← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 35

Sashe 7

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaki ya ja aransa hade da girgiza kai yace tabbas sai ya tasawa yarinyar nan atsaye kafin ta dai daita hankalinta

Dija kam bayan ta wanko bakin zama tai tafara cin abincin ,,tace nene baki samin manshannu ba,,kallonta nene tayi tace gashinan ai kusa dake ki tsiyaya mana

Manshanunta tacigaba da sawa kamar batai wani laifi ba hakalinta a kwance ta soma cin abincinta,,

Shiru gurin yai inbanda sautin ridio n nene dake tashi bb wanda y kuma cewa kala a gun

Yana gamawa ya mike daga gun yaje ya daureye sannuwansa domin cin tuwa dai dole sai da hannu kalla baice ba ransa a mutukar bace yabar gurin yana tunanin irin hukunci da zaiyiwa wan yarinyar ,,

Nene ce tace. Ina zaka naga kana kokarin fita ,,cigaba da tafiya yai yace zan dan fitane insha iska domindai itakanta nene haushi take bashi ganin duk da sa hannuta yarinyar tazama abinda tazama,,

Ficewarsa yai ko kallonta n taba baiyiba yayin datakecewa kai da ba kowa ka sani ba a garin iyi?

Shikam Ali a zahiri zama ne bayasan yayi inda dija na gurin dan ji yake zai,iya karyata ya zubar a yanda zuciyarsa take mai zafi ,,sbd ya tsani raini rainin ma daga yarinya karama shi abin ma mamaki yake bashi ,,ganin yaddasu na,ima da jamil suke bala,in jin tsoransa ko acikin abokai ne shi nada ban ne sam ba,a kawu mai raini amma abin mamaki wnn kazamar "yar bata shakkar ta zage shi a gaban kuwa,,

Lallai kam bazai dauki wann ba wallahi sai yayi mugun saba mata kammani in daishi ne ,,ahaka take so taje cikin jama,a tai tai musu rashin arziki tana zubar musu da kima wannan bazai yiwuba dole sai ya saita mata tunani

Haka ya gama zancan zucinsa da irin tanade tanaden a zabar da zai ganawa dija mudun tace zataje abuja da wannan haleyen nata

To nene kam daki tashige bayan Ali ya fita

Kokarin sauko da akwati take daka kan siff so take ta zuba musu "yan kayan da zasuyi amfani dashi ,,tunda yace gobe da wuri zasu kama hanya ,,

Ace warta bazata dibi wasu kaya dayawa ba tunda bawani dadewa zasuyi ba itakam tabazata wuce sati biyu zata dawu

Dija ta kwalawa kira dake tsakar gida gama cin abincinta kenan amsawa tayi tace "Nene menene?

Nene tace "zo ki tayani zuba kayannan acikin jakar nan gobe in sha,Allahu da wuri zamu tafi amma ki nikkesu akafin kisa domin sufi zama

Dija tace to fara zuba kayan tayi tace nene kala nawa kika ibarmin nawa kayan kuma yaushe zamu dawu iyi? tafada tana kallon ta

Ai bawani dadewa zamuyi ba baza mu huce sati biyu ba ,,turbune fuska dija tayi tace gsky nene in munje kar mudawo da wuri mubari sai andan kwana biyu kinji ta fada cikin shagwaba ,,nene tace ",inbanda abinki dija makarantar wa zaije miki ita

Dija tai sauri tace basai aje a fada ba,,

Shiru Nene tayi taci gaba da ninke kayansu tana zubawa cikin Akwati
D'ija ta marai rai ce tace"kin ji Nene. Dan Allah aje a fada"

Nene tace"waye zai je ya fada bayan lokaci ya kure"

Marairai ce fuska D'ija tayi tace "ba sai Haruna Na gidan baba malam yaje yafada ba"

Nene tace"to Allah ya kaimu
Ai ba wani dadewa zamuyi ba sati biyu zamuyi mudawo"

D'ija ta bata Fuska,tace"gaskiya kar mu dawo da wuri Nene Naji an ce garin yana da dadi"

Nene tace"sai kiyi kuma ni bazan je wata Abuja in share guri in zauna ba bayan ga dakina Na bari"
.zumbura baki D'ija tayi tana gyara kwanciya,sabida tasan halin Nene duk Abinda tafada ya sauna.

Ali ko yana shiga dakinshi Wanka yayi ,
Yayi shirin bacci ,sai ya zauna gefan katifarshi ya kunna loptp din shi yana duba sakkonin.

Duk yawanci sakkonin daga Abokan Aikinshi ne,mussaman ogansu,sai sakon Aminin shi Faruk yana kara jaddada masa dole gobe ya dawo domin Akwai wasu takkadu da zasu cike.

Sai sakon mutuniyarshi Siyama ,
Yafara dubawa Fuskarshi a sake lokacin da ya duba wani sakon ta inda take fadin ,ya taimaka ya karbi soyyayar ta zuciyarta ta makance a kansa,Zara iya hakura da Aure har abada mutukar bai Aure ta.

Yarinyar tabashi tausayi ,sabida yadda ta damu dashi da rayuwarshi shi kuma kwata kwata bata gabanshi domin bata da tsarin da yake son Matar da zai Aura,yana son Mace doguwa mai Addini wacce tasan meye rayuwa ,bayan haka yana son Mace mai sharp da tsarin jiki mai kyau. Gami da gashi bayan haka shi duk wani kyalekyalen matan Zamani baya rudashi ,a cewarsa duk qazamai ne a waje zaka gansu tsaf tsaf Amma daga anyi Aure ,sai qazanta ,da rashin iya kula da miji
Shiyasa matan da suke burgeshi ,

Mai hafin Siyama Abokin Abbah ne tare suke harkar kasuwancinsu sun shaqo sosai har ta kai suna son su hada zuri'arsu Aure ,wato Siyama da Ali

Siyama sa'ar Na'ima ce kanwar Ali shiyasa tasu tazo daya,siyama Na yawan zuwa Hutu gidansu ,Amma sabida Ali take zuwa ,Wanda bai San tanayi ba
Ashe ta cewa babanta soyyaya suke da Ali har sunyi Alkwarin Aure ,da ta kammala karatu zasuyi Aure ,Dady nta cikin farin ciki yasamu Abbah ya sanar dashi,sukaita farin ciki har dai suka saka lokacin daurin Aure duk ba tare da sanin Ali

WANAN KENAN

WACECE D'IJA?

Lawan Dai Kani ga Alh Bashir Mahaifin Aliyu Shine Mahaifin ta, Yayi Aure in da Ya Auri Wata yarinya mai suna Khadija nan bayan gidansu, babu yadda Alh Bashir bai yi ba a kan Lawan ya je Abuja,Zai Samar masa Abin yi,yace yafi son zama kusa da Nene,Dan ko da yayi Auran ma Colin gidan suka tare da matarshi Khadija,mai kirki kamar mijinta,Nene tana jin dadin Zama da ita Sosai Shiyasa duk wani Abu da tasamu Na ta ne

Cikin ikon Allah ,Allah ya azirta ta da ciki ,Nene ta riqa Murna,ta dauki son duniya ta dorawa cikin,

Cikin Khadija Na da wata takwas tafara wani irin ciwon Kai! Mai zafi,sukaje Asibiti likita ya Dora ta a kan Magani,

Yace ta rage Aikace Aikace yin hakan yana iya barazana da lafiyarta da ta jaririn.

To haka Nene ta hanata duk wasu Ai kace Ai kace Na gida ,ita take yi,

ranar wata laraba Khadija ta tashi da wani irin ciwon mara maitsanani lawan ya fita ,cikin daren yaje ya kira Nene,
Kallao daya tayi mata ta fahimci haihuwa ce,ta karasa cikin dakin sosai ta rirriqe ta ,tana mata sannu.

Ta kalli lawan tace"maza yaje gidan baba malam ya karbo rubutun nakuda(haihuwa)

Lawan ya fita da sauri yana addu'a Allah ya sauki Khadija lafiya,tabbas duk wanda bai bi iyayensa ba ya shiga uku,ganin yadda matarshi take shan wahala.

Ko minti goma bai yi ba ya dawo gidan hannunshi ruqe da rubutu a daure a farar leda yayi sallama ,gami da mika wa Nene rubutu,sannan ya ja ya tsaya bakinshi dauke da addu'o i na fatan Allah yasa ta haihu lafiya

Cikin ikon Allah Khadija na shanye rubutun ta haihu ,Nene tai yiwa Alkah godiya ,sannan ta dauke jaririyar ta nan nade a zani,sai ta dawo kan Khadija,tana yi mata dabaru domin a samu nahaifar ta fado,

Khadija sai nishi take na wahala tsawon awa daya da haihuwar ta mahaifa taqi fadowa,

Nene hankalin ta ya tashi ,ta kira Lawan ,wanda yake waje a tsaye,

Ya daga labule,kafin tace wani abu,yace"ta haihu ne"?

Nene tace "e ta haihu"

Cikin farin ciki yace"Nene mai a kasamu"?

Cikin tausayi Nene ta kalli Khadija dake durqushe tana nishi! ga jini ya tsinke yana zuba mahaifa bata fado ba.

Tace"macace maza kaje ka samo mana mota mutafi asibiti mahaifa taqi fadowa"
Nene ta fadi maganar
Cikin qarfin hali,domin ta gama sarewa da lamarin ganin yadda khadijan take ta salati tana rirriqeta

Lawan hankalinshi ya tashi,ganin yadda hankalin mahaifiyarshi ya tashi ya fita da sauri,

Nene tayi iya kokarin ta amma abinda Allah ya hukunta babu makawa sai ya faru, ana kiran sallar farko Khadija ta amsa kiran Ubangiji rai yayi halinshi.

*innaliliahi wa'ina ilaihi rajinun*

Shine abinda Nene tariqa maimatawa ta gyara gawar gami da lullube ta da zani, ta fito daga dakin tana wa Allah tasbihi gami da nemawa Khadija rahamarsa.

Tun a hanya jikinshi yayi sanyi zuciyarshi tana tayi masa saq-saq hakadai suka karaso kofar gidan dashi da mai motar.

Zai shiga gidan keken yaga Yayar Khadija da wasu daga cikin danginsu sun tawo suna kuka, daya daga cikinsu tace"Lawan ya mukaji da hakuri ,Allah ya jikan khadija

Bai ce mata komai ba ya sakai ya shiga gidan gabanshi yana faduwa

Ko da ya shiga gidan Nene na tsaye tsakar gidan ita da wasu mata duk sunyi jigum jigum yace" Nene ga mai motar nan"

Nene tace"ai ta samu sauki ma ,Allah ya amshi abinsa Lawan kayi hakuri kaji ko Allah ya jikan Khadija"

Lawan ya rika salati jikinshi sai karkarwa yakeyi ya bude dakin da Matartashi take kwance,ya ganta a lullube da zani,sai ya tsuguna kusa da ita ya bude fuskar yana kallo tamkar mai bacci haka ya gani innallilahi wa'ina ilayi raji'un kawai yake fada a zuciyara yace"yanzu Khadija kin tafi kin barni,Allahu akabar,zama yayi ya rika yi mata adduoi har a kayi kiran sallah,asubah ya fito ya daura alwala ta nufi masallaci,

Duniya kenan ,haka a kaiwa Khadija suttura a ka kaita gidanta na gaskiya, sai bayan sarakar bakwai ne sannan Alh Bashir yafara shirin tafiya shida iyalinshi a lokacin Ali na Engila karatu,sai waya a kayi masa,gaskiya yaji mutuwar auntyshi sabida yadda jininsu ya hadu da ita in yaje gurin Nene tayi ta hidima dashi ,yana son mace mai hankali da fahinta da tsafta shiyasa suke shiri da ita sosai,nan dai yayi mata adduoi na Neman rahamar Allah

Alh Bashir yayi yayi da Nene tabashi baby su tafi tare da ita ,Ummi ta hadasu tare da yarinyar ta da take goyo a lokacin Fa'iza ta shayar dasu Nene tace Sam a kyale mata ita zata iya kula da ita,babu yadda ya iya haka sukaje asibiti a ka Dora baby kan madarar da ta dace da ita ,sai da ya tabbatar ya ajiye musu komai na bukata sannan suka wuce abuja tare da iyalinshi,
Chapter 7 · 0% Book details