← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 35

Sashe 2

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin kallo yabi Nene n dashi daga ita har dijan yace "har indai wannan abar ce zata kawumin ruwa wallahi bazan ci abincin ba kina ganin yanxu tagama kazantarta bayan tagama lashe hannunta ko wanke wa batai ba sabida tsabar kazama ce ita kice taka wumin ruwa insha ki kwashe abincinki namafasa ci ya Riga yagama yin sanyi ma" yafada yana Dada gyara kwanciyarsa a gefenta ,,harararshi tai ta tashi tana sababi wannan yaro halinka sai dai kai matar ka zatasha iyayi da feleke cikin daki tashige inda firji yake tadauko mai ruwan..,

Dije kam tana gefe sai faman harara take aiko mai dashi a zuciyarta take fadin a kwai babban kazami ma irin ka wai kai mai tsafta kadinga wani tsartar da yawu saika ce wata mace
Harara a duhu kenan take domin shi Ali bai San ma tana yi ba

Nene CE ta,ajiye mai ruwa na roba hade da lemu mai sanyi tace "gashinan to sarkin tsurfa tafada tana zama a gefensa ,,tashi yai yanu fi can gefe ya dauraye hannuwansa duk da cewa bawani abin ya ta6aba ,,

Dawo wa yai ya zauna yajawo kayan abinci yai bisimillah ya fara ci,humm Ali kenan cin abincinnasa ma abin kallo ne cike da tsurfa yake ci yanaci yana ta6e baki yana kallon Nene yana jiran yaji abinda zata ce,,

Itako kallonsa batai ba sabida tasan Neman magana yake ta cigaba d sabgoginta,,

Dije kam tashi daga gun tana faman zumbure zumburen baki taje ta wanke hannunta ,,tadawu sai taji tana san taci tuwan gashi cikinta yacika bayadda zata yi haka tashige daki ta canja kaya tahaye gadon Nene tai kwan ciyarta,,

Yana gama cin abinci yatashi daga gun ya canja guri bayan ya wanke hannuwansa ,,haka Nene tatashi bayya da ta iya ta kwashe kayan ta gyara gurin tana yi tana sababi ,,shida yai mata shiru a zuciyarsa yace da rigima kenan idan kikaji da abinda nazo garin kenan duk wanann da kike shafar mai ne

Bayan ta gama gyara gun tadawo ta zauna tana kallonsa tace "tun dazu nake jiran inji dame kazo min yau kuma ?

Murmushi ya saki yace" Nene mu kenan dame nazo miki kuwa inba da alkairai ba yafada yana kallonta

Washe hakora tayi tace "dan nema to ina jinka tafada tana tsare shi da ido,,gyara fuskar sa yayi Alamar maganar dazaiyi mai muhimanci ce yace " sako ne da ga ABBA"

yace "kihada kayanki gabadaya inzan tafi in tafi dake dake d waccan yarinyar ,,

Wani irin kallo Nene ta watsa masa tace "wallahi kakiyayeni Ali ka rainani ko bazanje ba"
Tun yaushe ake magana daya nace bazan jeba yakyalemu anan ina ce wancan satin shima basiru yazo nace bazan jeba saime zaku takuramin sai nabar daki na inatafi wata abuja ban zuwa tafada tana gyara zamanta,,

Kallonta yayi yana kwantar da kai dan ya fuskanci inba haka yayi mataba da akwai matsala dole sai yai aikin rarrashinta,

"Haba Nene wai yaushe zaki gane ne ba fa cewa akai kitafi kizauna acan gaba daya ba zakina dawu wa anan lokaci zuwa lokaci ,,kiyi hakuri mutafi kije kidan huta acan kinji uwargidana ya fada yana murmushi

Ko kallonsa batai ba yace "kinji Nene ,, tai mai banza

Yace "to shikkenan tunda kinza6i atafi da da dijan taki babu matsala ai ,, cikin sauri tadago kai tana banka masa harara

Dariya ce ta su6ucemasa ya din gayi sai da yayi mai isar sa sannan yace " "ai dama zabi biyu ya bayar Abba n yace inkice baza kixo ba to a tawo mai da dije zai sata a makarantar boko tunda anan kin hana ta karatun,,

Kallon sa tayi tace "to ai sai ka jamu ka kai mu abuja nace ni bazan zuwa ahe,,

"To ai shikkenan kin san zan iya ko ya fada yana kallonta ,,wallahi kiyarda kawai mutafi in bahaka ba sai ki wayi gari kiga natafi da wacan marakunyar inga yadda zakiyi yafa da yana ya mu tsa fuskarsa

Harararsa tayi tace "to katafin da ita mugani"

"Haka kika ce",? Yafada idonshi a tsaye a kan ta.

"Eh haka Na ce" tafada tana hararsa a karo Na biyu ,taci gaba da cewa munanan in da mukafi wayo babu wata Abuja da zamu ai nan ma tana karatun " To! Kaji"!
kallon ta yake yana ya mutse Fuska Na sabo yace"Shikkenan tunda kin fi son A tafi da yarinyar taki zaki wayi gari ki ga ba ta nan domin ba zamu zauna da Yarinya haka ba babu Arabi babu boko kin sangartata"

Sanin Halin sa yasa Na in yace zai yi Abu to sai yayi tunda taga yana wannan murmushin nashi tasan zai ai kata Ta kalleshi gami da gyara,zama tace " yanzu yaushe zaka tafi"?
Shiru yayi sai da ta qara maimaitawa ,yace" Nan da kwana biyu"
"To shikkenan zan bika Amma bazan Dade ba kwana biyu kawai zanyi in dawo ,domin bazan tafi in bar dakina ba ,da"yan Uwa da Abokan Arziqi"

Cikin zuciyarsa yace "Ai sai kidawo mugani Nene kenan in kika tafi kin tafi kenan,

Mi kewa yayi yana kallon Agogon dake daure a hannunsa ,ya kalleta Cike da tsokana yace" Daga zuwana duk kin bi kin rikice sai faman fada kikeyi,kinqi ki barni Na huta"

Dariya Tayi gami da ban tarar goron ta tace"ai kai ne Ali halinka sai kai daga zuwa kafara cikin zalin "yar marainiya Allah.

Yace "zan shiga ciki in Dan huta"

"To to ,cewa zakayi sai da safe kawai ,Ai gwara ka huta nasan A kwai gajiya a tare da kai ,Allah ya bamu Alkairi" Tafada tana kokarin kunna redion ta domin sauraren taskar Labarai A tashar Redio Kano ta bello dan dago.

"To Allah ya tashemu Lafiya Uwargida kuma Amarya" yafada yana nufar ,hanyar dakinshi Na gidan Wanda idan ya sauka garin yake kwana ciki.

Murmushi Nene tayi ,tabi bayanshi da Kallo ,Afili tace Dan Nema sarki iyayi da Feleqe kai dai naga matarka ai ka tsaya ruwan ido"

Yana jin ta yayi mata shiru domain in ya Daka ta tata sai su kwana a gurin gashi shi bacci yake ji ,bayan haka kuma jikinshi yayi masa Nauyi Wanka kawai yake son yi ,
Shi Mutum Wanda baya son zafi ko kadan.

ASALIN LABARI

Malam Ibrahim Haifafen garin Kano ne cikin Karamar hukumar Dan batta ,Mutum ne Wanda Allah yayi masa Arziqi a wancan lokacin ,shararan Manomi ne Wanda Mutane da dama suka ci suka bayar ta dalilinsa ,Asabili da Karamcinsa kwata kwata bashi da ganin kyashi ,in yaga baka da qarfi sosai zai talla fa maka har ka tsaya da kafarka.
To Allah babu ta inda baya jarrabar bawa duk wannan dukiya da Allah ya Azurtashi da shi ,Allah bai bashi haihuwa ba,
Shekararsu goma sha biyu da Aure da Matarshi Hajara,
Wannan Abu sam bai tayarwa masa da hankali ba,tunda yasan haihuwa nufi ce daga Allah ,gashi duk fadin Kano babu Asibitin da basu je ba shida matar tasa maganar dai daya CE ,duk likitocin suke fada lafiyansu lau lokaci ne bai yi ba.

Shiyasa kawai suka tattara suka barwa Allah ikon shi.

Ganin haka ne yasa "yan Uwa da Abokan Arziqi suka dinga kawo masa yaransu ,wai ko zai Aura domin yasamu haihuwa,
Yace"duk su kyaleshi ,yasan haihuwa lokaci ne idan yana da rabon haihuwa a duniya zai haihu ,ko yayi Aure ko bai yi ba,
Su kyaleshi kawai shi yanzu bashi da bukatar karin Aure

Shine fa "yan Uwa suka yi ca! A kan Hajara wato (Nene) cewar ai its ce ta mallakeshi sai Abinda tace yake yi.

To Ashe duk wannan Abinda a ke ciki Hajara Na dauke da ciki Dan wata Uku dukkaninsu basu San dashi ba.
I ta dai tanaji sauye sauye a jikinta Amma bata kawo ciki gareta ba,yau da lafiya gobe babu ,Malam Ibrahim yace su tafi Asibiti kawai a duba ta.

Tashin Farko Likita da ya dubata yayi mata a won fitsari anan ya gano ciki gareta,Dan wata Uku da kwanaki

Ya kalli Malam Ibrahim yace"matarka Na dauke da ciki Dan wata uku.

"Alhmdullihi Alhmdullhi Alhmdullhi"
Shine Abinda Malam Ibrahim yariqa maimaitawa yace"hakika babu sarki sai Allah ,ya Ubangija Na gode maka da kayimin wannan baiwar,
Yafada yana kallon doctor din fuskarshi cike da Annuri

Dr yace"tabbas Allah ne Abin godiya,yanzu zamu daura ta kan Abubuwan da masu juna biyu ya dace suyi da irin Abinci da ta riqa ci ,bayan nan kuma idan cikin yayi wata hudu sai tafara zuwa Asibiti domin a riqa Auna shi"

"In sha Allahu Malam din yafada"

Doctor ya rubuta musu Magani masu kyau sosai da kara lafiya ga mai ciki.
Sannan sukayi masa sallama suka tafi bayan Malam yayi masa Alkairi sosai da sosai

Nene ma tayi farin ciki sosai Amma bata nunawa sabida kunya irin ta fulani ,to haka dai suka cigaba da rainon cikin har lokacin haihuwa yazo.

Cikin ikon Allah Nene ta haihu lafiya cikin Dakin ta in da tasamu da Namiji ,farin ciki gurin Malam Ibrahim babu kama hannun yaro "yan Uwa da Abokan Arziqi suka riqa tayashi murna ,shiko ya din ga fitar da hatsi yana rabawa talakawa,ranar suna yaro yaci sunan Bashir.
Haka Bashir ya ta so gaban iyayenshi cikin kulawa domin Nene macace mai kula da yara gami da tsabta,
Sai da Basir ya shiga pramary 4 sannan Nene ta samu wani cikin lokacin yana shekara goma sha biyu ,wannan karon ma Malam Ibrahim yayi farin ciki haka yayi ta hidima da Nene da cikinta.
Lokacin da Bashir ya fahimci Mahaifiyarshi Na da ciki sai yayi ta murna zai samu qani,domin yana da bala'in son yara

****
Wannan karon ma Allah ya sauki Nene Lafiya a dakinta in da raqara samun da Namiji ,malam Ibarqhim yayi farin ciki sosai da sosai ,ranar suna a ka sawa yaro suna Lawan,

Nene taci gaba da rainon yaranta cikin kulawa,Bashir yana kaunar Dan uwansa sosai ,in babu makaranta shi yakewe Nene raino Dan har makarqntar Allo ya kan tafi da Lawan

Allah sarki mai yadda yaso ,shekarar Lawan Uku a duniya Allah ya karbi ran Malama Ibarahim mutuwar da ta gigita Zukatan Al'uma sosai,Nene tasha kuka daga karshe sai ta danga ga Allah taci gaba da rainon yaranta.
Chapter 2 · 0% Book details