Sashe 16
Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin sauri tata shi fuskarta dauke da murmushi tace "ya AIi kaine ashe sannu da zuwa" ta fada tana kokarin gyara zamanta sosai
murmushi Ali yake sabida yarinyar tana birgeshe tana da hankali sosai yace " Nine nafisa wannan mijinnaki bai da kirki ya hanani shigowa da kyar ya barni na shigo sabida kawai nace kar yayi miki kishiya shine yake jin haushina " ALI yafada yana kallon faruk din wanda tun shigowarsa yaje ya makale jikin Nafisan yana faman lumshe ido
saurin kallon faruk din tayi tana harararsa cikin bata fuska tace " hakane" ?
cikin sauri faruk din ya tashi daga jikinta yace "man ta dashi my love kinsan mugun makaryaci ka wai yarasa sharrin da zai min ne dan yana jin haushi ina da iyali na
wata dariya ce takama Ali amma sai ya share yana kallon faruk din yace "ni nake maka karya ko"?
ok hannusa ya zira cikin aljihunsa yana kokarin fito da wayarshi yace "bara kiga zahiri tunda ina da pic din budurwasa kinsan bazai bari a wayarshi ba dan karki gani shi yasa yake boyewa a nawa wayar"
sakin baki faruk din yayi yana kallon Ali yana mamakin sharrinsa cikin zuciyarsa kuwa sai zaginshin yake "wallahi sai nai ma rashin mutunci " maganar tafito daga bakinshi bai shirya ba
cikin sauri yatashi yakarsa inda yake ya fizge wayar sai faman muzurai yake yana Aikawa masa sakon harara
Ali kam dariyar da take tacinsa tun dazu ya saki yace" meye haka zakazo ka fizgemin waya"
banza faruk din yayi mishi ya koma gurin nafisa ya zauna yana gyara fuska mika mata.wayar yayi yace "karbi kiduba ko ina na wayar kigani karya yake wallahi kinsan mugun makaryaci ne" yafada yana faman shishigewa jikinta
itakam in banda. harara babu abinda take aikwa da faruk din sannan cikin basawar wa takarbi wayar ta hau dubawa
Ali kam yana gefe sai faman murmushi yake yana kallon yadda faruk ya wani firgice lokaci daya shi abin ma mamaki yake bashi shi kam bazai iya zubar da girmanshi ba irin haka ba
kallon faruk din yayi yace "dallah malam kabar mutane jiranka fa nake akwai maganar data kawo ni "
wani kallo faruk din yake mishi na alamar kafitar dani a gurinta
Sarai ya fuskanchi abinda yake nufi ya basar
mai da kallonsa yayi kan nafisa yayi yace "rabudashi nafisa yasa scurity a glarey din babu abinda zaki gani amma kisha kuruminki babu ke ba kishiya tunda bakya so"
kallon sa tayi ta saki fuska tace "nagode ya Ali ni ba kishiyace bana so ba halinta nake gudu"
dariya Ali yayi yace "ki fadi gaskiya dai itama dariyar take tace "wallahi daske nake "
yace "to kici gaba da addu'a ALLAH yazabawa mijinki abu mafi Alaikari"
"to ya Ali ina yin masa addu'a ai ALLAH yazaba masa abu mafi alkairi amma gaskiya ni kam bana son kishiya shima ya sani"
nafisan tafada tana mai da nuffashi
kallonta Ali yayi yana nazarinta murmushi yayi aransa yace wai mata me suka dauki kishiya ne su dunga gudun junansu sabida rashin yadda
wannan abu ALLAH ne ya hallattashi mutukar namiji zai yi adalci sunna ce babba shi bai ga abun gudu aciki ba
mai da kallonsa yayi kan faruk din wanda yake kusa da nafisa sai faman shishshige mata yake yana aikin rarrashi da murya kasa kasa
kallon agogon hannusa yayi yaga goma . dara bi
kallon faruk din ya karayi akaro na biyu har yanzu abu daya yake tsaki ya ja cikin ransa ya wannan dan iskan ya manta dani a dakin in ce ko
tashi faruk din yayi rike da nafisa duk rabin jikinta yana jikinshi yana faman lallabata
kallon ALI tayi tace " ya ALI zanje in kwanta bana jin dadi wallahi ka gai da gida agaida ummi da Na'ima
cikin dan ya mutsa fuska yace " ok ummi dai za taji amma sauran sakon na ki ne mi dan aike ko ki aiki mijinki"
dariya nafisa tayi tace "ni na isa in aiki oganmu ai girman kujerarka ne ALLAH ya huci xuciyar mai martaba" tafada tana murmushi
faruk dake rike da hannnuta tun dazu yace "muje ki kwanta kira bu dashi yaje yaji da ya warshi hararshi tayi kasa kasa domin dai har yanxu bata gama sakkowa daga zargin data ke masaba""
ciki bacin rai faruk ya futu daga bedroom dinsu bayan yagama lallaba nafisa da cewar zolayarta kawai ALI yake amma ba gaske bane abinda ya fada da kyar dai yasamu ta yadda ta kyaleshi ya futu gun
Ali
"wai kai meyasa baka da mutunci ne iyi" faruk din yafada yayin da yake zama cikin kujera
eic pic din dake mane da kunneshi ya cire yana kallon faruk din cikin kwanciyar hankali yace "wane irin rashin mutumci na yimaka"?
"bansani ba" faruk din yafada yana faman huci
dariya Ali ya kama yace " bani zaka nunawa iyali ba dan iska har yaushe kayi auran da zaka dinga magana akai kabari su shamsu da suka jima aciki suyi maganar iyali bakai ba sabon shiga "
"eh naji nafi wani wanda yake yawo bashi da shi"
faruk din yafada yana hararar sa
da murmushi a fuskar AliI yace " to ai baka da matsala tunda kaje kun hada baki da Nene za aimin auran dole to na yadda zan auri Siyama shikkenan burinka yacika ko"
banza faruk din yai mishi ya dau romot din tv yana canja za tasha
"malam magana nake maka " AIi yafada a zafafe
"dama maganar data kawoka kenan "? faruk din yafada yana basarwa
banza yayi mishi ya mai da eic pic din shi kunne shi bayan yadan rage volom din
"to ai gata za muyi maka katsaya kana faman zabe mace ko a ina zaka samu irin mace mai wannan halayen da kake nema oho duk irin bai war da.ALLAH yayimaka gami da farinjini "yan mata kasan duk cikinmu babu wanda "ya mata suke rubibi irinka ko wacce sai kace batai maka "
Kallon sa Ali yayi yace " kwarai basuyi min ba itama siyaman ba wani yimin tayi ba ka wai dan kuna son abun kuma zabinku ce to zan aure tan sai a kyaleni in huta ai amma kasani dole zan auri zabina in sha ALLAHU"
Faruk yace "ai ba mu hana ka ba Alhji dama Annabi ya bamu ikon haka ,abinda nakeso ka fahimta shine kabi umarni abba ,ka auri yarinyar nan na lura ita ma tana kaunarka sosai in yaso daga baya sai ka auri zabin naka"
Tabe baki yayi yace "ai magana ta kare kuma na bar komai a hannunka ok
Allah yasa haka shi yafi alkairi"
"Alhmdullhi "
Faruk ya fada cikin farin ciki ya ciga ba da cewa zan je in samu abbah da maganar"
Mikewa yayi yana Sosa kunnenshi da key din motarshi yace"to mai iyali ni zan tafi"
Faruk ya sa dariya ya Mike tsaye yana dukan kafadar Ali cikin dariya yace"ai ba karya ba ne in mutum ya Ji haushi yayi ya huta
Dariya suka dukkaninsu suka fito tare Ali ya shige motarshi Faruk Na daga masa hannu har sai da yaga ficewarshi daga gidan sannan ya koma ciki fuskarsa dauke da murmushi,yana mutukar jin dadin yadda suke mu'amala da Ali cikin mutumci da sanin ya kama ta.
Washe gari da wuri Ali ya kimtsa tsaf ya shirya cikin kayan aiki Wanda sukayi masa mutukar kyau sosai da sosai ya daura a gogonshi ,sannan ya zauna gefan katifarshi yana daure takalminshi sosai ,sannan ya fito daga part din nashi kai tsaye cikin gidan ya nufa
Falo shiru babu motsin kowa yasan Ummi tana kchin ,kai tsaye dakin Nene ya nufa
Nene na zaune kan dadduma hannunta rike da carbi tana lazimi ,sai gyangyadi takeyi
Ali ya shiga yana ta sallama yaji shiru can ya hangota tana Neman faduwa ,bacci ya kamata
Ya karasa da sauri ta taro kan ta da hannunshi ,ya ce"Nene zaki fadi fa ,in bacci zakiyi ba sai ki kwanta in kin tashi kya karasa carbin naki"
Nene ta bude ido tana salati race"o yanzu baccin nan sai da ya fizge ni wallahi kokarina in cika carbin nan"
Ta dago kan ta na kallon Wanda yake tsaye a kanta
Gabanta ya fadi ganin mutum tsaye a kanta kikam da kayan soja Sam bata zaci Ali ne ba
Ya gyara fuska yana kallonta Dariya naso ta kwace masa sabida ya lura da yadda ta razana da farko
Yace"gaishe ki nazo nayi Uwargida sarautar mata"
harararsa take tace "nace kazo ka gaishe ni ne " ? "baki fada ba" yafada yana kallonta fuska ya dan ya mutse yace " wai ke bakya gajiya bacci ne "?
"bacci fa na tadda ke ki nayi a zaune saura kadan kiyi "yar dungure dan natasheki shine laifi"
"bakai laifi ba " tafada tana kokarin cire hijab din wuyanta
a gogo hannusa ya kalla .bakwai da kwata kallon ta yayi yace " antashi lafiya"?
"lafiya lau " tafada yace ya" karfin jiki da gajiyar hanya"?
"masha ALLAH gajiya tabi lafiya "
"zamu fita kimana addu'a " yafada yana kallon ta
kallonsa tayi "tace ALIYU ai kullum cikin addu'a muke ALLAH ya inganta rayuwarku da kai da kannanka ALLAH yabada sa'a ALLAH ya tsare min kai a duk in da zaka shiga"
"Ameen ameen uwar gida gaskiya ina ji .dake daka ke babu wata " yafada.da murmushi a fuskarsa itama dariya take tace "yo ai duk wacce zaka auro sai dai tazama gora dama"
murmushi yayi .bai ce komai ba yakama hanya fita
ita kam Nene Dija ta ke tashi tai sallah dan da asubah ba yadda batayi da ita ba tatashi ta aki a cewarta ta kyaleta tagaji duk da cewar sallar asuba bata wuce ta
a gurguje AIi ya kammala karyawa ya fita daga gidan dama sun gaisa da abbah tun da asubah bayan sun dawo daga sallar asubah
fa'iza ce tafito cikin shirinta na skull Abba ne zaune a falon yana sauraron labaran safe a tashar aljazira kusa dashi taje ta zauna tace "abba barka da asibah dafatan katashi lafiya"?
da murmishi a fuskarshi yace "lafiya lau fa'iza na kin shirts"
"eh abbah Fa'.iza tafada tana gyara book din ta
yace "masha ALLAH Allah ya tai maka "
"ameen abbanmu"