← Book details Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 35

Sashe 18

Nana Khadija Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi ce ta kara so gurin da suke tana kallon dijan wacce ke ta birgima a kasa tana faman gursheken kuka cikin rarrashi taje ta daga dijan ta rungumeta a jikinta tana kallon nene tace "don ALLAH nene kiyi hakuri kibar ta anan mana tunda ta nuna tana son karatun da da take gudun makaranta fa ai yanzun sai mu godewa ALLAH tunda da kanta take son tayi karatun"

hararar ummi nene take tace "au! daure mata gindi zakiyi kema wai waya gaya muku a can bata zuwa makaranta ehe?
ajin ta hudu fa pramary sai dai kuce ba kullum take zuwa ba amma tana karatu acan daza ku bi ku dame ni da maganar karatu"

"hakane nene to amma yawan fashin da take yi bashi da wani amfani kUma bazata fuskaci komai ba a makarantar dole sai da kulawa sosai " ummun tafada tana sauke numfashi

kallonta nenen tayi tace " au! ni bana bata kulawa kenan"?

"A haba nene bahaka nake nufi ba ina nufin ko da an kai ta skull din dole za asamu mai mata lesson har gida dan kwakwalwarta ta ta da wa she wa shine nufi na "

shiru nene tayi bata ce komai ba illa cigaba da cin abincinta da tayi hankalinta kwance

N'aima kam harara dija take tace "ke wane irin shashanci ne wannan da zaki na faman kurma wa mutane uban ihu a gida sai kace wacce a ka kona da ruwa zafi wallahi sa'arki daya ya ALI bayanan da kinci kaniyarki yadda ya tsani kwarfniya da iface iface"

"umm! kema kya fada sis ni da ta kurma ihun ma wallahi da guduwa zanyi dan nayi bala in tsorata " siyaman tafada tana faman hararar dijan

dije dake rike a hannu ummi har yanzu wani kallo take kirmamawa Na'ima da ga ita har siyaman tace "to meye ruwan ku anyi ihun duk abinda mutum zaiyi yayi ai kin banza aikin wofi "

tofa baki yasan abinda zai fada amma bai san abinda za'a mayar masaba

zare ido siyama tayi tana kallon dija rike da habarta tana mamakin rashin kunyar yarinyar

ita kam Na'ima kan dijan tana nufa tana kokarin kai mata duka ummi tana kare ta tace "zan bata miki Na'ima ai da gaskiyarta meye ruwan ku da ita sabida tsabar zubar da girma"

"haka zakice ummi kina jifa zaginmu take waye sa anta a cikinmu ehe"?

"to ai ku kuka shiga sabgarta tunda tazo ai inaji bata tankawa kowa acikinku ba in banda Fa'iza da suke sabgarsu tare"

kwafa Na'ima tayi tace "wallahi sai na hada ki da ya ALI tunda baki da mutumci marakunyar yarinya kawai " tafada tana wuce wa daga gun

kunkunni dijan take to " ki ga yamasa mana kar yabarni da rai"

in banda ummi da take rike da dijan babu wanda yaji abinda tace su dai sunga bakinta yana motsi

murmushi ummu take acikin ranta itama tana mamakin tsaurin idon yarinyar to amma ai khadija sunanta duk inda me suna khadija take tana da tsaurin ido da tsiwa gashi bata barin ta kwana to ammafa suna da bala'in kirki kuma baza su shiga sabgarka ba mudun batasu kashiga ba kuyi hakuri masu suna khadija a gafarceni kadan daga irin halinku

nene kam duk wannan abin tana jinsu ko kala ba tace illa data gama cin abincinta ta gyara kwanokan ta matsar dasu gefe ta koma kan kujera ta cigaba da lazimin safen da take wanda yazamar mata jiki da jini sai tayi in batayiba ma bata jin dadi cikin ranta kuwa tace kukarata in dai dija ce gatanan ga ku ai tunda bata kyale ALI ba wazata kyale

siyama ko kallo take ta bin dijan dashi tana faman ya tsine fuska lokaci guda sai taji ta tsani yarinyar jiya dai data ganta sai taji tana sonta kasan cewar tana yanayin kama da habibinta ita tunda take babu wanda yataba zaginta baranta na ya mayar mata da magana irin haka

dija kam data fuskanci hararar da siyaman take mata itama sai ta fara ramawa tanayi tana murmurdae bakinta

sakinta ummin tayi ganin abbah yana sakkowa da sama hannushi rike karamar jakarshi sai wayoyinhshi da ke rike a daya hannun

kara so wayayi gurin yana kallon nene wacce ta hakince akan kujera fuskarta babu yabu babu fallasa

yace "nene ya zamu fita kallonsa nenen tayi tace "Allah ya bada sa'a amma kana jin irin diban albarkar da yarinyar nan take ko" ? tafada tana kallon inda dija take zaune tana faman zuzzobaro dan karamin bakinta wanda hakan har ya zamar mata jiki

kallon agogo abbah yayi sannan ya mai da kallonsa kan nene cikin kulawa yace " babu lokaci nene yanzu in na dawi sai muyi maganar kwata kwata ya nuna bai san abinda yake faruwaba

"to babu laifi ALLAH ya tsare ya bada abinda ake nema mai amfani " nenen tafada cike da kulawa

"ameen ameen" abban ya fada yayin da yake barin gurin

"Abbah ALLAH ya kiyaye hanya" dija ta fada tana kallonsa " ameen dijana"

siyama ma Adawo lafiya tayi mishi ya amsa cikin kulawa

ummi kam bayansa tabi hannuta rike da karamar jakarsa ta aiki

Cikin sauri haruna drevar abban ya tashi wanda dama yana zaman jiran fitowar abban yakaraso ya karbi jakar dake hannun ummin yana gaisheta amsawa ummi tayi tana barin gun bayan takara yiwa abbah Allah ya ki kiyaye

da sauri haruna ya karasa ya budewa abba motar shikam abba har ya bude ya shige yana kallon haruna yace "shiga mu tafi bude motar ma sai na tsaya ka bude min da rai na da lafiya ta haruna"

murmushi haruna yake yace "ALLAH yaja da rai ALHAJI ai mu kam babu abinda za muce da kai da iyalinka ka ci damu kayi mana aure mu da muke karkashin ka mu za mufadi alkairinka in da masu kudinmu zasu dinga koyi da irin halayenka da dayawa ba'ayi talauci ba"

*******

To captin ALIYU yau an shiga offece bakin aiki bakin fama ko wanne da offece dinshi don haka bayan sun gaisa da faruk din kowa ya shige nashi domin akwai tari aiki wanda zasuyi

bakinshi dauke da addu'a ya shiga offece din yana karewa masa kallo

masha ALLAH babu abinda babu aciki zama yayi kan kujera hade da cire glass din dayake idanshi

yana kallon katon teble din da yake gabansa wasu manyan yan takkadu ya gani da dauka yayi ya fara dubawa

wayar shi ya dauka yana ne man ogansu yana son yai yi mai karin bayani akan su

"hello " ALI yafada bayan yaji an dau wayar

daga daya ban garan akace "ALIYU ZAKIN FAMA " cikin barkwanci

murmushi ALI yayi yace" oga barka da asubah " "barka kadai ' ogan fada

"ina fatan ka na" offece ko "?

"eh oga ina son karin bayani ne a kan wannan ta kaddun da nagani yanzu"

"Ok rigima nan ce ta jahar taraba jalingo ta wannan ba fulatanin mutuminan wanda aka A ka kashewa iyalinsa yaje garinsu yace bazai yadda ba shine "yan uwansa suka zo suna ta barna in suka yi kisa sai ane mesu a rasa dan haka mun tura captin shamsu da sauran "yan uwansa akan hakan,
ina so kayi binkice sosai akan rigimar nasanka da kokari da kai fin tunani"

idanunshi kan wata takkada yana nazarinta yace "karkadamu oga insha ALLAH komai zai yi daidai"

"ok shima faruk din nasa a ajiye masa ya yi nazarin sosai domin tare nake son in tura ko garin"

"ok amma ina tunanin arna garin ne suka yiwa wannan ba fillace wannan aikin lokacin da ya futa kiwo oga ka san cewar yana da karfi arziki da iyali da shanu da ALLAH yai mai arzikinsu"

"kwarai kuwa ana tunani wannan abinda ALLAH yayi masa shine yasa sukayi masa wannan ta'annatin sabida shima yanke jiki yayi yafadi lokacin da yadawo daga kiwo yaga rariyar gidansa tana kwararar da jini domin yankan rago suka yiwa iyalinshi bai tsira da komai ba sai shannusa to shine "yan uwansa suke ta barna suma da sunyi kisa sai a nemesu a rasa
so muke ane mi sulhu dasu "

"kwarai kuwa hakan yakamata ayi " Alin yafada yana kara nazarin abin

"gobe in sha ALLAH zakubi su captin shamsu sabida haka ku kwana cikin shiri"

"ok oga ALLAH yakaimu "

"yawwa ka kara nazari sosai" ogan yafada yana kokarin kashe wayar

yana kashe wayar kiran faruk ya shigo yace

"Meka fuskanta da rigimar da ake a jahar taraba tsakanin arnan garin da ba fillacen mutuminan"?

"Eh ina nazarin al'amarin ne amma fa ina tunanin wa "yannan mutanan yaki da bindiga bazai musu ba tunda ba'a ganinsu sai bayan sunyi barna suke bacewa bat"! faruk din yafada

"kwarai kuwa dama sulhu za'a ne ma kawai dasu tunda tabo su akayi "
Ali ya fada sannan yace " gobe insha Allah zamubi bayan su shamsu yanzu muka ga ma waya da oga"

"Ok ALLAH ya kaimu " faruk din yafada

"ameen" Alin yace yana kokarin kashe wayar

To acan gida kam dija yini tayi tana faman nukkufurci da bace bacen rai taki kula kowa ciki kuwa har da mutuminta jameel

Haka yazo ya karaci neman maganarsa a gun nene tayi mai banza itakam nene zuwa tayi tayi kwanciyarta tace kyayi ki gama kafata kafarki yarinya

ko da fa iza ta dawo kin kula ta tayi sai da fa'izan taje ta tambayi nene me akayiwa dija ta ke faman cin kunu

Kallonta nene tayi tana mamakin wannan kauna da suke wa junansu gami da shakuwa ita bata taba ganin mutumin da dija ta zauna dashi na awa daya batare da sunyi fada ba sai fa'iza

"kyaleta fai'za wai abarta ta zauna anan abbanku yace zai sata a irin makarantar da kike zuwa shine nace ban amunceba shine take ta faman bace bacen rai"

bata fuska fa'iza tayi cikin yanayin shagawaba tace " to meyasa bazaki barta ba iyi nene?"
"Ai tana zuwa makarantar acan in nabarta anan wazai dinga debe min kewa"
Chapter 18 · 0% Book details