← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 35

Sashe 27

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da suka gama hada komai guri daya sannan Aliyu ya saki dattijon mutumin nan wanda ya gama galabaita yana shirin faduwa kasa cikin sauri Aliyu ya tare shi kan ya kai yace kozu ku kama shi gaba dayansu suka zu daya daga cikinsu shiya sa6a mutumin A kafada suka kama hanya suka wuce

To su Aliyu ba subar gurun ba har sai da gari ya waye sosai suna kara nazarin gurin sai da suka tabbatar babu wanda zai dawo A cikinsu sannan suka bar gurin wannan shi ya nuna musu cewar su suke da nasara A tafiyar sabida haka cikin farin ciki suka bar gurin

To basu bar garin ba sai da suka yi kokarin kama mutanen da suka Aikata Abun cikin su goma sha shida sun kama mutum tara uku sun mutu hudu kuma sun gudu

Murna "yan uwa dattijon mutumin suka dinga yi tare da yiwa su Aliyu godiya dama su burinsu Kawai A daukarwa dan uwansu fansa

Haka suka sa su A moto suka dauki hanya bayan sun tabbatar da babu wani Abin tashin hankali da zai kuma biyo baya a garin

Wannan nasara da suka samu ta kara dau kaka Aliyu A gurin manyan kasa domin suma Abin yana damunsu ganin an kasa shawo kan Al'amarin da wuri sai gashi kan kanin lokaci yaron da ya fara Aiki ko sati daya bai ba shine ya kashe case din wannan Abin Alfaharine A gurinsu dashi kanshi Aliyun

Kan kace kabo magana, ta kan kama kafafen yada labarai tare da hasko Aliyu yana jawabi cikin tv game da nasarar da suka samu haka jaridu ma da sauran gidajen redio babu zancan daya ke tashi sai wannan

Su ummi suna falo dukannisu A nata hayaniya fa'iza gwanar kallo ta dauki ' remot tana kokarin canja tasha sai ga jameel ya shigo da sauri yace "ummi ba kusan me faruwa ko"?

"Meya faru" ummin ta fada tana kallonsa karbar remot din dake, hannun fa'iza yayi yana kokarin kama tashar da aka ce masa ya duba yace bara kigani fuskar Aliyu suka An hasko Ana ta faman dau karshi hoto "yan jaridu sunbi sun kewayeshi shi kuma sai faman bayani yaake musu cikin wani irin turanci sai kace wani A kasar waje sai ka rantse cewar black America ne sabida tsabar yadda yake turanci *nikam nace dama Aliyu ya iya turanci haka ko da yake ai kan Aikinsa yake kuma tsan tsar ba haushe ne shiyasa bai fi ya yin yaran nasara ba in ba kamawa tayi ba

Shiru falon yayi kowa yana kallon Aliyu cikin farin ciki ganin yadda Aka kewaye kowa yana so yaji ta bakinshi haka dai daya bayan daya suka dinga zan tawa da sauran sojojin tare da hasko fiskokin wadannan "yan ta Adda daya bayan daya tare da daukar hotonan su

Dija ce ta ta6o kafar fa'iza wacce ta zubawa tv ido sai faman farin ciki take tace "fa'iza bakya yiwa wancan mutumin da Ake ta haskowa A tv kallon sani gani nake kamar na san shi wallahi" tafada tana nuna Aliyu domin ita kam bajin turancin da suke take ba shiyasa bata fahimci me su ke cewa ba

Ga badayan su dariya,suke wa, Dija ganin da gaske take bata gane yaya,Aliyu ba cikin dariya Na'ima tace "ke kam Anyi "yar kauye wallahi, yanzu yaya Aliyu ne baki gane ba" da sauri Dija ta kuma kallon tv tana so ta tabbatarAikam shine tafada Acikin zuciyarta dama kyakykya wane Ashe ta ke tambayar kanta domin ita bata ta6a kare masa kallo ba irin yau ta6 tafada cikin ranta hade, da ta6e baki bata kara cewa komai ba' ta cigaba da duba book din dake hannuta

Ita kam Siyama wani irin dadi da da farin ciki ne ya lullu6eta tare da da dagawa tana me Alfaharin da cewar ,zata Auri Aliyu ko da baya santa Amma tasan in ta Aure shi tagama kashe boss din domin dole yaso ta ko da zata rasa zanin daura A doran duniyar nan kuma' ita kadai ke' da shi duk shegiyar datai gigin shiga tsakanita dashi saita sabautata ciki kuwa har da uwarshi wacce ta tsoguna ta haifesh

Kara kallon tv n tayi A karo mara A dadi tana murmushi yanzu friend dinta suna can suna can suna kallon Aliyu wannan ba karamin Abin Alfahari ne A garetaba

Wannan Abu yakarawa Aliyu daraja da mukami sabida namijin kokarin da sukayi gurin kawo karshen wannan badakala dake faruwa A can garin sai misalin sha biyu darabi na dare ya shigo gida kai tsaye cikin gidan ya nufa bayan yayi faking din motarsa A gajiye ya shiga dakinshi hannushi rike da tarkacen wayoyinshi da wasu muhiman abubuwan Am faninshi

Zube su yayi kan katifa shima ya zauna cikin gajiya bai yi tunanin shiga cikin gidan ba sabida ya san sun ruga sunyi bacci gashi coffe yake son sha sosai kwan ce takalminshi yayi yade da balle whatch dake daure A hannusa na zallar Azirfa A gajiye ya ke zare kayan jikinshi babu Abinda yake son yi sai wanka Amma ba zai samu ba sai yasha coffe tukunna da gashi sai 3qtaer sai karamar shart yanufi cikin gida ko ina shiru yasan duk sunyi bacci sabida haka kai tsaye kchin ya nufa da kansa zai hada cofee din

Kokarin kunna gas yake yakasa ya kunna Amma wutar tayi yawa sai faman tsaki yake rai Abace yakashe ya fita daga kchin din dakinsu Na'ima ya nufa kai tsaye domin dai Asabe mai Aikinsu tana can boys'Quoters bangaren masu Aiki bazai iya zuwa ya ta so ta domin da dafa masa ba

Tura kofar yayi fuska babu walwala yashiga yana kare musu kallo daya bayan daya so yake ya gano wa cece Na'ima domin dai shi kam bazai iya wani gane wace A cikinsu ba

Bubbuga gadon ya hauyi yana kiranta "Na'ima ke "Na'ima " shiru bata motsa ba kafarta ya ja yana kara kiran sunanta wani irin hannu Siyama taji mai sanyi da taushi taji yana ta bata in batayi karya ba kamar kamshin turaran ya'Aliyu take ji sabida cikin sauri ta yaye blanket din data lullube jikinta ta tashi zaune tana kallon inuwar mutum a tsaye A kanta wa zata gani yaya Aliyu ne ta6 tsuntsu daga sama ga shashshe tafada cikin ranta sabida haka cikin magagi irin na masu bacci ta mike a zabure ta yi kan sa ta makalkale shi tana ihu A hankali irin na munafurci wai ta tsorata

Wata Ajiyar zuciya Aliyu ya dinga sauke wa A hankali' tsigar jikinshi tana tashi ya sauke A jiyar zuciya' ta kai sau goma jin wasu Abubuwa masu taushi da yake ji tudunsu A jikinshi shiru yayi yana kallonta zuwa yanzu yasan wa cece A jikinshi ita ko Siyama jin yayi mata shuru bai ce komai ba sai ta kuma kama shi harda zagaya hannayenta A qugunshi tana faman shinshina jikinshi kamar wata mayya babu zato suka ga haske ya gauraye dakin cikin sauri Aliyu ya kalli gurun Dija ce A tsaye ta zuba musu ido cikin tsuru saura kadan fitsarin da ya matseta ta sakeshi a wando domin shiya tashe ta dama bin su da kallo ta dinga yi ganinsu a tsaye manne da juna idanunta A tsaye kan Aliyu tana kallonsa babu kiftawa shima ita ya zubawa ido yana kallo fuska a murtuke ita kam Siyama tasamu Abinda take so sai kara narkewa take A jikinshi bata san wainar da ake toyawa ba domin ta bawa
Dija' baya tunda idon ta A lumshe yake batasan ma Haske ya gaureye dakin ba balle ta Ankara da mutum A tsaye Aliyu ko yana sane ya kyaleta A jikinshi so yake yaga karshen jarabarta da iyakacin iskancinta sannan

Magana yakewa Dija da ido yana mata Alama da me yatasheta fuska A hade ta kallonsa take ido kir tana, mamakin Abinda suke tunda ita dai kullum in sukaje isilamiyya malaminsu yana fadar duk namiji da macen da suke ta6a junansu haramunne kuma "yan iska ne mutukar babu Aure A tsakaninsu hararasa ta hauyi sabida ta ga Abinda yake mata ko kallonsa bata yi ba ta wuce daga gurin tana faman zum6ura baki ranta A bace toliet ta shiga zuciyarta kamar ta fashe take ji tana kara tsanar Aliyu A cikin zuciyart" tace dan iska kawai sai yai ta faman dukanmu gashinan shiya kamata a doka toliet ta shige ta bugo kofar da da karfi

Kallo ya bita da shi yana girgiza kansa sannan ya mai da hankalinsa kan Siyama wacce tayi male male A kwance A jikinshi

Da hannu daya ya daga ta ya tsayar da ita tana fuskantarsa sai ga Siyama tana neman faduwa kasa kafafunta sai karkarwa suke bude idanta tayi ta zuba masa su wanda suke jazir gasu A lumshe sai faman kikkifta shi take ji' ko kunya' babu

Kallonta yake yana Na zarinta dariya yake cikin ransa yana kara kallonta ganin yadda ta kuma sabida jarabar dake cinta yarinyar nan ta kamu fa yafada A cikin zuciyarshi yana mata dariya fuska babu walwala yace "wuce kije ki hadamin coffe" ya fada cike da bada umarni

Ko kunya babu Siyama ta fara kame kame da inda'inda wata shegiyar tsawa Aliyu ya kwatsa mata yace "yimin shiru wuce kije kiyi Abinda na saki' " yar iskar yarinya kawai me zaki gayamin bayan kin gama iskancinki zanga karshen iskancin naki Ai "

Simi simi Siyama ta wuce tana dariya cikar burinta yau ta ta6a jikin da ta jima tana muradi gaskiya yaya Aliyu karshe in na Aure shi nagama morewa jikinshi kawai ya isa ya di mautar da mace humm daya ke cewa ni " yar iska ce shi din ma Ai shine tunda yana sane ya bar ni Ajikinshi zai wani kare kanshi haka take fada cikin zuciyarta
Chapter 27 · 0% Book details