← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 35

Sashe 19

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kallonta Fa'iza tayi tace to " Nene ai naji abbah yana gayawa ya Ali ranar da yaje zai tawo da ku cewar in kika zo bazaki koma can ba sai dai kidinga zuwa ziyara
kuma ma ai dazu abban ne yace wa dija zai sata a skull dinmu kinga sai mu dinga tafiya tare "Fa'izan tafada cike d kuruciya da yarinta

wani kallo nene takewa Fa'izan tace " tashi kibani guri ai ban ga wanda zai hanani tafiya ba to kaji"!
"ai nasan tunda naga Ali yana wannan murmushi nasa nasan da abinda ya taka zai zo ya sameni ai"

Tashi Fa'iza tayi da ga gun tana cewa "dama kinyi zamanki anan to in kin kuma can din ma me zakiyi"

Carbin dayake hannunta ta ke kokarin caula mata tace "wuce kiban guri shakkiyar yarinya kema sun koya miki ko kina yawo sumumu dake to ubanki zan koma nayi acan din"

cikin sauri Fa'iza ta kauce da ga inda take tana dariya tace "Allah ya baki hakuri ni dai in kince dole sai kin tafi to kibar dija anan don Allah"

banza Nene tayi da ita ta cigaba da laziminta

to koda Fa'iza ta koma dakinsu Dija ta tarar a kwace yayin d Na'ima da siyama ko wacce take abinda ya dameta Na'ima dai waya ce a hannuta kunneta mane da eir pic Siyama kam loptop dinta take dubawa

kallon Dija tayi bata ce komai sannan ta mai da kallonta kan Na'ima tace " ya Na'ima kije ki rarrashi Nene don Allah tabar Dija anan tace wai bazata barta ba"

kallonta Na'imma tayi tana rage volom tace "me kikace ne?"

sai da Fa'iza ta kuma maimaitawa sannan Na'ima ta kalli inda Dija take kwance tace "au shine dalilin da dama take wa mutane ihu a gida tun dazu taki kula kowa sai faman bacin rai take"

"eh Ya Na'ima don Allah kije in kuma taki kigayawa ya Ali nasan zai iya hana ta tafiya da Dijan"

dariya Na'ima take tana kallon Dija n tace " to wai ita bata da baki ne ke kike aron bakin nata kici mata albasa in tana so kwai tabari ya Ali ya dawo sai taje da kanta ta roke shi nasan tunda nene ta kafe cewar .da ita zata tafi to kam ba makawa da itan zata tafi "tafada tana kara kallon Dijan ceke da tsokana

Dirowa Dija tayi daga gadon tayi tazo ta zauna gefen da Fa'iza take tana kallon Na'ima tace "dan Allah.ya Na'ima ki taimaka min nasan halin Nene in ta kafe akan magana ko Abbah ne yai mata magana da kyar ta yadda "

harararta Na'ima tayi tace "dazu wa ki ka gama zagi iyi"?

cikin dan zumbura baki As'usuel tace "nifa bada ke nake ba ya Na'ima"

kallonta Na'ima tayi tace " to dawa kike dan uwarki akwai sa'anki a cikinmu iyi"?

ba tarai Dija tayi don ta tsani a zageta dan dai kawai tana so taje ta hada Nene da ya Ali ne amma da sai ta ra ma ehe

sunkuyar da kai tayi bata ce komai ba sai da Na'ima ta kuma maimaitawa sannan ta dago kanta tana kallon inda siyama take zaune ta zuba mata ido domin tunda lokacin da taji tace bada Na'ima take ba ta bar abinda take tana kallonsu to dawa take yarinyar nan tana nufin da ita take kenan

kara kallonta Na'ima tayi tana kallon inda take kallo itama girgiza kai tayi tana mamakin yarinyar kwata kwata bata da munafurci wato tana nufin da siyaman take

Siyama kam ranta a bace ta juya tana cigaba da duba loptop dinta tana saqa irin matakin da zata dauka akan yarinyar

cikin harara Na'ima take kallon Dija tace "wai ke wace irin yarinya ce ne iyi"?

kin san matsayinta a gidannan kuwa to babu ruwana duk abinda ya biyo baya, ki ciga ba da zaginta da yimata rashin kunya wallahi babu ruwana in ya Ali ya ji domin matarshi ce kin san zaneki
zaiyi"

kara kallon Siyaman tayi tana dan harararta kasa kasa cikin ranta tace ya kasheni kar ya barni da rai na

A fili kam shiru tayi bata ce komai ba domin dai so take Na'ima taje takara lallashin Nene akan maganar dan haka shiyasa ta kyale ta itama

gyara kwanciyaNa'ima tayi tana kara kallon yaran sunyi mata tsoru- tsoru a gabanta wata dariya ce ta so ta kufce mata amma sai ta dake bata yiba tana mamakin kaunar da sukewa junansu sai taji sun bata tausayi don haka sai tace "ku tashi zanje in na tashi daga bacci kunxo kunyimin tsoru-tsuru agaba "

a tare suka tashi suka bar gurn cikin farin ciki suna cewa "mun gode ya Na'ima "

ita kam Na'ima kallon inda Siyama take zaune tayi tace "besty kiyi hakuri da abinda fa yarinyar nan tayi miki haka halinta yake wallahi muma bata kyale mu ya Ali kawai take dan jin tsoro da shakka shima dan yana cin ubanta ne"

murmushi Siyaman tayi cikin siyasa tace "haba Na'ima ai nima kanwata ce kuma akwai kuruciya a tare da ita shiyasa wataran in an ce tayi ma bazata yadda ba " tafada tana kallonNa'ima nan ko cikin ranta ita tasan irin matakin da zata dauka akan yarinyar don wata irin tsanar yarinyar take ji cikin ranta

dariya Na'ima take tace " yawwa matar ya Ali haka nake sonki da fahimta don haka daka ke babu wata cikin gidan ya Ali " wani murmushi Siyaman take domin tana jin dadin yadda Na'ima take kaunar al'amarinta da ya Ali shiyasa itama take sonta

ita kam Na'ima iyawa kawai tayi domin ta fuskaci Siyama saida siyasa shiyasa take mata ta "yan duniya itama domin a zauna lafiya amma tasan a zahirin gaskiya ya Ali bai son ta ita take haukanta

tashi tayi tace " bara naje gurin Nene
''

"Ok Siyaman tafada tana cigaba da abinda take

Samun Nene tayi a kwance a inda fa'iza ta tafi ta barta tana cigaba da jan carbinta

Zama tayi kusa da kafafun ta tana jan kafar A hankali ganin gyangyadi yana dan fuzgar Nene bude ido Nene tayi tana kallon Na'ima sannan ta tashi zaune tana gyara daurin dan kwalinta tace "ke kuma yaushe kika shigo "?

dariya Na'ima ta dan yi tace " yanzu nazo na tarar kina faman gyangyadi ke kam Nene bacci baya yimiki wahala wallahi " itama Nene da murmushi Akan fuskarta tace"Ai lafiya duk mutumin da kika ga yana yawan bacci to yana samun lafiya musamman kamar irin masu shekararun mu Anfi son su dinga samun i shashen bacci domin in ganta Lafiyar su , "kwarai kuwa Nene domin sukansu likitoci suna bada shawarar haka "Na'ima tafada tana kallon Nene

"yawwa Nene da Akwai maganar da zamuyi don Allah " Na'ima tafada tana kallon Nene A karo na biyu

itama Nene cikin kulawa tace "wace irin magana ce zamuyi "yar nan ki ke hadani da girman Allah "

dariya Na'ima tayi ganin yadda Nene ta hada hankalinta guri guda tana jiran taji zance

"dama kan maganar Dija ne don Allah Nene wai meyasa bakya son ki zauna damu ne ba fa kya zuwan mana da kinzo ma zaki ce zaki tafi don Allah ki zauna damu mu ma muna bukatarki anan"

kallon ta Nene take tace "wannan ce maganar dama ,? to in zauna inyi muku me na bar dakina nazo na tare anan can ma "yan uwa da Abokan Arziki suna bukatata" Nene tafada tana dada gyara zamanta hankalinta kwance

"mu munfisu bukatar ki wallahi muna so mudinga ganin ki kullum Nene" Na'ima tafada tana karyar da kai domin ta fuskanci in ba haka tayi ba Nene bayadda zatayi ba

"ke bazan zauna ba nace wai tashi kibani guri wato hada baki kukayi ke da "yar uwarki itama tazo tagama ke ma kinzo kina yi ko nace bazan zauna ba ehe!
shima Aliyu zai zo yasame ni domin ai bahaka mukayi dashi ba mutumin banza babu wanda zai sakani in zauna a wata uwa duniya "yan uwana suna can wani guri ni ina wani guri gashi suna bukata ta sosai sabida haka bari Abban naku ya dawo gobe zamu kama hanya mutafi na fasayin sati dayan dana ce zanyi to kaji"""""

kallon ta kawai Na'ima take tana kunshe dariya domin Nene sai wani masifa take batasan ko kasa da sama zata hadu babu wanda zai mai data sai dai in ta tafi ita kadai

"to tunda kin ce bazaki zauna ba kibar mana Dija anan don Allah" Na'ima tafada cikin rarrashin Nena

banza Nene tayi da ita tana cigaba da laziminta

ita ma Na'ima bata kuma cewa komai ba illah zubawa Nene ido da tayi

kusan minti goma babu wanda ya kuma cewa komai cikinsu ita Na'ima tana tunanin yadda zata bulluwa abin ne yayin da Nene take tunanin yadda zata iya zama ba tare da tana ganin "yan uwanta ba domin dai Nene maca ce mai zumunchi kusan kullum atafe take kai wa Jan kai was "yan uwa ziyara da Abin arzikinta shiyasa sukan su"yan uwanta suke ji da'ita domin tana tai maka musu ba kadan ba to a zahirin gaskiya tasan nan dinma suna da bukatarta to Amma gwara nan domin su Acikin dadi suke kuma basu ne mi komai sun rasa ba tasan Allah ne mai ciyarwa da shayarwa Amma mutanen da take taimakawa da abinci suna dayawa kama daga dafaffe zuwa danye.yanzu ya zasuji in sukaji zamanta ya dawo nan gabada daya

tashi Na'ima tayi tace "Allah ya huci zuciyar uwar dakina ni dai zan gayawa yaya Ali cewar kin ce bazaki koma ba kin fison nan yafi dadi dabida haka ke kar Asake a mai dake kano"

Na'ima tafada cike da tsokanar Nene itakam Nene bata ce komai ba har Na'ima ta karaci neman maganarta ta fice daga dakin

to har dare Dija taki kula Nene tasaki ranta tana walwala da kowa Amma taki zuwa inda Nene take

har Abba yadawo yagama sabgoginsa asama ya sauko cin Abinci Dija bata cewa Nene kala ba gashi An hadu a babban falon Anata hira cikin nishadi jameel sai tsokanar Nene yake yana dariya kowa sai dariya yake Amma banda Dija wacce ta kame Akan kujera tana faman zumzumbura bakinta
Chapter 19 · 0% Book details