← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 35

Sashe 11

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ummi tayi tace"kai ma kafada ai faruku"

Yace" ummi ke ce kike wani damu wa dashi yai zuciya ya nemo mata ai mai aure kowa ya huta sai ka wai yazo ya dinga saki wahala wallahi kidaina bashi abincin ki yayi girma da cin abincin gida,ehe"

Dariya ummi tayi tace "wai baka mai fada ne shi baya ganin kai har ka haihu ko zuciya bayayi ba shima ,,

Yace "ummi kuka tsaya wani lallabashi me ake jira wai tunda da matar a hannu mun she da sai kawai a shafa fatiha in yaso takarasa karatun a dakin nata ita siyama n,,

Wani irin kallo Ali yakewa faruk din yana faman harararsa

Shikam faruk dariya ya kara kecewa da ita sabuda yasan ya gamma kunna Ali ,,a sabili da yasan ya tsani ai mai magana siyama,n

Faruk yace "kinga bamu gaisa ba ma

Antashi lafiya" tace "lafiya lau ya hjiya binta " yace "tanan lafiya lau wallahi,,

Nene ce ta fito daga wani daki acikin falon bayan ta,idar da sallah kwanciya tai tana lazimi sai taji surutu yai yawa ita a tunanin ta ko jameel ne

Zama tai da carbin a hannunta tana kallon faruk tace "au! ummaru kai ne ka zama haka" tafada tana rike bakinta dariya faruk yayi yace "me nazama kuma nene,, dan sun saba da nene sosai tunda shi mutum ne mai yawan wasa da dariya shiyasa duk sanda nene tazo garin sun dunga fafatawa kenan,,

Tace "kazama wani burgujeje haka aikin sojan ya mai dakai iyi"

Dariya yai yace "nene kenan wace irin tsaraba ki kawomin ne?

"Wace tsaraba, wancan yabari mukayi yabi yadaga mana hankali wai ana neman ku gurin aiki ,,

"Aikam dai wallahi kinsan yanayin aikin namu wani aiki zamu fita muyi gobe shine dalilin da nai mai waya yatawo"

Nene tace "ai kuna kokari aikin ku akwai hadari sai dai muyi ta tayaku da ado,a Allah ya tsare mana ku

"Ameen ,Ameen yace "nene kunzo lafiya

Ya aka baro "yan uwa "??

"Kowa lafiya lau wallahi ya iyalin naka"? murmushi yai "yace sunan lafiya lau ai zan kawu su ku gaisa kan ki koma "

"Ai da ka kyauta kuwa ". yace " insha Allah"

Ummi ce tace" ai nazata bacci ki kayi da naji shiru ,,

Nene tace "ko daya baccin yaki zuwa kwanciya nai ina hutawa wallahi , wai ina jameel ne"?

Ummi tace "ai bai dade da fitaba yagama zaman jiran zuwanki ganin har daya tayi baku karaso ba shi ne ya fita kuma
Bai dade da fita ba kuka karaso,,

"AF ko da naji" Nene tafada tana kallon Ali da yake cin Abinci tace "kai kam haka ake babu tayi kayiwa mutane shiru iyi?

Banza yai mata faruk ne yasaki dariya yace " nene kenan ki rabu dashi ai akan an mai magana shine yake ci wa mutane magani

Aure kuwa mutum sai an masa, ko yaki ko ya so"

Nene tace " au ! maganar aure ne baya so tafada tana rike baki

Ummi da tun fara maganarsu bata samu su baki sai yanzu tace "ke ma kyafada nene"

Kallon Alin nene tayi tace "ina ce akwai matar a hannu to me ake jira ehe"

Shidai bai ce mata komai ba cin abincin sa yake cikin kwanciyar hankali,

"Ko akawo ma abincin ne faruk "?

"A,a ummi alhmdulilah wallahi kinsan da zanci bazan tsaya wani sai an tambayeni ba"

"Tace nasani ai naji kai shiru ne ai shiyasa na tambayeka"

Ali kam tashi yai daga gun bayan ya kammala cin abincin,,

Canja gurin zama yai ya zauna yana dan ciccin magani fuskar sa a hade

Da kallo nene tabishi dashi tace" haka dai sai dai aci a bar kayan a gun aci ai tusa kai ko kunya bakaji abokin ka har da da kai ka zauna kana faman iyayi "

Wallahi kamar kinsani duk cikin abokanmu shikadai ne yai saura amma duk muna d aure,,

"Rabu da shi ummaru nasan abinda zanyi bari abban nasu ya dawo in ya so sai inji me ,akatsa Ya jira "

Kansa dake sunkunye yana faman latsa waya ya dago yana hararar Nene fuska a ya mutse yace "mezakiyi to?

"Sai kaji abinda zanyi "

"To wai ke ina ruwan ki ne iyi" ya fada ya na kallon ta

"Da ruwa na ehe me kake nufi sai muzu ba maka ido ko to baka isa ba tunda kungama sasanta kanku kai da siyamar to gwara ai a gama"

Kallonta yai yace "wayace miki mun sasanta kanmu ehe?

"To wai ma ni nataba cewa ina son siyama ne da kuke ta wannan abin ya fada yana kallon ta

Baki nene tasaki tana kallonsa tace "au! Mu zaka kamayar kananun mutane iyi Ali"

Dariya faruk yayi yace" karya yake nene. Yana sonta yana san dai yai wasa da hankalinku ne"

Wani duka Ali yakaiwa faruk yace " wallahi zanci ubanka mara mutumci "

Cikin sauri faruk ya kauce yace "au dan nadafadi gaskiya shine har da duka"

Cikin Hayaniya Ali yace "dallah malam kai mana Shiru wallahi ko,in ballo ma ruwa kai kasan a inda zan je inyi dan iska kawai"

Tsaki ummi tayi tace" kana da aiki Ali wa kake so ka mayar karamin mutum iyi"? tafada tana kokarin tashi d ga gun

Umm !! "ke ma dai kya fada inji nene" itama tana kokarin barin gun ganin lokacin sallahr la,asar yayi tace" ai kamar ka auri siyama kagama. tokaji"!!

Wani Kallo Ali yakewa faruk bayan nene tabar gun,yace "wai kai wane irin dan iska ne ehe. Haka kawai za kazo ka 6allo min aiki"

Dariya faruk Yayi "yan isa ka biyu dai ni da kai nizaka kashewa waya dan rainin hankali kawai "

"Malam ina takkadunnan Iyi?

Banza Ali yai masa sai da ya kara maimaitawa sannan yace "sai katashi kaje kaduba d kanka "

"Wallahi sai Nafisa taji labarin Mufida tunda baka da mutunci "

"To taji mana angayamaka tsoranta nake yi ko an ce maka ita kadai zan aure"

Ali yace "haka kace ko?

"Eh man"

Wani murmushi Ali yasaki yace" zakaga aiki da cikawa wallahi banza mayen mata aure ko shekara biyu bakaiba har ka soma hange"

Cikin sauri faruk yadawo ya zauna yace. "Rufan asiri wallahi bana iyawa da masibar Nafisa don Allah kar kafada mata wallahi inta ji shikkenan na dai na bacci kishin bala,i ne da,ita"

Dariya Ali yai yace "me kagama cewa dazu iyi"?

Faruk yace " me nace kuwa ai bakarya nayi ba yaza,ai kadinga yaudarar yarinya alhalin tasaki jiki zaka aure ta kowa ya shaida sannan kace bakasan zancan ba"

"Nida bakina na ta ba ce maka zan aure ta?"

"Sai kafada meyasa tun farko abun ba kafada ba sai yanzu d magana tai nisa kace bakasan zancan ba ai kasan wa sane"

"To dan ubanka sai ka aura min ita tunda kai kahaifeni"

Dariya faruk ya kece da,ita yace "to wai mekake nufi ne da kaketa wani hanya hanya ne ,,kasan dai yarinyar nan bakowa take kulawa ba sabida kai sai kafadi dalilin da yasa zakace bazaka aure taba"

Cikin yanayinshi kamar koda yaushe yace "ba taimin ba shine dalilina" ya mutse fuska

"Baka,isa ba wallahi" inji faruk,

Cikin mamaki Ali ya kalli faruk yana mamakin rantsuwar da yayi yace " au rantsewa kake"?

"Eh inji faruk banga dalilin da yarinya zata bata lokacinta ba sannan daga baya wata magana ta faru bayan kasan wannan zai zubarwa da Abbah kima da mutunci acikin abokai dashi kansa maihaifin siyamar wannan zai iya jawo zumuncin nasu yayi rauni
Dan haka wannan maganar ma ka,ajiyeta a gefe Sam bata,taso ba" yakare magana yana mai da nuffashi.

Kallo sa ya ke yace " to dakake wani tada jijiyar wuya dole zakaimin ne ehe" yafada fuska a hade

"E dole za,ai maka tunda kai bakasan daidai ba"

Wani murmushi Ali yayi yace "na bar maka kaje kai tabiyu da ita tunda da ma amatse kake da mata dan iska kawai"

Harararsa faruk yai yace "eh naji laifine dan naso mata ai su ababen a so ne"

"Kar kai tunani bansan halin dakake ciki ba da irin magungunan da kake karba a gun Dr Hashim dan iska jarabbabe ai kai mata Biyu ne suka dace dakai domin mace daya bazata iya daukarkaba "

Duka Ali yakai mai yace "wallahi zanci ubanka har nakai ka "

"To kar ya aikai maka" faruk yafada yana barin gun yace "dallah zo ka dauko min takkadun inkama gabana"

Banza Ali yai mai yacigaba da duba wayarsa "wai ba magana nake ba bafanasan raini hankali kasan nawa halin inyatashi "

Mukulin shashin nasa ya jefa masa yace "malam kar ka isheni kadauka kaje kadauko da kanka mana "

"Daba a hannunka suke ba meye na da womin da su iyi kabi kazo kadamu mutane"

Kwafa faruk yayi bai ce komai ba ya dauki key din dakin yai fita sabida yasaba da halin sa a zuciyarsa kuwa shima shiyasan abinda zai kyokyoyamishi na rashin mutunci

Shiru falon yayi inbanda Ali da yake zaune yana fama d waya,,

Su Dija ne suka fito itada fa,iza suna faman kyalkyala dariya kwata,kwata ba su lura da mutum a gun ba sai da suka zo tsakiyar falon sannan dija ta ankara ,,tsaya wa tai tana gyara fuska fa,iza kam kai tsaye tibi ta je ta kunna tace " yanzu za,afara amma maimaici ne sai kokarin neman tashar a rewa 24 take ,,

Ita dai dija batace komai ba tana nan atsaye a gun,,

Jiyoyawarwa da zatai bayan tagama kunna musu kallon me zata gani ya Ali ne a zaune yana kallonta da fuska a murtuke

Cikin sauri tace ya ali anyi ni lafiya? "zo nan" ya fada batare da ya amsa gaisuwar ba jiki na kyarma taje ta zauna a gefenshi yace "me nagaya muku iyi"?

Shiro fa,iza tai tana zare ido yace" badake nakeba dan ubanki "

"Imm dama kace mudaina yawan kalle kallen da muke"

Wani rankwashin ya kaima ta cikin sauri fa,iza ta rike kanta

"Bayannan fa? Iyi " yafada yana kallon dija dake tsaye har yanxu a,inda take ,,hararar ta yai yace "tsayuwar uban mekikewa mutane anan gun?

Cikin tsawa yace "zo nan"
Chapter 11 · 0% Book details