← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 35

Sashe 33

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ita kam fa'iza cewa tayi wallahi babu ruwana haka kawai in baki Amsa A zaneni to kawai sai in ce masa ke bakuwa ce salon yaha da dani ya daka kowa tasa ta fi sheshi hayayyaqo mata Dija tayi tayi kanta tace to wallahi sai na rama dukan Akan ki kan kace kwabo Dija ta haye kan Fa'iza zata daka

Ita kam fa'iza tsayawa yayi kawai tana kallonta domin bata saba da wannan wasan ba karaso wa yayi gurin fuska babu yabo babu fallasa, yasa hannu daya daga ' Dija daga kan Fa'iza kamar wata "ya tsana ya Ajiye A kan kujera ko kallonta baiyi ba domin tsigar jikinshi yaji tana tashi kadan kadan fa'iza ya mikawa hannu wacce ke kwance a kasa tana jiran dukan Dija kamma hannu tayi ta tashi zaune yace ke kam kinji kunya duk wannan girmab jikin naki kibari wannan ta kayar dake harda " hayawa kanki kin tsaya kina kallonta wacce kina nai mata duka daya zata fadi """ dariya falon ya dauka, harda ummin Asabe ma ba,abarta a baya ba ita kam Na'ima kamar tafado daga kan kujera dan dariya harararta Aliyu yayi yace meye ,Abinda dariya Anan dan ubanki shiru tayi tana mai da dariyar ciki ummi tace har damu zaka zaga tunda muma munyi dariya ba,abin dariya Akai ba kuka fa,iza ta fashe dashi domin ita hawa kanta da Dija tayi bai mata ciwo ba illa dariyar da suke mata wanda harda ita Dijan

Yaya Aliyu kaganta tana yimin Dariya ko tafada tana nuna Dija kyaleta zan nuna miki yadda zaki dinga yi mata kema, in ta kuma hawa kanki da kokawa "kice mata yar kauye mai hawasan jakai' kinjiko tunda ita kunne kashi gareta'' shuru Dija tayi bata ce ko mai ba Amma ranta ya 6aci kallonta Aliyu yayi yace "malama ina dankwalinki ban hanaki zama babu dan kwaliba iyi? Dago kai Dija tayi tana kokarin kallon inda ta zaauna hijab din skull din ta hango can kusa da kafar ummi sabida haka bata ce komai ba ta tashi taje ta dauko ta zira ta kama han yar dakinsu

Cikin magana kasa kasa take cewa "ko ina ruwansa da dankwalina oho kawai sabida a dinga ta kura mutane " bata yadda yaji Abinda take cewa sabida tana jin tsoron dukan da zai mata in yaji dakin tashige ta kwa6e unipom din tasamu zaninta ta daura iya kirji tashiga toliet wanka dan ita ma gwanar wanka ce a rana tayi sau uku zuwa hudu wanka tayi tafito daure da zanin taje ta dauko wasu riga da wando na fakistan'' tasa mai kawai ta safa a jikinta bata yi tunanin yin wata kwaliyya ba kayan sunyi masifar yima ta kyau sun fito mata da Ai nihin qirar jikinta '' bom,bom din ta ya fito a cikin wando duk da wando bayi da 'shaf' Amma yafito ya zauna das das sabida rigar me shaf ce ga tsaga da ta ke dashi a gefe da gefenta cikinta kuwa A shafe kamar wacce bata cin Abinci """ kirjinta kuwa sun fito sunyi cir cir kamar goroba Alama ce da bata jima da fara irgar dangi ba tunda wani lokacin ma ba'a gani in dai ba kurawa gurun ido kayi ba Alamun bayyanar fara girmanta sunfi ga mazaunanta dan karamin hijab dinta take nema gaba daya tafito da duk kayan sif' din har na fa,iza ma basu' tsira ba ranta a 6ace tace to ina hijab dina tun ranar da suka zo bata ne meshi ba sai yau dashi tazo garin kuma haka takaraci ne mansa bata ganshi ba ran ta a 6ace ta fita daga dakin

Still dai kanta babu dan kwali domin ta manta ma dama hijab din take so tasa, kan fa'iza ta tsaya tace ke fa'iza baki ga hijab dina ba ? Da kallo suka bita har Aliyu shima yana falon har yanzu suna hira da ummi kallonta fa,iza tayi tace' ni zaki tambaya banganshiba to ba dole na tambaye ki ba kije ki duba min cikin kayanki ko yana ciki' bazan jeba fa,iza n tafada tana tashi daga gurin da nufin zuwa ta cire unipom dinta ''' ya Na'ima kiyi mata magana ta dauko min hijab dina Dijan tafada' idonta a kanta kamar zata yi kuka ummi ce tace "ban da Abunki Dija" hijab din daya ne da ke kije kisa wani mana mybe, shi wanda kike ne ma yana gurin wanki ko kallonta Dija tayi tace shi daya ne dani ' ummi Ai '' ok yi hakuri ke Na'ima dauko mata A ran naki tasa kafin gobe sai ku shiga kasuwa" ayimata siyyaya A binda bata da shi kin ji ko '' to Na'ima tafada ta mike tana kallon Dija tace "ko meye Abin kuka Anan oho kwai sabida bakiga hijab sai kidinga 6are wa mutane baki" sabida shagwa6a tafada tana dariya'' "ke kam kin cika zubar da girma ummi tafada tace' yanzu kuma in tarama kice zaki dake ta sai kace wadda kuka samu jaka' tana tafiya tace "ke dai ummi bakya son laifin Dija' tace "e ba naso din" ummi n tafada

Shi kam Aliyu tunda yayi wa dija kallo daya yayi saurin dauke kansa fuska ya dinga ya mutsewa bai ce komai ba cikin ransa kuwa yana mamakin yarinyar gaskiya duk Namiji' da ya san mace yasan menene mace to ya kalli "Dija yasan tana cikin jerin mata masu Amsa sunansu babban Abin bada mamaki ma yarinyar bata gama cika mace ba Amma ko mai ya fito masha Allah"" sabida haka hannusa ya zira cikin Aljihun jins din daya ke jikinshi yana laluben glass dinshi fuska babu walwala ya dauko ya zira sannan ya dago kai yana kare mata kallo tunda ga kafafunta har zuwa tsakiyar kanta lokaci guda sai ya dinga jin wani matsanancin kishinta yana damunsa fuska A mutukar murtuke yace " wuce daga kan mutane yarinya mara tarbiya kawai kinzo kinyi wa mutane kerere Aka wallahi wataran sai na raunata ki na ji miki ciwo shasha " vileger" kawai " sai zuba ruwan bala,i yake wanda shi kanshi bai san dalili ba' Amma baya rasa nasaba da jin wani irin bala'in kishinta yana kamashi

Cikin kujera taje ta zauna tana zumbura baki bata ce ko mai ummi kam cewa tai "kai kam kana da ta kurawa me tayima ne ' shiru yayi bace komai domin sai yaji zaman a gurin ya gundureshi wayarsa ya dauko yana daddadannawa bai kuma kallon in da take ba

Ummi tace "da yamma Na'ima sai ta kaiki salon ko Dija ? A wan ke miki gashin nan naki ko baya damunki ne"? Sakin fuska Dija tayi tace 'yana damu mana ummi' Ammafa bana son kitso Abar min haka" ummi tace "da har ina cewa Ayi miki kitso zaifi miki kuma zaki ji dadi kan" "A,a ummi ni dai " Dija' tafada kallonta Aliyu' yayi yace "to wallahi kitso za,ana yimiki bazaki dinga yi mana yawo da gashi a gida ba kina hana mala'iku rahama su shigo mana gida in ba haka ba sai dai ki wayi gari kiga nayi miki kwal kwabo sosai zan Aske miki kan tunda bakyajin magana'' ya hakikance sai faman bala'i yake zuba masa ido ummi tayi tace " wai kai ina ruwanka da yarinyar nan ne iyi? Kabi kadamu da lamarinta' don Allah karabu da ita ta sake mana''

Saurin gyara fuska yayi yana kallon ummi' yace "rayuwar da tayi abaya baza tayi ta ba yanzu lokacin da tana gaban Nene sai Abinda ta gada ma take' Anan kuwa wallahi ummi bazatayi ba" sabuwar tar biya za ayi mata can daban nan daban" duk yanayin wanan fadan ne sabida yaji ummi tayi maganar zuwa gurin saloon so yake ya soke fitar kallon ummi yayi yace Akwai wata mata data ke zuwa tana yiwa Nafisan faruk kitso ita Na'ima n tasan yarinyar kice tayima 'Nafisa waya ta turo yarinyar sai ta dinga zuwa tana yi mu su kitson gaba daya Amma daga yau na soke zuwa gurin saloon kitso ko wankin kai

Hararsa ummun tayi tace "to sannu ubansu ka hakikance sai faman fada kake kamar wani wanda Akai wani Abun " zo nan " Dija ummi tafada tana dauke idonta daga kan" Aliyu' zuwa Dijan tayi gun ummi n ta zauna A kasa kusa da kafafunta kama kan ummi tayi tace "wannan gashin naki dole sai An wanke shi sosai kafin Ayi kitson " kiyi hakuri ana minki kitso kin ji ko " to Ummi Dija n tafada"
Tsaki Aliyu ya dan ja kasa kasa shi kadai yasan Abinda yake da munshi'' mikewa yayi yana kallon ummi yace "zanje in kwanta zuwa biyar na yamma" kallonsa ummi n tayi tace '' to Abinci fa? "Ok kibarshi kawai ummina inna tashi naci yanzu ban jinyunwa'' "shikkenan Ai " ummi n tafada tana cigaba da warwarewa Dija tufkar da take kanta gashinnata kallo daya yayi musu ya sa kai ya fice daga falon

To Siyama kam lokacin da taje gida momy n ta tana zaune A falo ita da babbar Kawarta hajiya ladidi suna ta hira cikin farin ciki hajiya ladidi tana bata labari sabon malamin da tayi A can da garin nasu cikin zumudi momy tace haba dai yaushe zaki rakani " kin tabbatar ya iya Aiki in ce ko? rike baki hjy ladidi tayi tace "Ai shi wannan akin shi kamar yankan wuka ne karki damu sabida haka duk sanda kika shirya sai kizo in rakaki " Amma Asubanci zamuyi " domin Akwai layi A gurin " jiki na rawa momy tace "ni kam ko yanzu ma A shirye nake wallahi "kallonta hjy ladidi tayi tace " me kike ci na baka na zuba mubarwa gobe mana sai mutaki sa'a" "to Allah ya kaimu momy tace" tana Allah Allah gobe tayi suje' domin ita kam duk inda taji sabon malami ko boka "yan tsubbu da sauransu jikinta har 6ari yake" shiyasa dadyn Siyama gashin Asusuce kamar wani shashassha kullum ka ganshi tsabar ta wanke ta bashi ya shanye
Chapter 33 · 0% Book details