← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 35

Sashe 8

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nene ta dau son duniya ta dorashi kan D'ija bata so ko kuda ya sauka a kanta sabida yadda take rattalinta,lokacin da ta isa shiga makaranta Alh Bashir yazo ya yiwa Nene maganar ya kamata tafara zuwa makaranta ko Ka wai ta bashi yarinyar ya tafi da ita ya hadata da sa'arta Fa'iza ya sakasu a tare,Nene tace Sam bata yadda ba ,ita ya kyale ta,alokacin shi kanshi Lawan yaso Nene ta hakura ta bada D'ijan a tafi da ita abujan amma ganin yadda ta rika fada yasa ,yayi shiru da bakinshi domin dama in Nene tana rigimarta akan "yar tasa yasa yaja bakinshi yayi shiru kawai ya zuba musu ido

Haka Alh Bashir ya kammalawa D'ija komai na makaranta sannan ya wuce ya tafi bayan ya tab star da ya ajiye musu komai Wanda zasu bukata

D'ija ta taso da rigima gami da kwarafniya yarinya mai wayo sosai gata Sam bata barin takwana shiyasa ko a makaranta yara sa'ointa suke shakkarta ,tana da bala'in son girma kamar gyambo shiyasa Sam basa shiri da kawarta Indo sabida itama indo bata son rai ni ko kadan,kullum sai ankawo kararta Nene tayi ta fada tana cewa sun takurawa marainiya kwata kwata D'ija taqi karatu ko taje makarantar ma babu abinda takeyi sai naiman fada ,malamai duk sun San halinta,Lawan in yana mata fada Nene sai tasa kuka tace"yana nuna mata iko dan yaga "yarsa ce"haka yake hakura kawai amma abinda "yartasa takeyi yana bata masa rai

Allah sarki rayuwa,D'ija na da shekara shida a duniya Allah ya karbi ran Lawan sakamakon ciwon ciki farat daya,mutuwar ta girgiza zukatan al'umma mussaman dan uwansa Alh Bashir Nene tayi kuka sosai da sosai ta fawwala wa Allah ikonshi bayan sadakar bakwai nanma Alh Bashir ya rika tausar Nene kan ta bishi abuja ganin yanzu tazama ita daya kadaici zai dameta,Tace Sam bata amunce ba ita dai ya barta a dakinta ai a kwai "yan uwa da abokan arziqi,haka alh Bashir ya tafi badan yaso ba sai Dan gudun bacin ran mahaifiyar tasa

Haka rayuwa tai ta tafiya D'ija Sam taqi karatu yau in taje makaranta gobe baza taje ba ,wannan ne dalilin da yasa makarantar boka suka sallame ta gaba daya Nene tace ta nemi guri ta zauna ai ba dole bane a karatun bokon ,sai na addini,ko isilamiyar ma a makare take zuwa ,shiyasa Sam bata gane karatu sosai.

To a cikin wannan lokacin Ali ya sauka garin bayan ya kammala karatunsa na aikin Soja a kasar Engila

Misalin karfe shida da wani abun ya fito yana sanye da jallabiya ruwan toka tsakar gidan ya rika bi da kallo ganin ko ina a share babu datti ,tsaf iska sai kadawa takeyi gwanin sha'awa ,girgiza kai yayi ,kawai sabida dama tuntuni yasan Nene macace mai bala'in tsafta,kai tsaye kchin ya nufa ,domin bazai iya Wanka da ruwan sanyi ba kasancewar an kwana ana ruwan sama ,duk da yake mutum ne shi Wanda baya kaunar zafi ko kadan hakan bazai sa yasawa jikinshi ruwan sanyi da safiyar nan ba ,Nene na zaune kan kujera "yar tsuguno a kchin din tana joye ruwan zafi cikin fulas ,ya shiga kchin din

Ta dago kai tana kallonshi , yana tsaye jikin kofa sai faman ya mutse fuska yakeyi kamar yadda ya saba

Tace"ka tashi ashe ,ka ganni nan nima sauri nakeyi in kammala hada kayan karin kummalo ,sai muyi wanka domin bana son muyi tafiyar rana"

Gyaran murya yayi kadan ,yace"Nene kin tashi Lafiya"?

Ya share maganar da take masa

"Lafiya kalau na tashi ni kam"
Nene tafada tana juye man da tayi soya da shi cikin wani kwano

Ya mutse fuska yayi yace"kina da ruwan zafi ko"?

"Me zakayi dashi"?
Nene ta tambayeshi kai tsaye
Sabida tasan ba ya wanka da ruwan zafi

"Wanka zanyi dashi naji garin a kwai sanyi"

Cikin mamaki Nene tace"Yau kuma kai ne zaka yi wanka da ruwan zafi,?ashe dai karya ce kawai mutum yace ,shi baya jin sanyi da ko wane lokaci

Babu abinda yace mata ,ya sunkuya yana kokarin daukar fulas din da ta juye ruwan zafin a ciki sabida yaga lokacin da take juyewa

Nene tace"ai ka tsaya na miko maka ko"

Shi dai bai ce mata komai ba ya dauki fulas din zai fita,tace "Muskili kafi mahaukaci ban haushi

Dai-dai bakin kofa suka kusa yin karo da D'ija ta shigo kchin din ,yayi saurin ja da baya yana ai ka mata da banzan kallo fuskarshi a murtuke

D'ija ma tsorata tayi ganinshi ne tsaye a gabanta ,sai jikinta yafara rawa,

Saurin dauke kansa yayi daga kanta ganin kayan da suke jikinta ,riga ce iya gwiwa gashi ta kama mata jiki ,gashin kanta duk a barbaje fatarta luwai luwai , gabanshi ya rika faduwa ,sabida Allah da ya halliceshi yana bala'in son mace mai gashi mai sharp sosai fatar ta tazama kalar coffee ya lura wannan yarinyar duk ta tara abubuwan da yake muradi ga "ya mace duk da take yarinya bata gama cika mace ba amma duk ga alamu nan sun nuna

Ficewa yayi yana jan tsaki ko da wasa bai kara kallon ta ba

D'ija ta sauke ajiyar zuciya tana tabi bayanshi da harara ta zumbura baki , kawai ta wuce ciki gurin Nene

Nene tace "kin tashi ko dube ki don Allah,kai yayi duguzun babu gyara gaki Allah ya baki gashi,amma Sam sai kice baza'a miki kitso ba"
Da zaki daure sai kije gidan Delu tayi miki ko manya ne kafin mu tafi"

D'ija ta karasa kusa da Nene tace"Nifa Nene bana son kitso wallahi kawai ki taje min kamar yadda kike min"

Tabe baki Nene tayi tace"ai shikkenan kanki ne ,ke zai dama, ai

Zumbura baki tayi gami da cewa "Ni dai ki kyale min kai na haka"

Nene tace",to mai kika ji nace dake ne "yannan"?

"Allah ya shiryeki

Tashi tayi daga kan kujerar da take zaune ganin sabon ruwan data daura yana nai man tafasa bandaki tashiga tare da dauko baban bahon dasuke wanka tajuye wa Dija ruwan tace " kimaza kije kiyi kifito kin tsaya surutu da fadi ba,atambayeka ba kinsan in yariga fito zai zo ne ya azzalamana ko"

Fita tayi daga kchin din ta nufi ban daki tana zumbure zumbure na shagwaba

Ita ko Nene kayan Karin nasu ta hau dauka tana shiga dashi daki tana kimtsa gurin da zasu zauna

Ali ne ya fito tsaf dashi cikin wata shadda wacce tai bala,in yi masa kyau ga sumarsa da tayi luf ta kwanta a kansa sai sheki take da ,alama ana kula da ita
Ida nunsa sanye da glass yayin da hannunsa yake daure da a gogo as,usuel fuskarsa kamar ko da yaushe ya shigo dakin yana bin ko i na da kallo

Fuska Nene ta hau gyarawa tace " AF ashe kagama kintsawa kaga muma mungama ai ga kayan kari ai yauma mutumin naka nai ma" tafada tana gyara zama itanan lallabashi take karya botsare al halin basugama kintsawaba, bayan hakama tana so tashiga makotan nasu ta yi musu sallama ganin cewar ansaba babu dadi kayi tafiya irin wannan baka sanar da abokan zamanka ba

Ya mutsa fuska yayi yana duba a gogo yace "duba time fa Nene yanzu karfe Tara har da "yan mintoci ummm"! yafada yana kallonta tare da fadin sai yaushe kike so mu kama hanya ne"?

Cikin sauri Nene tace "yanzu nan ai babu abinda zanyi kuma in ba wanka ba Dija nake jira ta gama nashiga naje nai"

Bai CE komai ba ya shige dakin kan kujera ya zauna yana Dada gyara link din hannun rigarsa

Nene kam kunun ta hau zubamasa da zafinsa gashi sai kamshi yake yaji kayan kamshi sannan ta CE "ko in hada ma shayi ne kallonta yai yace "me kika mai da nine wanan dinma is ok yafimin wani shayi ni" amman dan zubamin madara a cikin kunun ya fada yana dan sakin dariya ciki ciki sabida yasan sai tayi magana

Ai kam harara ta gallamasa tace" baka da hannu ne zuba ma na da kanka ai gatanan kan ta rufe baki Dija tashigo dakin jikinta daure da wani karamin zani kanta duk rabinsa a jike da ruwa kai tsaye jikin siff ta nufa ta na kokarin futu da kayan da za tasa dan tun jiya da daddare ta waresu a gefe

Nene tace "kin fito ba bara nashiga kafin infito sai kihada kayan karin gashinan"

"To Dija tace yayin da take kukarin. Saka kayan ta kwata kwata bata lura da mutum a dakin ba kasan cewar dakin yana da girma Nene kawai tagani wacce take daura da bakin kofa,,

Cire kayan ta tai tana kokarin saka wando bayan tasaka ta jawo rigar tana kokarin sawa rigar taki shiga kasancewar ta mai botor ce irin rigunan ne dogaye odar dubai wanda Alh bashir ne ya kawo musu iri daya ita f'aiza wani zuwa dubai dayayi

Shikam Ali tun lokacin da ta cire kayanta yai saurin dauke kansa abin yana yimasa yawo aka domin dai wata irin hallita ya gani wacce ta bashi mamaki ,,,asace ya kara kallon gefen da take itakam sai kici kicin sa, rigar take takasa gano daga inda rigar takasa shigarta.

Kallon ta yake tagefen idon sa yana dan kurbar kununsa hankali kwance aransa yace dubi ba gidajiya ko tayaya rigar zata shiga bayan bata balle botir din taba

Cire rigar ta yi daga inda ta makale cikin bacin rai tai hanyar fita da rigar ahannun ta gashi daga ita sai karamin wando

Ali kam ganin tayi hanyar fita daga dakin babu kaya a jikinta bai San sanda yace "keeee!! cikin sauri Dija ta waigo cike da tsoro dan batai zaton da mutum a dakin ba bayan Nene

Gyara fuska yayi ya hau ya mutsata yana kallonta kasa kasa dan shikam bazai iya jurar kallonta a haka ba duk da ceawa da glass a manne a fuskarsa,,

Cikin maganarsa da isa yace "gidan ubanwa zakije haka da riga a hannu"? domin dai shi a zatonsa zata iya fita daga gidan ahaka da nufin taje a sa mata rigar ganin cewar Nene tashiga wanka

Zumbura baki Dija tayi tana kallonsa kai tsaye tace "rigar ce taki shiga jiki na bayan kuma ina sata bata ma tseni ba yanzu kuma nayi nayi ta shiga taki shine zan nunawa Nene
Chapter 8 · 0% Book details