← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 35

Sashe 21

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

banza Nene tayi dashi bata ce komai ba'shi kam Abbah mai da hankalinsa kan Nene yayi yace "kiyi hakuri Nene duk yadda kika ce haka za'ayi Amma ina neman Alfarma A karo na biyu kiyi hakuri kiyi mana sati daya Anan don Allah in ya so sai in mai dake da kaina "

shiru Nene tayi bata ce komai ba ta mai da hankalinta kan tv da take ta faman yi.ita kadai

wannan ya nunawa Abbah cewar Nene Ta Amince da hakan

Ummin ce ta sakkon daga sama yayin da Dija da fa'iza suke biye da bayanta kara sowa tayi falon tana kallon Ali tace "kai kuma yashe ka dawo"?

kallon Agogo dai ya kara yi Akaro na biyu sannan ya kalli inda umminnasa take yaca "ban jima da shigowa ba ummi kinyini lafiya"?

"lafiya lau nayi ni ya Aikin"?

"Alhmdulilah Ummi. " ya fada

"masha Allah Allah ya tsaremana ku duk inda zaku shiga" 'Ameen ummi"

"gobe in sha Allah zamu tafi jahar taraba can jalingo ummi kiyimana A ddo'a " kallonsa ummin tayi tace " Addu'a kam kullum cikin yinta muke insha Allah zakuje lafiya kudawo lafiya"

"in sha Allahu " Abbah ya fada yana kokarin canja tasha hankalinshi na kan tv

fa'iza dake kusa da Abbah tun zamanta A gun kallon yaya Ali take cikin kayan sojoji sai taga kamar sojojin da suke gani A tv mussaman A tashar mbc 2

bakinta na rawa tace" yaya Ali ina wuni 'kallon inda yaji A na gaidashi yayi dan yasan muryar fa"iza ce Amma bai san sanda ta shigo falon ba sai waccan marakunyar ya gani tunda gurin zaman su daya da umminsa

kallon f'iza yayi fuska babu yabo babu fallasa yace " lafiya lau fa'izan Abba
"

mikewa yayi tsaye yana kallon Nene wacce tayi gurum A zaune ta tsurawa tv ido kamar wata mai fahimatar Abinda suke fada 'yace "wai haka A ke yi An barni ko ruwa baza 'A bani ba in magana Ace duk wacce tazo sai dai tazama bora ni dai babu ruwana duk wacce tafi kyautatamin itace mowa A gurina"

ko kallonsa Nene batayi ba domin ta san neman magana yake dariya yake kasa kasa wanda nene ce kawai ta fahimci Abinda yake

kallon ummi yayi bayan ya mike yace " ummi kisa Na'ima ta kai min Abinci zanje nayi wanka " "to.ummi tace 'kan tarufe bakinta ma sai ga Na'ima sun fito ita da siyama dama sallah suka shiga yi

jiki na rawa Na'ima take kallon Ali wanda ya ke kokarin fita daga falon tace " yaya Ali barka dare Andawo lafiya"?

yana kokarin sanya takalmansa yake Amsawa "ita kam siyama jikinta ne ya mutu tun lokacin da taga Ali cikin kayan sojoji domin bakaramin kyau su kayi masa ba sai. taga kamar bashi ba domin Allu Arjun ya ko ma mata na kasar hindu dan haka da wani irin mayataccan kallo ta bishi har ya fice da ga falon bata samu damar gaisheshi ba domin kasa motsa bakinta tayi sabida tsabar mutuwa da jikinta yayi

jiki A sanyaye Siyama taje tasamu guri ta zauna zuciyarta sai wani irin bugawa take jikinta yai bala,in sanyi sabida wani irin kwarjini da yaya Aliyu yayi mata

kallonta Ummi tayi tace " Siyama zo muje ki kai wa yayan ku Abincinshi domin Ummi bazata tura 'Na'ima ba kamar yadda yace Sabida dalili Siyama ita ce yafi dacewa ta kai masa domin ita yake shirin Aura 'tashi Siyama tayi har yanzu jikinta babu kuzari A ranta take fadin ga bikin zuwa Amma babu zanin daurawa dan ita yanzu shakkar tun karar yaya Aliyu take wallahi

bayan Ummi tabi kchin din tana ta faman zancan zuci

sai da Ummi ta kammala hada masa komai sannan ta kalli inda Siyama take tsaye tace ''gashinan ko"

"to" siyama tafada tana tana kokarin daukar Abinci da Ummin ta hada cikin wani kwando mai kyau

gabanta na faduwa ta fara bubbuga kofar dakin

yana zaune gefen katifarshi daga shi sai gajeran wando 'wani irin gashi duk yayiwa fatar jikinshi rumfa dama tun Asali shi mutum ne mai gargasa A jiki tun yana yaro

rigarshi yake kokarin ya jawo wacce take gefe A ajiye fitowarshi kenan daga wanka ya zauna yana tsane jikinshi da towol ya ji wayarshi tana kara shine ya zauna yana Amsa kiran wayar

kafin ya saka rigar yaji An turu kofar dakin An shigo

me zai gani Siyama ce A tsaye rike da kwando Abincinsa''ita kam siyama da taji An yi shiru ba 'a ce mata ta shigo ba shine kawai ta yanke shawarar shiga domin ita A tunaninta ko yana toilet ne sabida haka shine kawai tai tunanan bari ta shiga ta A jiye masa ta tafi domin har yanzu bata gama da wowa daidai ba tun ganin da tayi masa dazu

Wani irin kallo Ali yake wa siyaman gashi ya tsareta da idanuwanshi masu rikirkikita mata lissafi'"fasa sanya rigar yayi ya mayar ya A je a inda take 'har yanzu idanunshi yana kan siyaman ya zuba mata su kawai bai ce komai ba

Zubewa tayi A gun domin ji tayi gangar jikinta bazata iya daukar kafafunta ba wanda sukayi mutukar yin sanyi A sabili da irin kallon da Aliyu yake watsa mata 'ji take kamar wani magana diso yana fizgarta zuwa gareshi

dan haka da rarrafe takarasa har inda yake zaune ta gyara zamanta sosai sannan ta sunkuyar da kai kamar wata mai mummuna tace " yaya Aliyu barka da dare An dawo lafiya ya Aiki" ?

duk A lokaci daya tayi masa wannan gaisuwar

har yanzu Idanunshi yana kanta yana nazarinta ganin yadda ta wani firgice lokaci daya 'shi yarasa meyasa suke firgita idan sun ganshi tunda shi ba wani shiga sabgarsu yake ba Amma yana mamakin hakan shiyasa yake mamakin irin Abinda Dija take masa kwata kwata babu tsoransa A idanta A yadda yake ganinta 'dazuma cikinsu babu wanda bai gaida shiba banda ita yana kallon lokacin da take ta faman harara fa'iza lokacin da take gaisheshi

dauke i donshi yayi daga kan Siyama wace take zaune dabas A kafet din dake malale A dakin domin baza ta iya kallonshi ba A yanayin da yake ciki ba gaskiyar magana zata iya zuwa ta rungumeshi sabida ta shiga cikin wani yanayi shiyasa kwakwkwaran motsi ta kasa

Muryarshi ta ji yo kamar baya so yace "me kika shigo kiyimin A daki dama ke nace ki kawu min Abinci "??

bakinta yana rawa tace "A'a ummi ce tace in zo in kawo maka"

shiru yayi yaci gaba da danne danne A wayarshi

tafi minti Ashirin A zaune A gurun sannan ya dago kai yana kallonta yace ''zaman me kike yimin A daki har da wani tankwashe kafafu dan ubanki"

Jiki babu kwari siyama ta mike daga gaban yaya Ali ranta in banda tukuki babu Abinda yake ita tarasa yadda zatayi ta shawo kan gayan nan wallahi Amma babu damuwa Allah ya kai damo ga harawa wallahi in Ali ya shiga hannuta sai ya raina kansa "ita ka dai take fada A cikin ranta

ko kallo bai bita dashi ba don shi A rayuwarsa ya tsani mace mara kamun kai wallahi shiyasa kwata kwata bata burgeshi siyaman sabida ya fuskanci itama tana daya daga cikin irin wannan matan

A jiye wayar yayi gefe sannan ya jawo kayan Abincin yana dubawa fuska.A ya mutse

dambun shinkafa ne wanda A kai masa hadi da kayan lambu sai hanta yaji kayan kamshi sai turiri yake kamar yanzu A ka sauke shi ' gefe kuma farfesun kifi ne shima da zafinsa sai hadin lemonsa nafa wanda kullum sai ummi tayi masa sai dai in baya gari'

saukowa yayi ya tankwashe kafafunshi 'da kansa ya hada Abincin yadda yake so don ba zai iya yadda siyama ta zuba masa sabida ita ma bai yadda da tsabtar taba.

To Acan falo rigima ce ta hautsine tsakanin Dija da Siyama 'siyama ce ta zo wucewa bata gani ba ta takewa Dija "yan yatsun kafarta ta 'ita kam siyama sam bata lura da kafar Dija A gurin ba sabida ba 'a cikin hayyacinta ta shigo.falon ba

ta shi ne Dija tayi ta rike kugu tace ba zata yadda ba Sabida ita.ba dutse ba ce da zata taka ta don haka sai ta rama' dama gashi A cikin hadin zafinta take masifa sai cin ta take ' kallonta Siyaman take cikin mamaki ganin yadda Dijan take wani girgiza kamar wacce take fada da sa arta '

"ke Dija meye haka ki ke sa'arki ce ita"? Ummi tafada tana kallon Dijan

"Ummi taka ni fa tayi kina kallonta ita me yasa bata kallon gabanta in tana tafiya ' ni dai kawai ta A jiye kafarta in rama in tana so .na bata hanya ta wuce " Dijan ta fada tana kuma kankane hanyar "wai ita lallai Siyama baza ta wuce ba sai ta rama

Nene kam uffan bata ce ba ta zuba musu ido tana kallonsu ita tana mamakin tsiwar da take cin Dijan

Na'ima ce ta taso A fusace tayi kan Dija gadan gadan tace "zaki ci ubanki wallahi "yar iskar yarinya mara kunya ' bata hanya ta ko in zab zab ga miki mari"

ko gezau Dijan batayi ba tana tsaye tirmin danya tana magana kasa kasa " wallahi badai ubana ba kuma ni ba "yar iska bace "

mari Na'ima ta kaiwa.Dija tace " Au! nima zagina zakiyi mara kunya eyi"?

wani irin uban ihu Dija ta kurma wanda yasa Na'ima barin gurin babu shiri Siyama kam babu bakin magana 'domin bakinta ya mutu dama da tarin bakin cikin Abinda Aliyu ya kunsa mata sai gashi wannan marakunyar yarinyar tasa ta A gaba tana cin mutuncinta kamar wata sa'arta

zama tayi gefe dan ita ma ihun da Dija ta kurma ya bata tsoro saura kadan tasaki fitsari A wando

Nene kam ko A jikinta kallonta ma ta cigaba dayi kamar batasan Abinda A ke a gurin ba

Na'ima kam ranta A bace ta fita daga falon ta nufi bangaransu.yaya Aliyu domin taga shine daidai da Dijan in tana ta kama da taurin kai da rashin kunya

bugu daya tayi tajiyo muryarshi yana tambaryar wanene? "Nice yaya Ali" Na'ima tafada da sauri

"menene"? yafada sabida ya fahimci muryar Na'ima ce
Chapter 21 · 0% Book details