← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 35

Sashe 5

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fuskarshi ya dago yai mata wani mugon kallo cikin tsawa yace kwashi kayannan kifita dasu waje kisa ,,tsayawa tai tana kallonsa itama da zanin a hannunta gashi daga ita sai dan wando ,,cikin wata tsawar yace" badake nake ba iyi cinki sauri ta dibi kayan ta fice tana kunkuni "aikin banza aikin wofi duk an zo an takurawa mutum kawai,,

Sa rai yaji abinda tace sabuda wanin irin kunne ne dashi mai bala in ji shiyasa bashida nauyin bacci ko yaya aka motsa a bu zai tashi,,

Girgiza kai yai yana mamakin halin yarinyar baita ba ganin mara kunya irinta ba ,,shikam tunda yake babu wanda yataba yimasa rashin kunyar datake masa to yaushema ya shiga sabgar mutum bare haka ta faru ko cikin abokai baifiya sakin fuska ba gudun raini ballanta na kannasa dasuke bala,in jin tsoronsa ,,

Kwafa yayi aransa yace zakici ubanki wallahi saina gyara miki zama ni ba,akawo min raini

A fili kam shiru yai yai kamar baji abinda take cewa ba ya ciga ba da abinda yake aransa shiyasan abinda ya shirya mata,,
.
Tana gama sa uniform din cikin sauri ta karbi kudinta gurin nene da ke faman aikin kosai bayan tagama hada kunun kamshi sai tashi yake

Tace "sai nadawu nene,,,to kiyi sauri ai da sauran lokaci ai

Nene kam bayan tagama hada komai ta jera kayan karin a babban faranti ta nifi da kin dashi,,

Yanan dai still inda yake zaune sa6anin dazu da yake daddane dane a waya ,,yanzu waya yake da ogansu akan fara fita aiki da zasu fara ranar mondy ta sama

Kallonsa tayi tace aikin ke nan latse latsenn waya ko gajiya bakai tashiga zuba mai kunun" to gashinan sai ka sako in kuma kabarshi ya huce kasan badadi zaiyi ba ,,kanta rufe bakinta taji sallamar dija,,

Tashigo dakin "wallahi nene anfara dukan makara yanxu naga sa,a itama ta ke gayan nidai bazani ba ta fada tana turo baki ,,nene kam cewa tai ai shikkenan sai kizauna gobe kyaje ,,

Ali kam kallo ya bisu dashi yana hararar nene domin shi nene n ce ma tabashi
haushi ba dija ba,, fuska a ya mutse yace mayar da kunun cikin fulas yafada yana kallon nene ,,

Baki tabude zatayi magana taga ya mike tsaye ,a,a inazaka kuma ehe ?tafada tana kallonsa kaifa kace zakasha kunu bagashi nayi maba,,

Ai zansha tashi muje yafada yana kallon dija ,,kallonsa tai tana zare ido cikin tsawa ya kuma mai maitawa
Cike da tsoro ta mike tai waje shima ya rufa mata baya

Nene kam baki tasaki tana binsu da kallo har suka fice daga gidan

Tana gaba yana binta abaya har suka je makarantar yai mamaki da yatarar da wasu daga cikin da libai a n tsare su sun makara ,,dija tana bayansa sai faman zare ido take dan arayuwar ta ta tsani duka gashi malamin zafin hannu ne da shi mai musu taran makara,,

Sallama Ali yai wa malami tare da mika mai hannu suka gaisa ,,sannan malam siraja yakai dubansa ga dija dake bayan Ali a 6oye,, yace " a,a Khadija kekam kin saba makara dama, in yau kin makara gobe kizo akan lokaci wanan bashi ne himma ba,, ya kai dubansa inda Ali ya ke yace" malam tare kuke ne da,ita,?,

Ali yace "eman ga tanan ku zane mata jikinta yadda ya kamata domin bata fi sauran dalibai ba ,,

Dija kam in banda hawaye babu abinda take haka tana ji tana gani Ali ya sa aka zane ta dan dukan da ake mata yafi na makarar da tai sai da yatabbatar an zane mata jiki sannan yai wa malami sallama yakama hanya yai tafiyarsa ko ta kanta baibi ba ,,

Haka dija tashiga aji ranta abace tana ji duk duniya bata da makiyi irin yaya Ali
Sai taji wata irin tsanarsa a ranta ganin irin kiyayyar dayake nuna mata ,acewar ta dan yaga bata da uwa bata uba shiyasa yake mata haka ,,dan duk da kananin shekarunta tana sane da wanda yake nuna mata kulawa da kauna,,

Shikam Ali bayan yakoma ,,ya tarar da nene tayi shinfida a tsakarkida da redi,o tana saurarar tashar freedom cikin shirinsu na barka da hantsi,,

Kallo tabishi da shi bayan ta amsa sallamar da yayi ,,samun gefe yayi kusa da ita ya zauna tace" rakata makarantar kayi tafada tana kallonsa ,,cikin yanayin sa daya yasaba yace "ehe ina kunun yake ? tace "yana dakin inda kabarshi sai katashi ka dauko da kanka bai ce komai ya mike ya shige dakin,,

Zama ya tsiyayi kunun yafara sha da zafinsa dan kamar yanzu a ka yi da,ike a cikin wata irin kula yake mai bala,in rike. Zafi hakama kosan da ya bude kular da aka zuba sai turiri yake kamar yanzu aka tsame,,humm nene badai iya girki ba jin wani irin kamshi yana tashi ga wani gardi da kunun yake yi,,

A gaskiya ya ji dadin kunun dan rabonshi da shan irin shi tun kafin yabar kasar yatafi karatu ,,,

Hamdala yai bayan yagama karyawa ya mike ya futu ,,samun nene yai tan dan kashin gida tana ta faman gyangyadi ga redio sai faman yi take kallonta yai yace" kedai bacci bayai miki wahala ,,to ai sai kigyara kwanciyar karki fadi yafada yana dan kara karfin redio dan tatashi ,

Tashi tai tana gyara daurin dan kwallinta tace" har kayime? kagama karyawa ne tafada tana kallonsa ,,yace 'ke zan tsaya jira ai wai kin ma karya kuwa naga kinzo kinata faman gyangyadi sabudu yasan halinta ita ma bakasafai tafiye damuwa da abinci ba,,

"Tun yaushe ai kuna fita nakarya yaushe zantsaya jira,,ince ko bakasa an dake taba tafada tana gyara zama sosai,,

"To meye amfaninta ai batafi sauran yara ,,yan makarantarba yafada yana ya mutsa fuska ,,

Kwafa tayi tace "ai shikkenan kaji dadi an daketa sai kazuba ruwa a kasa kasha tafada tana harararsa,

Shiro yai mata yace " zanje in yi wanka zan dan zagaya mugaisa da "yan uwa ko,,

Dariya tayi "da ko ka kyauta wallahi dan kwanaki baba furera take tambayar ka kaga sai kaje ku gaisa ko ta fada tana washe baki ,,yace "to ai matsalar bazan iya gane gidan ba kinsan najima banjeba ai kam dai abu mai sauki kabari dija su taso da ga makaranta sai taraka ka gdan ,,,

Gidan bawani nisane dashiba ma dan dai bazaka gane bane,,

Wani irin kallo yake mata yana dan ya mutsa fuskarsa wanda yazame masa jiki ,,yace "sai dai ke kirakani amman indai wacan yarinyar ce zata rakani wlhy bazan taba zuwa ba yafada yana kokarin barin gun cikin sauri nene tace "ai babu damuwa sai in rakakan,,sabida tasan halinsa sai yaki zuwa intace lallai in dijan CE zata rakashin baice komai ba Yakama hanyar shashin da ya sauka domin duk jin sa yake a ta kure wanka yake son yayi wani zafi zafi yake ji a jikinsa shikam bayasan zafi a rayuwarsa yafi son lokacin sanyi da lokacin damuna

Tsaf ya fito cikin qananun kaya da sukai masa kyau sosai Kafarshi sanye da takalmi mai gidan ya tsa Na fata Hannunshi daure da ahogonshi ,kamar ko da yaushe yana cikin qamshi turarenshi da ya bi jikinshi

Nene Na zaune kan tabarma tana gyara goron ta ta shirya tsaf cikin Atamfa "Yar engila riga da zani da dankwali hade da maya fin Atamfar ta tufe jikinta dashi staff!!

Tsayawa yayi yana duba a gogo ,A ya mutse yace"Sai mu tafi ko tunda naga kin shirya"

Ta dago kai tana kallonsa tace"Eh Na shirts ni kam D'ija za mu jira yanzu yanzu ta shiga bandaki zatayi Wanka"

Fuska babu yabo babu fallasa ,ya Nemi guri ya zauna gami da dauko wayarshi ya Na dubawa,

Dija kam bata wani Dade a bandakin ba ta fito ,,wani kallo Ali yabita da shi ganin ko minti biyar ba tai ba wai har tayi wanka a ransa yace wannan yarinyar kam anyi kazama dubi wai har tayi wanka wanan ai jika jika ne ,,kallon nene yayi yana ya mutsa fuska yace ai dama keki keyi mata wankan wannan ai babu abinda ta iya in banda ta tada dauda dubi wuyanta fa inda dauda hade da sabulu suke yafada yana nuna gefan wuyanta

Kallon ta nene tayi tana duba inda yake nunawa itama taga sabulun tace "ke dija ai ga sabulu nan abayan wuyanki baki wanke ba ,,

Zumbura baki dija tayi tace "wai ni ina ruwa na da mutum ne komai sai a dinga cemin kazama to anyi kazantar ta fada tana murguda baki ,,wucewa tayi daki batare da taje ta wanke sabulun ba,,

Nene kam shiru tai tana kallonta tace "wai ban hanaki mayarwa da babba magana ba waye sa,anki a nan,,

"To ai nene ni badake nake ba tafa da tana kukarin saka kayanta

Ali kam bai ce komai yana mamakin wannan rainin da tayi masa wai ai bada nene take ba tana nufin dashi take kenan

Fuska a hade ya kalli nene yace" kinji ko wai dani take ashe sabida ni sa,an tane?

Nene tace "ai sai kayi hakuri kanwarkace ai ku ma kaga kuruciya tana damunta"

Ya mutsa fuska yai yace "ki ka dai sangar tata amman in bahaka ba ni Santa ne da zata dinga mayar min da magana..

"To ai sai kayi wai kai bakasan yaro bane"? tafada tana tashi daga gun

Kwafa yai a ransa yace zaki ci ubanki indai kika shiga hannuna

Shima tashi yai yayi hanyar fita yace "in kun gama ina waje

Bai jira jin abinda zata ce ba yai ficewarsa,,

To haka dai nene tara ka Ali gidajan "yan uwa suka gaggaisa da juna anan take fada musu zasu tafi abuja jibi zata bi Ali zataje tayi kwana biyu tadawu

Sai a sannan dija ta san da tafiyar a ranta sai murna take zata je taga kawarta fa,iza wacce suke sa,annin juna da,ita da mutumin ta jamil

To sai wajan bayan la,sar suka dawu gida
Suna da wuwa ko sauransu bai yi ba ya shige shashin wanka yake son yayi sannan yadan kwanta ya huta domin dai nene tasha yawo dashi a cewarta tunda ya dade bai zo ba sai yaje ya gaisa da "yan uwa sosai
Chapter 5 · 0% Book details