ce. "Ke kuma lafiya kike jan tsuka ke kaɗai?" Ɓata fuska na yi na ce. "Wani ne ya dame ni wallahi, wai dole sai ya zo mun haɗu yau." Ta ce. "Wane ne? A ina kuma kuka haɗu?" Yadda na faɗa wa Maman Sabir haka na zayyana mata ita ma." Haɓa ta kama ta ce. "To shi ne me? Mene abin damuwa? Ki tsaya ki saurare shi, ki bar shi ya zo. Ki cire wancan tsohon mijin naki daga ranki ki fuskanci abin da yake gabanki." A shagwaɓe na ce. "Inna yana da kuɗi daga gani mutumin, ni kuma gaskiya ba na son irin masu mahaukatan kuɗin nan." Dundu ta ɗaka mini ta ce. "Ku ji mini sakarar yarinya kai, Allah ya kawo miki tsuntsu daga sama gashashshe za ki butulce masa, wa yake ƙin kuɗi? Ai kuɗi abin so ne, tashi ki je masa ki share seat room ki ƙara gyara shi, ki zo ki karɓi turaren wuta ki saka, sai ku yi zancen a can." Ina murmushi na tashi cikin farincikin haƙata ta cimma ruwa, da ma na san ina cewa mai kuɗi ne za ta goya mini baya, kuma da ma a gurinta kaɗai nake tunanin samun haɗin kai cikin ruwan sanyi. Address ɗin gidan na tura masa, da ma text ɗin da ya yi mini kafin na yi mata maganarsa akan yana jiran address ɗin ne.
Sai da ta saka na sake sabon wanka na yi kwalliya, ta ba ni turare na fesa. Bayan Magriba ya yi mini text ga shi a ƙofar gidan, inda Allah ya taimake ni mota tana shiga cikin layin. Da zan fita ta ce. "Ki sakar masa fuska fa, kar ki cukule ki yi dinkum, kin ji na faɗa miki." Na ce. "To Inna."
Da na fita na yi zaton zai fito daga motar ne, sai ga bai yi hakan sai horn ma da ya danna. Ina murmushi na ƙarasa gurin motar na buɗe front seat, zuciyata cike da kewar shi, don yau kwata-kwata ba mu yi waya ba sai dai chat, saboda yana cikin hayaniya ya jejje companies ɗinsa don ganin yadda abubuwa suke tafiya.......✍️

*Zeey Kumurya*✍️
[3/8, 1:43 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

*21.*
Chapter 40 · 0% Book details