← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 35

Sashe 23

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mai da kallonta tayi kan SIyama 'wacce ke zaune gefe jikinta A sanyaye domin ita kanta tasan ba ta kyauta ba"""to Amma Ai yarinyar ita ta jawowa kanta Don haka ko gobe 'ya kara cewa ta mareta sai ta mareta''domin ba karamin tsanar yarinyar tayi ba

Ummi tace " haba Siyama ko kara babu 'ki daddage ki dinga Marin yarinya iye"?

Cikin jin kunya Siyama tace "Ummi kina jin Abinda yace fa cayayi in ban mare ta ba zai sata ta mare ni''
Nasan tun da Ya fadi haka zai Ai kata. ''Kuma nasan halin ,Dija tsab zata mareni shiyasa"

Kwafa ummi n tayi tace " Ai shikkenan Kece A wahale tunda kece matarsa sai kije ki ta Abinda kika saba 'Amma ki sani shi namiji duk ta inda ka bida shi da haka yake tashi sabida haka sai ki . Zauna kiyi nazarin wane irin miji zaki Aura

Maganganu ummi tagaya mata masu A Lamar jirwaye me kamar wanka

"Insha Ummi zan Kiyaye da Abinda kina CE" Siyama tafada 'tana kokarin tashi daga gun

Kallon Nene tay tace '' ran uwargida na ya Dade kina ta gyangyadi A zaune kije ki kwanta mana"

Gyara zama Nene tayi A kan kujearar ida nunta A kan Siyama ''tace yanzu kuwa zan tashi "yar nan"

To "Ummi sai da safe Siyaman tafada tana Barin gun " cikin walwala da farin cikin domin ji take kamar wacce A kayiwa Al bishir da gidan Aljanna '

yau ta sauke baciran da dija take had a mata shiyasa take jin wa sai A cin zuciyarta

To Allah ya tashe mu lafiya

Karfe biyar shaura na Asubah Ali ya fito domin zuwa masallaci'sai da Ya tsaya ya tashi jamel sannan ya wuce masallaci'A can suka hadu da Abba

To cikin gidan ma hakane duk sunyi sallah 'sallahr Asubah bata wuce su 'sai Abba ya tabbatar da kowa ya tashi. Yake wucewa masallaci wannan shine Abu mai kyau *Allah kasa mu dace*

Anyi Anyi da Siyama taki tashi ba yadda Na'ima bata yi da ita ta tashi ba Amma taki haka ta hakura ta kyaleta ta koma ta yi kwanciyarta

Duk Abinda yake faruwa A'idon Dija domin da'ta idar da sallar bacci bai dauke ta. Ba sabida haka tana jin nacin ' da Na'ima take Wa siyama A kan ta tashi taje tai sallah taki tashi'

Sai da Ta tabbatar 'bacci ya dauke Na'ima' sannan ta'ta tashi Cikin Sanda ta nufi 'friji' da ke gefen gadon da Siyama' take kwance' ta' ta dauko Ruwan' gora mai bala'in sanyi Dan har ya soma yin kan kara ' ta ' bude 'ta dai dai ci' fuskar siyaman 'ta. Hau zuba mata shi

A gigice Siyama ta tashi 'tana rike fuskarta' domin ji tayi kamar An daura mata' kankara A fuskarta' sabida nauyin da ta yimata''

Dago fuskarta tayi ganin 'I nuwar mutum A tsaye A kanta me zata gani' Dija CE rike da robar ruwa A hannuta' ta zuba mata 'ido tana yi mata kallon ' wana kama

"Ke wane Dan iskan ne yace ki wa TSA min ruwan me kankankara A jikina iyi"?

Shiru Dija tayi mata bata CE komai ba' sai da ta kuma mai maimaitawa' sannan 'dijan ta magantu'

Kai tsaye Tace ''yaya Aliyu ne yace A tashi ki kiyi sallah ' kowa ya tashi yayi ban da ke wai Nan ba gidan 'Ar na bane''

Kan ta Siyama n tayo tace " zanci ubanki ''wallahi makaryaciya 'banza yaushe yaya'Ali yashigo da zaki 'masa karya' yau zanga uban da ya tsayamiki A gidanan"

"Wallahi badai ubana Ai uba baifi uba ba Dan 'haka A dai na zagar min iyaye na domin 'ni nasan Mutum cinsu"

Cikin bacin rai' Siyama ta kaiwa DIja wani ba hagon mari tana fadin ''Dan uwarki ' karki sake hada 'iyaye na da naki domin 'iyayena sunfi Naki komai jahilar yarinya 'yar kauye kawai"

Saurin kaucewa Dija tayi 'Marin da Siyaman'ta' kai mata ya bi iska ma tsawa tayi baya ta tsai da idanunta kan Siyaman ' sannan tace "Ai mun San komai 'Ai fa'iza tace ma dady' din naki ma Dan 'Aiken Abbah ne' kullum sai yazo Maula gun Abbah"

A fusace Siyama ta nufi 'Dija ta rufe ta 'da duka ' ko 'ta 'INA

Ihu Dija take kurma wa' na ne man dauki

A gigice Na'ima ta tashi tana mutsika ido ' tana son taji daga INA take jin kuka' sai taji kamar kukan 'Dija

"Wayyo ya Na'ima zata kasheni ki CeCe ni''

Saurin kallon gadon Siyama tayi 'domin A nan ta me jiyo kukan

Me zata gani Siyama CE ke ta faman dukan Dija babu ji babu gani

Da A zama Siyama ta karasa gun tana Kokarin ' janye Dija wacce ke kawance kasa tana kokarin shigewa kar kashin gado 'ita kuma 'Siyama ta kama gashin ta 'ta rike sai faman ja take' ita kuma. 'Dija' sai zaginta. Take ta Uwa Ta uba

Ba zato suka ga 'Ali A gabansu Dan dukan su ba su ji shigiowarsa ba

Kallonsu ya ke daya bayan daya 'fuska babu Annuri ko kadan

Ga Siyama rike da gashin Dija A hannu tayi tsili ttsili ' ita ma dijan tsuru-tsuru tayi tana zare 'ido min har yanzu bata gama watsakewa daga dukan da ta Sha jiya ba

Kallon Na'ima yayi wacce ke tsaye ita ma tana zare ido 'yace me ya hadasu"?

Bakinta yana rawa tace "wallahi bansani ba ma nima bacci na ke yi suka ta she ni"

Mai da kallonsa yayi kan siyama wace har yanzu kan Dija yana rike A hannuta ta Kasa saki

"Me ya hadaku"? In da In da ta fara ''um ''um zuwa tayi ta watsa min ruwan sanyi ina bacci " ta fada cike da rashin gaskiya

hannuta ya kalla Wanda ke rike da gashin Dija' yace ' " cika mata kai '' cikin Sauri ta saki kan don ita ta manta ma tana jama Dija gashinta

"Me na CE dake jiya iyi"? Ke wace irin mace CE Mara kamun kai yanzu ke baki ji kunya ba kina fada Da kanwar,kanwar Ki"?

Sun kuyar da kai siyama tayi " Tace 'kayi hakuri' bazan kara ba'' banza yayi da 'ita 'ya mai da kallonsa kan ' Dija fuska A hade yace "wato ke ba kyaji ko? Meya sa kika watsa mata ruwa 'A jiki iyi"?

Cikin kuka tace ''ban wa TSA mata ruwa ba tashin ta nayi tayi sallah 'ganin kowa ya tashi yayi 'shine. Ta tashi take ta zagina na wai iyayena talakawa ne sannan "yan kauye ne ja hilai ne"

"Wayyo kai na yana yimin ciwo Dan Anga in marainiya CE shine A keta cin zalina Allah sai ya saka min " tafada cikin gursheken kuka Wanda sai da ta ga ,Alin ta kirkireshi

Ranshi yaji ya na masa zafi 'ganin yadda Dija take kuka 'ya tsani kuka A rayuwarsa ' sai yaji kukan da take yana taba masa zuciya

Kallon ta yayi yace " tashi daga gurinan "tashi Dijan tayi tana kuka A hannuta rike da Kanta ta nufi hanyar fita da ga dakin

" Cikin tsawa Ali yace INA zakije A haka dawo kisa Dan kwalinki "

Dawo wa tayi taje ta dauki hular rigar baccin da ta ke jikinta ta sa ,,ta kama hangar fita daga dakin

"Koma ki zauna " yafada A karo na biyu yana dauke ',,, ido daga kanta Dan wani irin yanayi yake ji A jikinshi in ya kalleta A haka ,domin kan shi babu Abinda yake birgeshi A jikin mace kamar ,gashi' da kyakyawar sura ,,to ya fuskanci duk yarinyar ta Tara A bubu wan gashi dai karama CE Amma Alamar karfi A Na ganewa

Kallon Siyama yayi fuska A murtuke yace "kina nufi har yaanzu baki sallah ba"?

Sun kuyar da kai tayi bata CE komai ba

Kwance blet din dake daure A jikinsa yayi domin dama cikin shirin fita yake ba zato Siyama taji saukar duka 'A jikinta 'domin kanta A sun kuye ya ke

A gigece ta dago kai tana kallon Ali ' kafin ta dawo dai dai ya kuma shinfida mata wani dukan

Dur kushewa tayi A gurin tana Sosa jikinta Dan ba karamin shiga dukan yayi mata ba bai bari ta gama watstsakewa ba ya kuma shinfidama ta wata

Sai da yayi mata sau shida masu Shiga jiki sannan ya kyaleta ' ya mai da blet dinshi ' jikinshi hankalinshi kwance,

Tana zaune A gun tana hawaye ya kalleta Fuska 'babu walwala yace " wannan shine hukuncinki na kin yin Sallah 'A kan lokacin ,daga yau A kuma tashin. Ki kiyi sallah ki ki tashi 'dukan da zan miki sai yafi wannan
Domin nan gidan musulumai ne ba na Arna ba "

Shiru Dakin yayi ba ka jin komai sai sautin kukan Siyama zuwa sannan lokacin gari ya soma wa shewa da ga duhun Asubah

Ko kallonsu bai kuma yi ba ya fice daga dakin yana Jan tsakii

Tsaki Na'ima taja bayan Ali' ya fice daga dakin ' tana kallon 'siyama' tace " wai me yake damunki ne sis"?

"Kamar ki ki tsaya kina fada da 'karamar yarinya kamar 'Dija wacce kuriciya ke da. Munta ' Ai ko wani Abin tayi miki ba kya yi kokawa da 'ita ba ' wannan Ai zubar da girma. Ne"

Wani kallo siyaman take wa 'Na'ima tace " A binda zaki CE.) Kenan kema"?

"To me kike so in CE bayan wannan 'iyi" ?

"Ba kiga irin ta shin da nayi miki ba 'domin kiyi sallar Asubah Ki ka ki kowa ya tashi banda ke

Ni kam 'Dija tayi min dai dai wallahi da ta wa tsa miki ruwan" Na'ima tafada hankalinta kwance Don bakaramin 'dadi taji ba 'ganin Ali ya Zane ta'' Tun ba'Aje ko INA ba 'Al hakin Dija yakamata.

"Kwarai kuwa Ai gwara ki nuna min cewar Dija Jininki CE dole ki fifita ta A kai na Na gode Na'ima " siyaman tafada Ranta A mutukar bace

"Ba haka bane sis , kece wallahi da A bin haushi 'A CE kamar ki bakya yin sallah A kan lokacin sai rana ta fito 'ko kunya ba kyaji wannan ba dai dai bane wallahi kinsa '',dole in gaya miki gaskiya 'domin haka tunda zaman Amana ne A tsakanin mu.....................
Chapter 23 · 0% Book details