← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 35

Sashe 4

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya tabbatar komai ya kammala sannan suka tafi bayan yadada kwantarwa da kanin nasa hankali ganin yadda kanin nasa ya koma lokaci qan kani,,,,,

Duk wnn abin da yafaru Ali bayanan yanaca london karatu sai dai waya yaji komai shima yaji mutuwar auntynsa ,,sabida yana mutukar kaunarta ,,

Haka kawai Allah y hada jininsa da ita ,,a rayuwarsa yana san yaga mutum mai tsabata wanda yasan meye rayuwa ya san abinda yake,,,

To khadija duk tana da wnn halin

Haka yai mata adu,a acan ,amma yaji mutuwar sosai

To nene haka taciga da rainan dije tana bata kulawa yadda ya kamata ,,tai bala,in shagwabata batasan Bacin ranta ,,duk abinda tayi daidai ne a gunta gashi zataje tai tsokana amma in aka doke ta tace anci zalin mairaniya ko makaranta dije batasan zuwa saitace wai dukan ta,ake ita ko nene sai tace tai zamanta,,,

Lawan har yagaji ya zuba musu ido dan baya iyawa da bala,in nene in dai akan dije ne,,,

Allah sarki rayuwa shekarar dije hudu Allah ya karbi ran lawan ,,ranar wata juma,a da dadddare ciwon ciki farat daya,,

Wannan mutuwa ta lawan ta gigita Alh bashir da nene ,,to ya za,ai haka duniya take dama,,

Dije tazama marainiya gaba da baya bbu maihaifa ,,

Nene kuwa tace ,,yan nan bazakiyi maraici ba indai ina raye,,

To ko da Alh bashir yazo bayan an share makoki bayyada bayi da nene ba akan tazo su tafi can abuja n amma nene tace bata zuwa haka yahukara ya kyale ta suka tafi sai dai duk wani abu na more rayuwa yana siyar mata ya a ajiemata kan yatafi shiyasa bata da matsalar komai na rayuwa ,,sai dai lokaci zuwa lokaci yan kazo ya ganta ko yaran su zu hutu ,,

Acikin wanan lokacin Ali ya dira a gidan bayan ya kammala karatun sa yadawo gida,

cigaban labari,,

Ali kam yana barin gun dakin da yake sauka yashige da,ike babu abinda bb aciki toliet ya shiga ya watsa ruwa dan wani irin zafi yake ji a jikinsa duk da cewa yanayin garin akwai iska tunda lokacin damina ne gari yayi sanyi ,,shikam Ali ai baya wani gane da zafi ko bazafi sai yai wanka sau hudu a rana a kamar wata mace,,,

Yafi to yayi shirinsa na bacci ya kwanta bayan ya feshe ko ina da turare a dakin ,,nikam nace asuba tagari Ali,,

Nene tashi tai bayan tagama sabgoginta agun ta shige daki tatarar da dije ta jima da yin bacci ,,gyara mata kwanciya tai ,,itama tai shirin kwanciya,

To da safe da Ali yafito bb kuwa a filin tsakar gidan ,,kallo yabi gurin dashi ganin ko ina a share tsaf tsaf wata irin isaka sai kadawa take ,,aransa yake fadin nene sarki n tsafta dubi har ta gyara gidan ,,shikam yana son mace mai tsafta a rayuwarsa ,,shiyasa yakewa matan wannan lokacin kallo hadarin kaji sbd acewarsa bbu abinda suka,iya sai soyayya da iyayi a waje amman da anyi aure sai su canja hali a cewarsa matan da sunfi iya kula da miji da tattalinsa shikam zai jima bai aure ba wallahi dan bazai iya da wannan shirman ba,,

Motsi yaji abayansa dan wai wayawa yai nene ce tafito daga kicin hannunta rike da fulas ,,kallonsa tai tace katashi ashe nazata kana can kana faman baccin naka daka saba ,,

Baice mata komai ba sai bata guri da yai ta wuce,,bin bayanta yai ganin ta nufi dakin ,,tsayawa yai a bakin kofa yana karewa dakin kallo yana ya mutsa fuskarsa ,,kallonsa nene tai tace " kashigo mana ka karya ka tsaya anan ta fada tana kokarin hada shayin tanayi tana tashin dije da ga bacci ganin lokacin makaranta yayi tunda ,,asabar ce akwai isilamiyya da take zuwa asabar da lahadi,,,

Kallonsa takuma yi tana hararsa tace "wai bada kai nakeba katsaya a bakin kofa kashigo daga ciki mana ,,

Ya mutsa fuska yayi a karo na biyu yana kuma kallon dakin,, yace" wai ina kike nufin zan zauna inna shigo duk guri a hargitse ehe yafada yana kallon ta,,

Gyara fuska nene tai sabuda tasan yanxu zai fara yima ta feleken nasa ,,tace gwani sarkin tsafta baka ganin dije bata tashiba iyi duk fadin dakinnan karasa inda zaka zauna sabida tsabar neman magana irin naka tafada tana hararsa,,,

Kallonta yai ya kalli gadon da dije take kudindine a,ransa yace au sabida wannan yariyar taki gyara dakin kenan dan kar tatasheta daga bacci kwafa yai ransa ,,,

Yaga sai wani lallabata nene take gurin ta shinta daga baccin,,

Shigowa yai kamar gaske ,,ya daki gadon da mugun karfi ,,ba dije ba da take gadon har nene sai da ta firgita dije kam tashi tai zata kurma ihu yai sauri yarike bakin,, sauri tai tadago kai ganin mutum tai kikam a kanta dan ita har ga Allah ta manta yazo garin ma,,

Murtuke fuska yai yana kallonta still hannusa yana rike da le6enta sai mutsika shi yake cike da mugunta!!dije kam ido ya raina fata in banda hawaye bbu abinda take,,

Nene sai masifa take "Ali kakiyane kasakar mata baki ,kai duk wani nau,in mugunta ka,iyashi ,,akwai wanda yafi soja muguntama tafada tana gyara zama!

Ali kam ko kallon nene baiyi ba sai da yatabbatar dije ta yi laushi sannan yasaki bakin hankalinsa kwance ya tsallake can kuryan daki yasamu guri ya zauna hade da ciro wayarsa ya hau danne danne babu abinda ya dameshi,,

Dija kam tunda tasamu ya sakarmata bakin take ta wani irin kuka tama kasa magana sabida tsabar zafi da vakin yake mata bbu bakin rashin kunya su dije nene kam inbanda harara babu abinda take makawa Ali ,,,

Yana kallonta ta gefen idonsa murmushi yayi yace nene kenan,,indai akan wannan yarinya ne zata iya batawa da kowa ya fada ransa ,,yacigaba da danne dannesa babu abinda ya dameshi yana ji nene tana ta aikin rarrashin ta amma kamar kuma zugata ake,,

Kallon su yayi ya kalli dijan fuska a hade yace wallahi kika sake Nazo gurinnan sai naci ubanki uban me aikaimiki iyi? yafada yana ware mata idonsa gaba daya

"Wai kai Ali me yarinyar nan tai maka kabi ka tsan gwameta ,ehe kai ko tausayin ta bakaji nene tafada tana kallonsa ,,

Tambayar kanakeyi?
Ta kuma maimaitawa

Kallonta yayi cikin ya mutsa fuska yace "menene abinta tausayi an an ai tausayin kenan ,,yafada yana cigaba da danne dannesa a waya ,,

Haushi ne yakama nene batasan sanda ta dauko mifici dake kusa da ita ba ta saita ta jefa masa caraf yarike mificin kan ya sauka ajikinsa yana sakin murmushi ,,wai shi nene zata jefa batasan tun lokacin da ta dauki mificin ba yaganta,,

Yace "jifa na zakiyi akan nagayamiki gskiya,,

Cikin fushi tace " banasan gaskiyar nace banasan gaskiyar tana yi kamar zata kaimai duka ,,baisan sada dariya ta su6uce mass ba yadinga yi sannan yace "kafin kidakeni bari kiga abinda zanyi yanzu nan

Miqewa yai yai kan dije gadan gadan ,,ai kan kace katt dije ta fincike daga hannu nene tayi waje tana faman rusa ihu kamar wacce aka kona da ruwa zafi!

Cikin zafin nama nene ta mike itama tayi waje tana sababi "kai wannnan masifartaka ta isheni wallahi zansamu basiru ai yai ma Katanga da dije dan wallahi wataran karaunatata ba yadda yanyiba ehheee!! tafada tana gyara daurin zaninta

Ko mawa yai ya zauna daga inda yatashi dama barazana yai musu amma baida niyyar sake dukanta,, yana jin nene sai faman surutai take a kansa ,,yai mata banza,,

Dija kam wanka ta shiga bayan nene tahada mata ruwar wanka ,aranta sai Allah ya isa take masa ganin har yanzu bakinta bai bar zafiba

dakin ta koma ta taddashi a zaune a inda yake bata ce masa komai bah tashiga gyara gurin,,

Cikin maganar sa ciki ciki kamar bayan yi yace "nene kimin wannan kunun naki mana na gyda na dade bansha irin shi ba,, yafada hankalinshi na kan wayarsa,,

Banza tai dashi ta cigaba da abinda ta ke yi ,,shikam Ali yasan sarai taji abinda yace ,,shima sai ya share bai kara cewa komai ba ya ciga ba da hira da abokinsa ,,faruk. Wanda yake ce masa yau she zai dawo ne ??

Dija ce tafito daga wanka daga ita sai daurin kirji cikin sauri ta ke kuma wanke bakinta duk da cewa ta wanke da asubah kafin ta yi sallah ,,

Sai sauri take ganin ta kwas har ta wuce gashi takwas din suke shiga Aji duk wanda ya huce takwas kam sai an dake shi,,, ita kuma tana balain tsoran doka , gaskiya,
.
Dakin tashiga ta tsaya gefen da nene take ta ce" nene na ga kamar ta kwas ta huce nidai bazaniba wallahi kinsan in mutum ya makara dukan sa ake tafada tana zunbura baki ,,

"A,a dija ai ta kwas din yanzu tai ki sauri kisa kayan makaranta in kikayi sauri bazaki makaraba"nene tafada tana kallonta cikin rarrashi

Sake zumburu baki tayi ,tace "ina uniform din nawa yake ??

"A,a fara karyawa tukun gashi na hadamiki shayin ta mikamata ka yan shayin ,,zama tai tafara sha cikin sauri,,

Tashi nene tai ta dauko mata kayan makarantar ta ajiye mata kusa da ita "gashinan da kingama sai kiyi sauri kisa ,,dadinta ma makarantar babu wani nisa ai,, tafa da yayin da take niyar fita daga dakin so take taje ta daurawa wancan fitinan ne kokon da ya ce ai masa

Ali kam duk abinda sukeyi yana jinsu hankalinsa ya na kan wayarsa ,,

Dakin yai shiru kamar babu kowa aciki dija sai sauri take tayi tagama ta fita dan ita yanzu tsoro ma ya ke bata ,,ganin kullum fuskarsa a murtuke babu fara,a ga muguntar tsiya ,,bakamar dan uwansa ba jamil. wanda shi yana sakar mata fuska yai ta janta da wasa da dariya,, shiyasa suke shiri da nene

Tana gama shan shayin tashi tai tafara kokarin kwa6e zanin daya ke jikinta wai tana so tasa kayan makaranta,,yana kallonta ta gefen ido ,,
Chapter 4 · 0% Book details