← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 35

Sashe 20

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nene kam itama ko kallonta batayi ba tace kyayi kyagama ni ko A mafarki ma ban yi zaton zaki.ce zaki zauna Anan ba sabida rashin sabonki da jama'a Nene take fadar haka cikin zuciyarta

jameel ne ya kalli inda Dija take zaune yace "ke wai me A kayimiki kike ta faman cin kunu tundazu"

banza Dija tayi dashi ta dauke i danunta daga inda suke zaune dariya yakama yace "wa kike harara da wannan kwala kwalan i danun naki " ?

harararsa ta yi tace "tubarkalla masha Allah "
ta dauke i danunta da ga kansa dariya ya kuma yi A karo na biyu yace "zo kiga wata sabuwar game mai dadi ce " yafada yana kokarin ciro wayarshi daga Aljihun gaban rigarshi banza tayi dashi bata ce komai ba

ummi dake zaune tun dazu bata ce komai sai yanzu tace "dan Allah ka kyale ta mana kazo kabi ka damu mutane da surutu ba gaira babu dalili"

murmushi yayi yace "wai don Allah ummi me A kayi mata ne"?

"ina ruwanka to" ummin tafada tana harararsa

fa'iza ce da sauri tace" ita da Nene ne fa wai baza ta barta A nan ba "

kallon Nene yayi yace "kamar yaya bazata barta A nan ba"?

ita ma Nene shi take kallo tace" e bazan barta A nan dinba ka wani zuba min ido "

"to ke ina zaki da ta keso kibarta Anan din"?

"bansani ba gobe in sha Allah zan kama hanya na koma in da nafito tunda A bin yazama haka" Nene tafada tana kara kallon inda Ummi take zaune

dariya jameel yake yace "wasa ma kenan Ai sai dai kitafi ke kadai Amma Dija baza ta biki ba tunda tana son zama A nan "

ko kallonsa Nene batayi ba ta ciga da kallonta hannuta rike da carbinta

Abba ne yai sallama domin kai tsaye da ya sauko bai zauna A falon ba masallaci ya nufa sai da ya jira yi isha'i sannan yai A ddu'oinsa sannan ya bar masallacin

kallon jameel din yake yace " ba ka wuce masallaci ba kanaji A na sallah ko"?

"eh Abbah yanzu zan tafi" jameel din yafada yana sunkuyar da kansa

"Ai sai dai kayi taka kai kadai tunda yanzu babu masallacin daza su tsaya jiranka " Abba yafada yana kokarin zama kan kujarar da take fuskantar Nene

tashi jameel din yayi yana faman sosa kansa ita kam Nene harara tabishi da shi tace "sai Aukin surutu jam'i yana huce ka"

bai ce komai. ba ya fice gaba daya daga gidan

to suma su Na'ima ta shi sukayi bayan sun sake gaishe da Abbah

A kabar Nene da Abba A falon Ummi kam tun lokacin da Abbah ya shigo ta tashi ta nufi daynnig domin ta hada masa Abinci

gaishe da Nene Abbah ya kuma yi yace "munyi lafiya Nene"?

cikin kulawa Nene tace " lafiya lau ya Aiki da fama da jama'a"???

"lafiya lau Alhamdulilah "Abban yafada

"masha Allah Allah ya taimaka yayi jagora "

"Ameen ya Allah Nene"

"dazu kina magana babu lokaci ko" Abbah yafada yana kara mai da hankalinsa kan ta

"eh ni da Dija ne baka ga irin rashin kunyar da takewa yarannan ba suna Na'ima ita da wannan yarinyar matar Ali"

"Assha "! Abban yafada yana gyara zamansa hankalinsa gabadaya Akan Nene

"yawwa sai magana ta biyu tasa rigimar wai sai nabarta Anan wai kace zakasa ta A makarntar da fa'iza ta ke zuwa to Ai acan din ma tana zuwa makarantar sabida haka gobe nace dama zamu kama hanya mu koma tunda kun zugata da kai da sauran yaranka"

murmushi Abba yake acikin ransa yace "nasan za Arina dama "

kallonta Abba yake cikin rarrashi yace "haba dai Nene Ai munyi da ke cewar sati biyu zakiyi sai in sa A mai dake ko ni in mai da ke da kaina ko"

"kwarai kuwa haka nace to yanzu na canja shawara gobe nake so in tafi tunda Abin ya zama haka dama kadade kana so ka dauke min Dija daga gaba shine yanzu kuka taro da kai da yaranka kuke zugata yarinyar da bata so natafi ko ina na barta yau ita ce take cewa baza bini ba"

dariya ta kama Abba ganin yadda Nene ta wani hakikance ita fa da gaske tafiya.zatayi

yace "kiyi hakuri Nene kikara kwanaki ko sati ne kiyi don Allah kuma ina rokon Alfarma kibar min Aron Dija don Allah in hadata da "yan uwanta guri guda tana gama skull zan mai do miki da ita "

"wai karatu duk ba karatu bane da za ku wani dame da zancan karatu ehe Acan din ma Ai tana zuwa makarantar "

"Ai nasani" Nene Abba yafada cikin rarrashinta

sannan yace "karatunmu.na nan ba daya suke.da na can ba nan zatafi samun kulawa sosai sannan tana ganin "yar uwarta zatafi mai da hankali"

Shiru Nene tayi bata ce komai ba Abbah yace "ke nake sauraro Nene in baki Amince ba sai kutafi babu damuwa tunda tana debe miki kewa yarinyar"

Ajiyar zuciya Nene ta sauke tace 'shikkenan Ai tunda kun matsa sai ta zauna Amma nasan halin Dija zata iya bijerewa in An kwana biyu tace A maida ita to wannan ne ban Amince ba tunda har kun zabi zamanta Anan din ita ma tana so to sai dai in ce Allah ya bada mai Amfani ilimin"

"Ameen" Abba yace fuskarsa cike da Annuri bai zaci zai shawo kan Nene cikin sauki haka ba

yace "in sha Allahu haka baza faru ba Nene Dija zata zauna samu ilimi mai Amfani"

"to Allah yasa gobe kasa A mai dani Ai mun gaisa ko to zaman me zanyi"

"Aa ' Nene kikara hakuri kiyi mana sati daya mana"
Abba ya fada

kan Nene tayi magana Ali ne yayi sallama cikin falon fuskarshi babu yabo babu fallasa shigowarshi kenan wata irin yinwa yake ji tun safe rabonshi da yasa wani Abin Abakinshi don haka,da ya shigo gidan bai nufi bangarensu ba ya shigo gidan so yake ya fadawa ummi cewar tasa Akai masa Abinci can domin wanka yake son yayi

tun A mota ya cire rigar saman yabar ta cikin wacce suke daura rigar kakin Akai wata mai yan kakakke hannu don haka A hannu ya shigo da rigar

daya hannunashi rike da wayoyinshi da key din motarshi da ma loptop dinshi A motar yake barinta

sun kuyawa yayi yana kwance igiyar ta kalmin shi wanda tun da ya sashi bai cire ba sai dai in zaiyi Alwala

kara sowa yayi tsakiyar falon ya karasa in da Abbah yake zaune yana mika masa hannu

shima Abba hannu ya mika masa sukai musabaha A junansu Alin yace "Abbah barka da dare Abbah"

"yawwa barkanmu dai haidar ya Aikin na ku" ?

"Alhmdulilah mun gode Allah Abba, gobe ma Insha Allah zamu wuce can jahar taraba jalingo domin kwantar da wata tar zoma da ta ke faruwa"

"to masha Allah Allah yakiyaye ya bada sa'a"

"Ameen Ameen" Alin yafada to duk wannan Abin da suke hannayensu nanan rike da na junansu kamar wasu Abokai wannan shakuwar haka take tsakanin Abban da Aliyu

cikin murmumushi Abba yace" yawwa sai ka zauna ka rarrashi uwargidan naka gatanan tace wai gobe take so ta tafi"

kallon inda Nene take zaune Ali yayi yana dan ya mutsa fuska na sabo

ita kam Nene tana zaune zukudinm tana mamakin wannan shakuwa tsakanin uba da dansa kamar wasu Abokai

ita ma shi take kallo tace "meya ka tsareni da wa "yannan ida nuwanan naka kamar na masu jin bacci ko ince kamar na mashaya sai ka dinga faman kikkiftamin ido eh ! , nace zan tafi kuma bance kai zaka mai dani ba ehee!"

kallonta yake fuskarshi A hade sabida dama shi haka yake in dai ya gaji ba ko wane yake gane gajiyarsa ba sai umminsa ita ce take fahimtarsa in dai tanganshi babu wal wala duk da cewar dama ba kasa fai yake dariya ba

cikin ransa kuwa cewa yakecewa wannan Nene masifarfiyace dubi sai wani masifa takewa mutane

fuska babu walwala yace mata "Nene kin Wuni lafiya"?
Ya bar maganar da take tabi ruwa

"lafiya lau " Nene ta fada tana dauke i donta daga kan sa

ta daura A kan Abba sannan tace " ka tambayeshi ya muka yi dashi da yaje tawo damu "

kallon Alin Abbah yayi yace" to kai kaji yaya kuka yi da ita ne"? Abbah ya nuna kamar bai son Abinda suka shirya mata shi da Alin ba lokaci da zai je daukota

cikin yanayin maganarshi yace " bangane A tambaye ni yaya mukayi ba ke ce fa kika ce zaki zo sabida kin dade bakiga danki ba da sauran jikokinki " Alin yafada ida nunsa Akan Nene gashi fuskarsa A hade kamar da gaske

kallonsa Nene take tace "Af Ai ka kware wajan kulla sharri kamar wata mace kai wata macen ma in kana guri duk sharrinta sai ta kauce " Nene tafada tana faman hakikancewa

wata dariya ce ta so ta subucewa Ali Amma ya dake yana yinta A zuciyarsa ganin yadda Nene take kokarin fadowa daga kan kujera sabida masiba

Abba dake gefe shima dariyar ke cinsa Amma ya dake yana kallon Alin
yace "kai bana son shirme tambayarka nake ya kukayi da ita lokacin da kaje dauko ta"

gyara zama Ali yayi yana duba A gogo dake daure A hannusa.sannan ya kalli Abba yace "lokacin danaje ne Abba na tarar da yarinyar nan suna dambe da yara gashi lokacin makaranta Nene bata tura ta da nai mata magana sai tace,Ai makara tayi shiyasa bataje ba,to A dan zaman danayi na lura da yarinyar bata son karatu gashi bata da kunya shine nace kace in tawo da itanan zaka sata A makaranta shine fa,Nene tace ita ma zata zo to kaji yadda mukayi fa Abbah"

kafin Abbah yace komai Ali yaji saukar Abu Ajikinshi kallon gurin yayi romot din tv ne Nene ta cillo masa tana faman harararsa kamar idanta zai fado ita kam bazata iya da sharrin Ali ba ta fada cikin ranta

murmushi yake yana kallonta sannan yace "me nayi miki daga fadin gaskiya kefa kika ce in fadi yadda mukayi dake"
Chapter 20 · 0% Book details