Sashe 3
Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****
Bashir mutum ne Na jama'a baya zama ,sosai tunda ya kammala scondry skull yafara harkar Siyasa,
A daddafe ,ya tafi ,bayaro univasity dake kano ya samu difoloma ,sai ya watsar da karatun ya shiga siyasa gadan gadan
Tun Nene bata so ,daga baya sai ta dawo tana masa Addu'a.
Dan Uwanshi kuwa Lawan babu ruwanshi domin magana ma bata dameshi ba,
Shima a yanzu yana makarantar gaba da primary
Duk Abinda Bashir ya samu Na jama'a ne ,shayasa a kasa ka masa Bashir Mai jama'a
Ganin girma yazo masa ya
Sa Nene tayi masa maganar yayi Aure domin shine cikar mutum
Nan ya nuna mata shifa yanzu bashi da wata budurwa harkar Siyasar sa kawai yake
Nene tace to yaje yaga Zainab "yar gidan kawun shi wato Kanin Malam ibarahin tace taga yarinyar tana da hankali da nutsuwa
.yace to shikkenan zai je ya ganta
Ko da Bashir ya ga Zainab sai yaji ta kwanta masa,sabida haka ba'a dauki wani dogon lokaci ba a kasha shagali Amarya ta tare nan gidan kusa da Nene dake gida ne girman gaske ,haka Bashir ya yanki guri yayi ginin zamani sosai.
Yawan kyautarsa da tausayin talakawa yasa matasa da tsaffin yankin Nash suka tsayar dashi takarar Craman ,Aikuwa Abin ikon Allah lokacin zabe yana zuwa Bashir ya lashe yazabe.
Zoka ga murna gurin jama'ar gari ,da "yan Uwa da Abokan Arziqi jama'a sun ji dadi domin suna ganin Bashir zai kawo ci gaba a yankin nasu
Lokacin Zainab matarshi tana da tsohon ciki ,Haka tai ta taya mijinta murna,
Nena ma tayi farin ciki sosai tai tayi masa fatan Alkairi gami da Addu'a Allah ya tayashi riqo,ya sauke nauyi da ya dauko
Lawan ko dashi a kai ta fadi tashi ,bakinshi yaqi rufuwa ,Sai murna yake.
A taike dai Alh Bashir yariqe mukamai da dama ta fannin Siyasa in da daga baya yasaki harkar Siyasa yafada kasuwanci ,shida wani Abokinshi Alh Auwalu ,sosai suke shi go da motoci Iri daban daban Na zamani Cikin farashi mai sauqi
Ya gina gida nagani nafada a Abuja ,yayi yayi da Nene ta zo su tare a can tace ita dai ya kyaleta a nan yafi,hakama babu yadda bai yi da lawan ba a kan yazo su tafi yace ya qyaleshi anan zai biyo bayanshi in an kwana biyu.
Babu yadda Alh Bashir ya iya haka ya hada kan iyalinshi ya tafi lokacin Ali ne kadai a lokacin shekarunshi Tara ,Yaro ne Mai nutsuwa Wanda baya son kwarfniya ,mugun miskili a jin karshe Dan in yaga dama sai ya kwana bai kula Kowa a gidan ba,Nene ce kawai ta iya da halinshi.
Tun yana yaro yake da mugun kyankyami Abu qalilan zai sashi yai ta kwara A mai
Nene tayi kewarsa sosai sabida sun shaqu da juna
Basu jima da komawa Abuja ba Hajiya Zainab tasamu ciki Alh Bashir yayi ta murna
Lokacin haihuwa yazo Allah ya sauke ta lafiya an samu da Namiji
Nene tace A sama jamelu
To haka rayuwa ta tafi Alh Bashir Arziqi yana kara bunkasa sosai da sosai
Yaranshi hudu biyu maza biyu mata
*wanene Aliyu*
yana da bakar zuciya da miskalnci sai kai mai mgn goma bai kula kaba sai yaga dama zai amsa daya yana da bala,in tsafta dan haka ba abincin kuwa yake ciba in kacire nenensa da ummi bai yadda ko ruwa masu aiki subashi ba indai bai daga hannu ummi ya fito ba duk da cewar ruwan roba ne
Yana mutukar san ya ga yazama soja tun yana yaro shiya sa yadage sai da yatafi yai karatu sosai akan aikin yanxu haka ya kammala aiki kawai yake jira ya fara,,,
To lawan ma akwai wata daya so anan bayan gidansu yarinyace mai sanyi hali kamar sa sunanta khadija ,,
Da nene ta fuskanta tace to baza ay kasa a gwiywa ba taje tasamu yayan mahaifinsu tace to aje a ne mar mai auranta ,,
Aikam ba,awani dau lokaci ba aka sha shagali bayan duk 6angare biyu sun amince ,,amarya ta tare anan gidan kusa da nene tunda gida ne mai girman gaske bangare bangarene ,,
Idan baku mantaba dama mlm ibarahim mai arzikine a wannan yankin nasu a wancan lokacin gidansa ma abin kallo ne
iyama.
Nene tana mutukar jin dadin zama da khadija sabida irin matan nan ne masu kirki da saukin kai babu ruwan ta da hayaniya haka shima lawan din yana jin dadin zama da ita ,,
Alh bashir kam yakanzo lokaci zuwa lokaci dashi da iyalinsa yakan dan jima kan yakuma abuja shiyasa yaran sukasa saba sosai musamman Ali mutumin nene tana bala,in sansa ,,shikam Ali bai san tanayi bah
Sai tahana kowa abu tace Ali zata bawa sai yazo tabashi yace bayaci ko ya kar6a ya bayar a gabanta ba yadda zata,yi takari mitarta ta gama yai mata banza ,,
To haka rayuwa taita tafiya lawan Allah bai bashi haihuwa da wuriba sai da sukai shekara sha uku da aure sannan Allah ya a zurta khadija da samun ciki,,
Nene taita murna dan a zuciyarta take cewa shine yagaji irn haihuwata dan har tana ganin ma ko bazai haihu bashi huumm ,,,,,nace nene ai abin na Allah
Tunda khadija tasamu ciki take faman shan wahala yau da lafiya gobe bb irin cikin nan ne mai bala,in laulayi ta ke dashi dan haka nene bata barinta tai komai a gidan. ,,gashi nene taudau son duniya ta daurawa cikin abu kadan khadija zatai zatahau yimata fada wai bata kula da kanta,,itadai sadai tai dariya kawai,,
To dahaka watan haihuwa ya kama ciwo matsawa khadija musamman ciwon kai da mara nene tace suta fi asibiti aikam da sukaje likitoci suka dubata sukace haihuwa da sauran kwanaki amma akan hanya take suka ce ta kula da daukar abu mai nauyi da yin aiki n wahala kuma tadaina cin gishiri dayawa idan da wata damuwa d tasa ranta ta cire,, nene tace ai dama bb wani aiki da take kawai larura ce irin ta masu ciki haka suka dawu gida bayan an bata magani kuma sukace yaron lafiyar sa lau
Kwana biyu da zuwansu cikin dare khadija ta tashi da ciwo haka lawan ya fito ya sanarwa nene
A gigice nene ta shiga bangarannasu ta tarar da khadija sai faman zubda jini ta ke gashi sai nishi take haihuwa taki zuwa da sauri nene taka mata ta rike tana tofa mata adu,oi sannan ta kalli lawan tace yai maza yaje yakarbo rubutun nakuda a gun malam yahaya wani makocinsun ne anan mai "yan makaran ta
Cikin a zama yatafi yana tafiya yana ado,a acikin ran,sa ganin irin wahalar d khadija take sha yana girmama irin wahalar da mata suke sha yayin haihuwa tunda duk a gabansa khadijan tafara nakudar,, a xuciyar sa yake fadin duk wanda bai bi iyayen sa ba yayi asara,,
To cikin hunkuncin ubangiji kan yadawu ma Allah ya sauki ta lafiya inda ta haifi diya mace ya dawu wa yai ya tarar nene sai hidmar gyara baby take baki ya washe yana nene me,akasamu ne?
Nene jikinta a sanyaye tace mace ce lawan bani rubutun daka kar6o ka kuma waje tukkun kafin a gyara gun,,mikamata yai shima jikin sa da dan sanyi ganin yanayin nene,,
Nene kam khadija ta dago tana bata rubutun ganin har yanzu mabiya bata fado ba gashi jini sai zuba yake sosai,,
Tayi duk dabarun irin na gida abin ya faskara ,,lawan takira tace maza yatafi ya samu mota suzu sutafi asibiti ,,da sauri yatafi gashi har an soma kirayekirayen sallar asubah ,,
Allahu Akabar kafin yadawu rai yayi halinsa kadija ta amsa kiran ubangiji
Wayyo duniya abar tsoro,,
Innalilahi wa ina,illahi raji,u shine abinda nene take ta fada
Wannan yarinya Allah yakar6i shadarki Allah yasa annabi yasan da zuwanki Allah ya kafartamiki shine abinda nene take ta maimaitawa,,
Tun a hanya lawan yaji gabansa yanata faduwa yacigaba da nana ta innalilahi a ransa sai yaji kamar anace masa ta mutu ay ,,,gabansa ya yanke y fadi da sauri ya shiga gida ,,sai yatarar da nene a tsaye da wasu mata biyu ,,
Yace nene ga mai motar nan ansamu ina khadijan ta ke yafada ya na kokarin shiga dakin nene ce ta rike hannunsa tace jeka sallami mai motar ai tasamu sauki ma ,,to yace jikinsa a sanyaye ya fita yana fita yaci karo da yayar khadija da maihaifiyarta da wasu daga cikin danginta ,,wasunsu nata hawaye ,,
Tsayawa yai kawai yana kalloansu sai yaji wata acikin su tana lawan ya hakurinmu ido ya bita dashi kawai ya sallami mai motar yajuya shiga gidan ,,
Kai tsaye dakin da khadijanta ke ya sa kai yana so ya tabbatar da abinda kunnuwansa suka jiye mai,,
.
Bb wanda ya hanashi shiga har nene ,,yana shiga yadaga zanin da nene ta rufe khadija da shi yatsaya y na kallonta ,,a ransa yana ta nanata innalilahi wa innalahi raju,u ,,sai yaji wata dauriya tazo masa ya tsuguna a gefe daya ya fara yimata karatu yana ta nai man mata gafara a gun buwayi gagara misali,,
Ya ji ma a gun a zaune babu wanda yashiga dakin ,,dakansa yatashi ya fito ganin gari ya soma washewa yaje ya dauro al wala yai sallah,,
To haka rayuwa take dama haka akaima khadija suttura a kaita gidanta na gaskiya,,,,,
Haka lawan yaci gaba da karbar gaisuwa gurin "yan uwa da abokan ar ziki""
Alh, bashir shida iyalinsa sun jima kan sukoma abuja ,,,,ganin yadda hankalin nene ya tashi a wancan lokaci ya zauna yadinga rarrashin kanin nasa da ita kanta nene n,,,
To yarinya dai nene tace amayar mata da sunan maihaifiyarta ,,wanda nene tadauki son duniya ta daura mata bata san ko tsinke ya sauka a kanta,, ita tasama ta dije wai tunda sunan maihaifiyarta ne da ita ,,Alh bashir ba yadda vaiyi da nene tabashi baby sutafi da,ita tunda a lokacin hjy zainab tana da karamin goyo ta hada ta shayar dasu tare ,,amma nene ta ke kashe tace bata yadda ba a kyaleta a gunta ita zata kula da ita ,,haka suka je asibiti a ka daura baby n da irin madarar da yakamata a bata,,