← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 35

Sashe 17

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nene ce ta fito dija na bayanta samun guri tayi ta zauna a kan kujera

tana kallon fa'iza tace "haka kuke tafiya makaranta da wuri "? "ai nene ba asan mu makara sabida in malami yashiga. yai karatu ba kanan ba kuma, yima. zai yiba kuma in ka makara zane mutum ake a skull din mu"

dariya abbah yayi yace "ai skull din nan ba daya.suke da na ko ina ba duk da cewar makaratun na kudi ne amma akwai tsaro da bada kulawa "

jin jina kai Nene tayi tace " ai karatu duka karatu ne indai yaro zai tsaya ya kula"

"hakane abban yace dan bayasan yaja maganar sabida ya fuskanci inda nene ta dosa

"Nene antashi lafiya ya karfin jiki?
abban.yafada yana kallon ta

"lafiya lau masha ALLAH "

"Nene ina kwana " in ji fa'iza "daban kwana ba kya ganni" inji Nene dariya fa'izan tayi bata ce komai ba

Dija dake kusa da nene tun zamanta.sai kallon fa'iza take ta cike da sha'awa domin bakaramin kyau kayan makarantar sukayi mata ba sai taga unipom din ma kwata kwata ba ta taba ganinin irin shi a kano ba duk da yawan makaratun dake birnin na kano

sakowa tayi kasa ta durkusa tace " abbah barka da asubah katashi lafiya"?

"lafiya lau Dijana kin tashi lafiya kema ya gajiyar hanya "?

"lafiya lau Abbah masha ALLAH"

"Zonan "abbah yafada yana kallon ta

Tashi dijan tayi ta karasa inda abban yake zaune ta zauna gefen kafafunshi

shafa kanta abban yayi yana jin yarinyar har cikin ranshi ga tausayinta da yake ji sosai to amma komai na ALLAH ne yafada acikin ranshi

Kallonta yayi yace "dija kina son zama anan ko"?

Kallon sa dijan tayi sai kuma ta sunkuyar da kanta, bata ce komai ba

"kinga sai a saki a skull dinsu fa'iza ko"?

abban ya kuma yin magana a karo na biyu

daga kai dijan tayi tace "abba ina so "

yace " yawwa daga wane aji kikatsaya"?

"Pramary 4 ne abbah" tafada tana kallon sa

"Masha ALLAH zansa jameel ya kaiki skull din ai miki intervio sai a samu mai miki lesson ko"?

"eh abba " dijan tafada tana dada sunkuyar da kanta

"yawwa yarinyata ALLAH yai miki ALbarka kinji"

"ameen abba"

To.duk wannan tattaunawar da abbah da dijan sukai nene bata ji komai ba domin dai abbah kasa-kasa yayi da muryarsa shiyasa nene bata fuskanci abinda suke cewa ba illa tv da ta tsurawa ido sai kace mai fuskantar abinda suke fada

fa'iza kam babu wanda ya kai ta murna domin dai taji komai tunda kujerar da take zaune a kusa da abban ne

Ummi ce ta shigo falon asabe mai aikinsu na bayanta rike da kulolin kayan karin kai tsaye daynnig din ta nufa ta hau gyara gun koma wa kcin din tayi ta futu da wani kato flas din shayi ta ajiye ta dauko duk wani abinda tasan za'a nema sannan ta bar gun bayan ta kwashi gaisuwa gurin nene da mai gidan

Ummice ta kalli fa'za tace "kitashi mana kije ki karya ki na duba time ne takwas shaura cikin sauri fa'iza tashi

abbah ma mikewa yayi yakama hannu dija suka nufi dannig din

ita dai dija tayi shiru cikin ranta kuwa tana kara kaunar abban ganin irin kulawar da yake nuna mata duk da karancin shekarunta tana gane mai kaunarta sabida haka abba yana da babba matsayi a cikin ranta dan haka duk abinda yace tayi zatayi mutukar bai sabawa umarnin ubangiji ba

zama ummin tayi kan kujerar dake kusa da nene wacce ta tattara hankalinta kacokan kan kan tv tana kallon kamar mai jin abinda suke fada

murmushi ummi tayi tace "nene kallo kike ne "?

dauke idonta da ga kan tv tayi ta mai da kan ummi tace " yaushe kika shigo dakin ke kuma"?

dariya ummi ta danyi tace "yanxu na fito da ga kcin ai ina ta magana bakiji ba naga hankalinki. yana kan tv

numfashi Nene ta sauke tace "wato dai musulmi ya shiga uku a gun ya hudawa dubi yanda wa "yan nan yawudawa suke ragargaza gida jan musulmai suke kashe su kamar wasu kiyasai "

"to ya za ai nene karshe duniya ne ai dama annabi yafada ALLAH sai yagama zabe nasa yanzu a duniyar nan in dai zakai ruko da addini da bin sinar annabi muhammadu (slw) to baka da kima da mutumci a idanun wasu mutanen in ka tsannata ma a nemi rayuwarka ALLAH kasa mufi karfin zuciyoyinmu Allah kasa mu mutu muna musulmai da darajar annabi" ummin tafada tana girgiza kanta

"ameen dan ya rabbi " Nene tafada

"bamu gaisa bama nene antashi lafiya" ?

"lafiya lau na tashi "

"to masha ALLAH akawo miki kayan karin nan ko"?

"Me kuka dafa ne"? nene tafada tana kallon ta

"Wainar shinkafa ce nene amma nasa asabe tayi miki kunun gyada naga kina sonshi"

"kwarai kuwa kin kyauta ai kawo min nan bana iya hawa wancan abin yanxu sai kafata ta kumbura"

murmushi ummin tayi tace "hakane abin dama in yahadu da girma sai hakuri"

Abba kam yana zaune yana hira da dija cikin sakin fuska ummi takaraso gun itama ummin dariyar take tace "A'a hira ake ne nima bara nazo ayi.dani sunkuyar da kanta tayi tana dariya tace " ummi ina kwana "

"lafiya lau kintashi lafiya"?
ummin tafada da murmurshi a fuskarta

"lafiya lau ummi"

fa'iza ta wuce ne"? ummin tafada tana kallon abba

kallonta abban yake yace "ina hankalinki yake lokacin data ke ce miki ta tafi"

"ALLAH ya huce zuciyar abban yara ina can ina magana da nene lokacin inaji"

"eh yanzu muke magana da dija ma tace zata zauna damu a sata skull fa'iza ai "

Dariya ummin tayi yayin da take kokarin hada masa abinci tana masa magana da ido ya akai ta yadda nene kuma tasani

girgiza mata kai yayi alamar subar maganar

dariya ummin tayi cikin ranta tana adduar ALLAH yasa nene dai ta yadda tayi zamanta anan dan itama tana bala'in kaunar dija da tausayawa mata

kallon dija ummin tayi tace "daughter duba kiga ni abincin ya isa ko in kara miki"?

kallon abincin dija tayi tace "ummi yayi min yawa ma arage " A'a dija kidinga cin abinci kinji ai bawani yawa ne da ita ba hudu ce kawai fa daure ki cinyeta
ga tae nan kihada in zaki sha kinji dijana"

"To ummi " dijan tafada tana kokarin jawu flas din shayin

Siyama ce ta fito daga dakinsu Na'ima jikinta sanye da wata doguwar riga cotton kanta da hula

Ta karaso itama cikin iyayi da kissa ta durkusa gwiwa biyu tana gaida abbah

cikin sakin fuska abba ya amsa kamar yadda yake wa yaran sa

kallon ummi tayi wacce take faman hadawa nene kayan kari tace " ummi an tashi lafiya"?

"lafiya lau siyama kintshi Na'ima bata tashi ba kenan"?

"eh ummi kin santa da bacci na tashe wai na kyaleta "

"to ai shikkenan sai kizo ki karya kira bu da ita duk sanda ta tashi ta karya babu wanda zai tsaya jiranta " ummin tafada tana barin gun hannuta dauke. da kayan karin Nene

Ita ma siyama falon ta karasa tace " bara nazo na kwashi gaisuwa a gun uwar gida sarautar mata"

Dariya nene tayi tana kallon siyaman tace " da dai ya fi miki domin shima uban gayyar sai da yazo ya kwashi gaisuwa sannan ya fita"

Murmushi siyama tayi tace " ai girmanki ne uwar gidan ya ALI
ina fatan kin tashi lafiya"?

"lafiya lau na kwana" Nene ta fada tana kokarin sakkowa daga kujerar da take kai

Ummi kam barin gun tayi bayan ta kammala hadawa nene abincin

"Sakko kita yani ci mana zaifi lada" nene tafada tana kallon siyama

"A'a nene kici kawai zan tashi in da fa indomee bazan iya cin wai na da safe nan ba" siyama tafada tana dan ya tsine fuska

"haka dai ga abincin kirki kin barshi zaki tafi dafa wata indomee sabida kwadayi d son jiki "

dariya siyama tayi tace "nene ba kisan dadi ba wallahi,
amma kamar naji kince ya ALI ya fita ko"?

"kwarai kuwa ya fita mana tun safe"

Shiru siyama tayi ta so ta ganshi dan kwana tayi tana mafarkinshi wai gashi an daura musu aure suna rayuwa a guri guda itakam tana mutukar kaunar ALI shiyasa duk irin cin mutumci da yake mata bata gani an ce so hana gani hana ganin laifi

dija ce ta taso daga in da take bayan ta gama karyawa inda nene take ta je ta zauna ta na dan ya mutsa fuska

kallon ta nene tayi cikin kulawa " tace ke kuma meye" ?

shiru dijan tayi bata ce komai ba sai da nene ta kuma maimaitawa sannan tace " nifa babu komai "

"to meye zaki zo kina batawa wa mutane rai iyi"

"Nifa nene munyi magana da abbah zan zauna anan gidan zai sakani a makarantar su fa'iza dan haka in zaki tafi sai dai kitafi ke kadai " tafada tana tutturo bakinta

kallonta nene take cike da mamaki tace "au tanan kika bullo kuma"

"To baki isaba tare zamu tafi acan ba kya zuwa makarantar da xaki ce abarki anan ehe"?

"Nifa nene nafi son irin tasu fa'iza kinga anayin karatu gashi ta "yan gayu ce "

harararta nene tayi tace " sai kiyi kuma tafiya dake babu fashi to kaji""

ta fada tana cigaba da cin abincinta

wani irin ihu dija ta zunduma tana turje turje
cikin kuka tace " ni kam bazan koma ba nace miki ki barni anan dan ALLAH ke kiyi tafiyarki"

a guje Na'ima ta fitu taga dakinsu tana faman rarraba idanunta domin ihun da dija ta zunduma shi ya tashta ta ga bacci

Shikam abba tuni ya bar gurin tun lokacin da yaji dija tana ga yawa nene ta barta a anan dan haka yana daga sama ya jiyo ihun dija daman yasan haka zata faru

murmushi yayi kawai yana kokarin shiga wanka domin dai shima so yake ya fita offece maganganusu da dija su suka makarar dashi dan haka a gurguje yake shiryawa
Chapter 17 · 0% Book details